Sourate: Suratu Maryam

Verset : 55

وَكَانَ يَأۡمُرُ أَهۡلَهُۥ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ وَكَانَ عِندَ رَبِّهِۦ مَرۡضِيّٗا

Kuma ya zamanto yana umartar iyalinsa da (tsai da) salla da kuma (ba da) zakka, kuma shi yardajje ne a wurin Ubangijinsa



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 56

وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ إِدۡرِيسَۚ إِنَّهُۥ كَانَ صِدِّيقٗا نَّبِيّٗا

Kuma ka ambaci (labarin) Idrisu a cikin (wannan) Littafi (Alqur’ani). Lalle shi ya kasance mai yawan gaskiya ne, Annabi



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 57

وَرَفَعۡنَٰهُ مَكَانًا عَلِيًّا

Muka kuma xaukaka shi daraja maxaukakiya[1]


1- A Mi’iraji da Annabi () ya yi ya haxu da shi a sama ta huxu.


Sourate: Suratu Maryam

Verset : 58

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِن ذُرِّيَّةِ ءَادَمَ وَمِمَّنۡ حَمَلۡنَا مَعَ نُوحٖ وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡرَـٰٓءِيلَ وَمِمَّنۡ هَدَيۡنَا وَٱجۡتَبَيۡنَآۚ إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُ ٱلرَّحۡمَٰنِ خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَبُكِيّٗا۩

Waxannan su ne annabawa waxanda Allah Ya yi ni’ima a gare su, daga zuriyar Adamu, da kuma waxanda Muka xauko (a jirgin ruwa) tare da Nuhu, daga kuma zuriyar Ibrahimu da Isra’ila (watau Ya’aqubu), da kuma waxanda Muka shiryar da su Muka kuma zave su. Idan ana karanta musu ayoyin (Allah) Mai rahama sai su faxi su yi sujjada suna kuka



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 59

۞فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٌ أَضَاعُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَٱتَّبَعُواْ ٱلشَّهَوَٰتِۖ فَسَوۡفَ يَلۡقَوۡنَ غَيًّا

Sai wasu suka maye gurbinsu bayansu waxanda suka tozarta salla suka kuma bi sha’awace-sha’awacen (duniya na savo); to ba da daxewa ba za su haxu da mummunan sharri (a Jahannama)



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 60

إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ شَيۡـٔٗا

Sai dai wanda ya tuba ya yi imani ya kuma yi aiki na gari, to waxannan za su shiga Aljanna, kuma ba za a tauye musu komai ba



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 61

جَنَّـٰتِ عَدۡنٍ ٱلَّتِي وَعَدَ ٱلرَّحۡمَٰنُ عِبَادَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّهُۥ كَانَ وَعۡدُهُۥ مَأۡتِيّٗا

(Watau) gidajen Aljanna na dindindin waxanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa bayinsa alqawari da su alhali ba su gan su ba. Lalle alqawarinsa kuwa ya tabbata mai zuwa ne



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 62

لَّا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوًا إِلَّا سَلَٰمٗاۖ وَلَهُمۡ رِزۡقُهُمۡ فِيهَا بُكۡرَةٗ وَعَشِيّٗا

Ba za su ji wani zancen banza ba a cikinsu sai sallama (daga mala’iku); kuma arzikinsu na nan tare da su a cikinsu safe da yamma



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 63

تِلۡكَ ٱلۡجَنَّةُ ٱلَّتِي نُورِثُ مِنۡ عِبَادِنَا مَن كَانَ تَقِيّٗا

Waccan ita ce Aljannar da za Mu gadar da ita ga wanda ya zamo mai taqawa daga cikin bayinmu



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 64

وَمَا نَتَنَزَّلُ إِلَّا بِأَمۡرِ رَبِّكَۖ لَهُۥ مَا بَيۡنَ أَيۡدِينَا وَمَا خَلۡفَنَا وَمَا بَيۡنَ ذَٰلِكَۚ وَمَا كَانَ رَبُّكَ نَسِيّٗا

(Mala’ika Jibrilu ya ce): “Ba ma sauka sai da umarnin Ubangijinka[1]; abin da yake gabanmu da wanda yake bayanmu da kuma abin da yake tsakanin waxannan (duka) nasa ne. Ubangijinka kuma bai zama Mai mantuwa ba


1- Allah () shi ne ya umarci Jibrilu () ya ba wa Annabi () amsar tambayar da ya yi masa game da rashin zuwansa na wani xan lokaci.


Sourate: Suratu Maryam

Verset : 65

رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا فَٱعۡبُدۡهُ وَٱصۡطَبِرۡ لِعِبَٰدَتِهِۦۚ هَلۡ تَعۡلَمُ لَهُۥ سَمِيّٗا

“(Shi ne) Ubangijin sammai da qasa da kuma abin da yake tsakaninsu, sai ka bauta masa kuma ka yi haquri ga bautarsa. Shin ka san wani tamkarsa?”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 66

وَيَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَءِذَا مَا مِتُّ لَسَوۡفَ أُخۡرَجُ حَيًّا

Kuma mutum (watau kafiri) yana cewa: “Yanzu idan na mutu anya kuwa za a ta da ni da rai?”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 67

أَوَلَا يَذۡكُرُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَنَّا خَلَقۡنَٰهُ مِن قَبۡلُ وَلَمۡ يَكُ شَيۡـٔٗا

Yanzu shi kafiri ba zai tuna ba cewa Mu Muka halicce shi tun farko kafin ya zama komai?



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 68

فَوَرَبِّكَ لَنَحۡشُرَنَّهُمۡ وَٱلشَّيَٰطِينَ ثُمَّ لَنُحۡضِرَنَّهُمۡ حَوۡلَ جَهَنَّمَ جِثِيّٗا

To na rantse da Ubangijinka lalle za Mu tashe su tare da shaixanu, sannan za Mu kawo su a gaban Jahannama suna a duddurqushe



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 69

ثُمَّ لَنَنزِعَنَّ مِن كُلِّ شِيعَةٍ أَيُّهُمۡ أَشَدُّ عَلَى ٱلرَّحۡمَٰنِ عِتِيّٗا

Sannan daga kowace jama’a lalle za Mu ware waxanda suka fi tsananin yi wa (Allah) Mai rahama tsaurin kai



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 70

ثُمَّ لَنَحۡنُ أَعۡلَمُ بِٱلَّذِينَ هُمۡ أَوۡلَىٰ بِهَا صِلِيّٗا

Sannan babu shakka Mu Muka fi sanin waxanda suka fi cancanta da qonuwa da ita (watau wuta)



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 71

وَإِن مِّنكُمۡ إِلَّا وَارِدُهَاۚ كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ حَتۡمٗا مَّقۡضِيّٗا

Ba kuma xaya daga cikinku face sai ya bi ta kanta (watau wutar Jahannama). (Wannan) ya kasance tabbataccen abu abin hukuntawa a wurin Ubangijinka



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 72

ثُمَّ نُنَجِّي ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْ وَّنَذَرُ ٱلظَّـٰلِمِينَ فِيهَا جِثِيّٗا

Sannan kuma za Mu tserar da waxanda suka kiyaye dokokin Allah Mu kuma bar kafirai a duddurqushe cikinta



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 73

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَيُّ ٱلۡفَرِيقَيۡنِ خَيۡرٞ مَّقَامٗا وَأَحۡسَنُ نَدِيّٗا

Kuma idan ana karanta musu ayoyinmu bayyanannu sai waxanda suka kafirta su ce da waxanda suka yi imani: “Wane ne daga cikin qungiyoyin nan biyu (watau muminai da kafirai) yake da mafificin matsayi da kuma mafi kyan majalisa?”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 74

وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّن قَرۡنٍ هُمۡ أَحۡسَنُ أَثَٰثٗا وَرِءۡيٗا

Kuma al’umma nawa Muka hallaka a gabanninsu waxanda suke da mafi kyan abin duniya da kyawun gani



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 75

قُلۡ مَن كَانَ فِي ٱلضَّلَٰلَةِ فَلۡيَمۡدُدۡ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ مَدًّاۚ حَتَّىٰٓ إِذَا رَأَوۡاْ مَا يُوعَدُونَ إِمَّا ٱلۡعَذَابَ وَإِمَّا ٱلسَّاعَةَ فَسَيَعۡلَمُونَ مَنۡ هُوَ شَرّٞ مَّكَانٗا وَأَضۡعَفُ جُندٗا

Ka ce (da su): “Wanda ya zamana yana cikin vata to (Allah) Mai rahama zai tsawaita ransa Ya yalwata masa; Har sai sanda suka ga abin da ake yi musu alqawari da shi ne, ko dai azaba (a duniya) ko kuma tashin alqiyama, to fa za su san wane ne ya fi mummunan matsayi da kuma (wanda) ya fi raunin mataimaka.”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 76

وَيَزِيدُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ٱهۡتَدَوۡاْ هُدٗىۗ وَٱلۡبَٰقِيَٰتُ ٱلصَّـٰلِحَٰتُ خَيۡرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَابٗا وَخَيۡرٞ مَّرَدًّا

Kuma Allah Yana qara shiryar da waxanda suka bi hanyar shiriya. Wanzazzun ayyuka na gari kuma su suka fi lada a wurin Ubangijinka, suka kuma fi kyakkyawan qarshe



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 77

أَفَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي كَفَرَ بِـَٔايَٰتِنَا وَقَالَ لَأُوتَيَنَّ مَالٗا وَوَلَدًا

Shin kuwa ka ga wanda ya kafirce wa ayoyinmu, ya kuma ce: “Lalle tabbas za a ba ni dukiya da ‘ya’yaye?”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 78

أَطَّلَعَ ٱلۡغَيۡبَ أَمِ ٱتَّخَذَ عِندَ ٱلرَّحۡمَٰنِ عَهۡدٗا

Shin ko ya san gaibu ne, ko kuwa ya sami alqawari ne a wurin (Allah) Mai rahama?



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 79

كَلَّاۚ سَنَكۡتُبُ مَا يَقُولُ وَنَمُدُّ لَهُۥ مِنَ ٱلۡعَذَابِ مَدّٗا

A’a, ba haka ba ne. Za Mu rubuta abin da yake faxa, za Mu kuma qara masa azaba ninkin-ba-ninkin



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 80

وَنَرِثُهُۥ مَا يَقُولُ وَيَأۡتِينَا فَرۡدٗا

Kuma Mu gaje abin da yake faxa xin (na dukiyarsa da ‘ya’yansa), ya kuma zo mana shi kaxai[1]


1- Watau Allah zai xauke shi kacokam lokacin mutuwarsa, ya raba shi da dukiyarsa da ‘ya’yansa da yake taqama da su.


Sourate: Suratu Maryam

Verset : 81

وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةٗ لِّيَكُونُواْ لَهُمۡ عِزّٗا

(Kafirai) kuma suka riqi wasu abubuwan bauta ba Allah ba don su zama mataimaka a gare su



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 82

كَلَّاۚ سَيَكۡفُرُونَ بِعِبَادَتِهِمۡ وَيَكُونُونَ عَلَيۡهِمۡ ضِدًّا

A’a, ba haka ba ne. Ba da daxewa ba za su kafirce wa bautar da suke yi musu, su kuma zama abokan gaba a gare su



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 83

أَلَمۡ تَرَ أَنَّآ أَرۡسَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ تَؤُزُّهُمۡ أَزّٗا

Shin ba ka san Mu Muka xora shaixanu a kan kafirai ba suna ingiza su (cikin vata) ingizawa?



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 84

فَلَا تَعۡجَلۡ عَلَيۡهِمۡۖ إِنَّمَا نَعُدُّ لَهُمۡ عَدّٗا

To kada ka yi gaggawa a kansu; kawai dai Muna qididdige musu (kwanakinsu) xai da xai