أَمَّا مَنِ ٱسۡتَغۡنَىٰ
Amma wanda ya wadatu (daga wa’azinka)
Partager :
فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ
To kai shi kake fuskanta
وَمَا عَلَيۡكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ
Babu kuwa komai a kanka don ya qi ya tsarkaka
وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسۡعَىٰ
Amma kuma wanda ya zo maka yana sauri
وَهُوَ يَخۡشَىٰ
Alhali kuma shi yana tsoron (Allah)
فَأَنتَ عَنۡهُ تَلَهَّىٰ
To kai shi kake kawar wa da kai
كَلَّآ إِنَّهَا تَذۡكِرَةٞ
Abin ba haka yake ba, lalle (wannan da’awar) wa’azi ne
فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ
Don haka wanda ya ga dama ya wa’azantu
فِي صُحُفٖ مُّكَرَّمَةٖ
(Wannan Alqur’ani) yana cikin takardu ababan girmamawa
مَّرۡفُوعَةٖ مُّطَهَّرَةِۭ
Maxaukaka, tsarkaka
بِأَيۡدِي سَفَرَةٖ
A hannayen jakadu (mala’iku)
كِرَامِۭ بَرَرَةٖ
Manya masu biyayya
قُتِلَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَآ أَكۡفَرَهُۥ
An la’anci mutum, me ya kai tsananin kafircinsa!
مِنۡ أَيِّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥ
Shin daga wane abu ne (Allah) Ya halicce shi?
مِن نُّطۡفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ
Daga maniyyi ne Ya halicce shi, sannan Ya qaddara shi (matakai a halitta)
ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ
Sannan tafarki (na rayuwa) Ya hore masa shi
ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقۡبَرَهُۥ
Sannan Ya kashe shi, sai Ya sa shi cikin qabarinsa
ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ
Sannan in Ya ga dama Ya tashe shi
كَلَّا لَمَّا يَقۡضِ مَآ أَمَرَهُۥ
Fafau (zaton mutum) ba haka ne ba, har yanzu bai aikata abin da (Allah) Ya umarce shi ba
فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ
To mutum ya yi duba zuwa ga abincinsa mana?
أَنَّا صَبَبۡنَا ٱلۡمَآءَ صَبّٗا
Cewa lalle Mu Muka zubo da ruwan sama zubowa
ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقّٗا
Sannan Muka tsaga qasa tsagawa
فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبّٗا
Sai Muka tsiro da qwaya daga cikinta
وَعِنَبٗا وَقَضۡبٗا
Da inabai da ciyayi
وَزَيۡتُونٗا وَنَخۡلٗا
Da zaitun da dabino
وَحَدَآئِقَ غُلۡبٗا
Da gonaki cike da itatuwa
وَفَٰكِهَةٗ وَأَبّٗا
Da kayan marmari da makiyaya
مَّتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ
Don jin daxinku da na dabbobinku
فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ
Sannan idan mai sa kurunta ta zo (watau busa ta farko)
يَوۡمَ يَفِرُّ ٱلۡمَرۡءُ مِنۡ أَخِيهِ
A ranar da mutum yake guje wa xan’uwansa