Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 153

۞إِذۡ تُصۡعِدُونَ وَلَا تَلۡوُۥنَ عَلَىٰٓ أَحَدٖ وَٱلرَّسُولُ يَدۡعُوكُمۡ فِيٓ أُخۡرَىٰكُمۡ فَأَثَٰبَكُمۡ غَمَّۢا بِغَمّٖ لِّكَيۡلَا تَحۡزَنُواْ عَلَىٰ مَا فَاتَكُمۡ وَلَا مَآ أَصَٰبَكُمۡۗ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Ka tuna lokacin da kuke guduwa ba kwa waiwaye ma ku ga wanda yake baya da ku, kuma Manzo yana can bayanku yana ta kiran ku, sai (Allah) Ya saka muku da damuwa bisa damuwa domin kar ku yi baqin ciki a kan abin da ya kuvuce muku, da abin da ya same ku. Allah kuma Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 154

ثُمَّ أَنزَلَ عَلَيۡكُم مِّنۢ بَعۡدِ ٱلۡغَمِّ أَمَنَةٗ نُّعَاسٗا يَغۡشَىٰ طَآئِفَةٗ مِّنكُمۡۖ وَطَآئِفَةٞ قَدۡ أَهَمَّتۡهُمۡ أَنفُسُهُمۡ يَظُنُّونَ بِٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ ظَنَّ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِۖ يَقُولُونَ هَل لَّنَا مِنَ ٱلۡأَمۡرِ مِن شَيۡءٖۗ قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَمۡرَ كُلَّهُۥ لِلَّهِۗ يُخۡفُونَ فِيٓ أَنفُسِهِم مَّا لَا يُبۡدُونَ لَكَۖ يَقُولُونَ لَوۡ كَانَ لَنَا مِنَ ٱلۡأَمۡرِ شَيۡءٞ مَّا قُتِلۡنَا هَٰهُنَاۗ قُل لَّوۡ كُنتُمۡ فِي بُيُوتِكُمۡ لَبَرَزَ ٱلَّذِينَ كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَتۡلُ إِلَىٰ مَضَاجِعِهِمۡۖ وَلِيَبۡتَلِيَ ٱللَّهُ مَا فِي صُدُورِكُمۡ وَلِيُمَحِّصَ مَا فِي قُلُوبِكُمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Sannan bayan damuwa sai (Allah) Ya saukar muku da kwanciyar hankali har gyangyaxi yana xaukar wasu daga cikinku; amma wani sashin kuma tasu ta ishe su, suna yi wa Allah zato wanda ba na gaskiya ba, zato irin na jahiliyya; suna cewa: “Anya kuwa muna da ta cewa cikin wannan lamari?” Ka ce: “Lalle al’amari gaba xaya na Allah ne.” Suna voyewa a cikin rayukansu abin da ba sa bayyana maka shi; suna cewa: “In da al’amarin a hannunmu yake ai da ba a kashe mu a nan ba.” Ka ce: “Ko da kun kasance kuna cikin gidajenku, tabbas da waxanda aka rubuta za su mutu sun fito da kansu, sun zo inda nan ne za su kwanta (dama).” Kuma Allah (Ya qaddara haka) don Ya jarraba abin da yake cikin qirazanku, kuma don Ya tace abin da yake cikin zukatanku. Kuma Allah Masanin abin da yake cikin qiraza ne



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 155

إِنَّ ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ مِنكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِ إِنَّمَا ٱسۡتَزَلَّهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِبَعۡضِ مَا كَسَبُواْۖ وَلَقَدۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Lalle waxanda suka gudu daga cikinku yayin da runduna biyu suka haxu, Shaixan ne ya nemi ya zamar da su saboda wani laifi da suka yi; kuma tabbas haqiqa Allah Ya yi musu afuwa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai haquri



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 156

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَقَالُواْ لِإِخۡوَٰنِهِمۡ إِذَا ضَرَبُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَوۡ كَانُواْ غُزّٗى لَّوۡ كَانُواْ عِندَنَا مَا مَاتُواْ وَمَا قُتِلُواْ لِيَجۡعَلَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ حَسۡرَةٗ فِي قُلُوبِهِمۡۗ وَٱللَّهُ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku kasance kamar waxanda suka kafirta, kuma suka riqa faxa wa ‘yan’uwansu yayin da suka yi tafiya a bayan qasa, ko kuma suka kasance mayaqa: “In da sun kasance tare da mu, ai da ba su mutu ba, kuma da ba a kashe su ba,” don Allah Ya sanya waccan (maganar) ta zamo nadama a cikin zukatansu. Kuma Allah Shi ne Mai rayawa, kuma Shi ne Mai kashewa. Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 157

وَلَئِن قُتِلۡتُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَوۡ مُتُّمۡ لَمَغۡفِرَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَحۡمَةٌ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ

Kuma lalle idan ma har an kashe ku a hanyar Allah ko kuma kuka mutu, to kuna da gafara ta musamman a wajen Allah da kuma rahama, wanda shi ne mafi alheri fiye da abin da suke tarawa



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 158

وَلَئِن مُّتُّمۡ أَوۡ قُتِلۡتُمۡ لَإِلَى ٱللَّهِ تُحۡشَرُونَ

Kuma lalle in kuka mutu ko aka kashe ku, lalle zuwa ga Allah dai za a tattara ku



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 159

فَبِمَا رَحۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمۡۖ وَلَوۡ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلۡقَلۡبِ لَٱنفَضُّواْ مِنۡ حَوۡلِكَۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ وَشَاوِرۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِۖ فَإِذَا عَزَمۡتَ فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَوَكِّلِينَ

To saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zamo mai tausasawa gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu’amala, mai qeqasasshiyar zuciya ne, to da sun watse sun bar ka. To ka yi musu afuwa, kuma ka nema musu gafara, kuma ka nemi shawararsu cikin duk lamura; amma idan ka riga ka qulla niyya, to ka dogara ga Allah. Lalle Allah Yana son masu dogara a gare Shi



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 160

إِن يَنصُرۡكُمُ ٱللَّهُ فَلَا غَالِبَ لَكُمۡۖ وَإِن يَخۡذُلۡكُمۡ فَمَن ذَا ٱلَّذِي يَنصُرُكُم مِّنۢ بَعۡدِهِۦۗ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

Idan Allah Ya ba ku nasara, to ba wanda ya isa ya rinjaye ku, amma idan Ya tavar da ku, to wane ne ya isa ya taimake ku in ba shi ba? Kuma muminai wajibi ne su dogara ga Allah Shi kaxai



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 161

وَمَا كَانَ لِنَبِيٍّ أَن يَغُلَّۚ وَمَن يَغۡلُلۡ يَأۡتِ بِمَا غَلَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Kuma bai dace ba ga wani annabi ya yi ha’inci. Duk wanda ya yi ha’inci kuwa zai zo da abin da ya ha’inta ranar tashin alqiyama. Sannan kowane rai a cika masa (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su (halitta) ba za a zalunce su ba



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 162

أَفَمَنِ ٱتَّبَعَ رِضۡوَٰنَ ٱللَّهِ كَمَنۢ بَآءَ بِسَخَطٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَمَأۡوَىٰهُ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Shin yanzu wanda ya bi yardar Allah, zai yi kamar wanda ya dawo da fushin Allah, kuma makomarsa ta zamo Jahannama? Kuma tir da wannan makoma



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 163

هُمۡ دَرَجَٰتٌ عِندَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ

Su darajoji ne a wajen Allah. Allah kuma Mai ganin abin da suke aikatawa ne



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 164

لَقَدۡ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذۡ بَعَثَ فِيهِمۡ رَسُولٗا مِّنۡ أَنفُسِهِمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِهِۦ وَيُزَكِّيهِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

Lalle haqiqa Allah Ya yi baiwa ga muminai yayin da Ya aiko musu Manzo daga cikinsu, wanda yake karanta musu ayoyinsa, kuma yake tsarkake su, kuma yake koyar da su Littafi da Hikima, lalle kuma sun kasance kafin (zuwansa) tabbas suna cikin vata mabayyani



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 165

أَوَلَمَّآ أَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةٞ قَدۡ أَصَبۡتُم مِّثۡلَيۡهَا قُلۡتُمۡ أَنَّىٰ هَٰذَاۖ قُلۡ هُوَ مِنۡ عِندِ أَنفُسِكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Shin yayin da wata musifa ta same ku, wadda kuma haqiqa kun yi wa (kafirai) irinta ninki biyu, sai ku riqa cewa: “Yaya haka ta faru?” Ka ce: “Ai wannan daga gare ku ne.” Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 166

وَمَآ أَصَٰبَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِ فَبِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَلِيَعۡلَمَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma abin da ya same ku ranar da qungiyoyin nan biyu suka haxu, to da izinin Allah ne, kuma don Ya bayyana muminai



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 167

وَلِيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ نَافَقُواْۚ وَقِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ قَٰتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَوِ ٱدۡفَعُواْۖ قَالُواْ لَوۡ نَعۡلَمُ قِتَالٗا لَّٱتَّبَعۡنَٰكُمۡۗ هُمۡ لِلۡكُفۡرِ يَوۡمَئِذٍ أَقۡرَبُ مِنۡهُمۡ لِلۡإِيمَٰنِۚ يَقُولُونَ بِأَفۡوَٰهِهِم مَّا لَيۡسَ فِي قُلُوبِهِمۡۚ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يَكۡتُمُونَ

Kuma don Ya bayyana waxanda suka yi munafunci; kuma aka riqa cewa da su: “Ku zo ku yi yaqi don Allah ko don kariya.” Sai suka ce: “Da mun san za a yi yaqi ai da lalle mun biyo ku.” Su a wannan lokacin sun fi kusanci ga kafirci fiye da imani, suna faxi da bakunansu abin da ba ya cikin zukatansu. Kuma Allah Ya san abin da suke voyewa



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 168

ٱلَّذِينَ قَالُواْ لِإِخۡوَٰنِهِمۡ وَقَعَدُواْ لَوۡ أَطَاعُونَا مَا قُتِلُواْۗ قُلۡ فَٱدۡرَءُواْ عَنۡ أَنفُسِكُمُ ٱلۡمَوۡتَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Su ne waxanda suka faxa wa ‘yan’uwansu, alhalin suna zaune a gida cewa: “In da sun bi (shawarar) mu da ba a kashe su ba.” Ka ce: “To ku kare kanku daga mutuwa in har kun kasance masu gaskiya.”



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 169

وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتَۢاۚ بَلۡ أَحۡيَآءٌ عِندَ رَبِّهِمۡ يُرۡزَقُونَ

Kuma kada ka yi tsammanin waxanda aka kashe su a wajen yaxa kalmar Allah matattu ne. A’a, rayayyu ne a wajen Ubangijinsu, ana arzurta su



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 170

فَرِحِينَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ وَيَسۡتَبۡشِرُونَ بِٱلَّذِينَ لَمۡ يَلۡحَقُواْ بِهِم مِّنۡ خَلۡفِهِمۡ أَلَّا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Suna cike da farin cikin abin da Allah Ya ba su na falalarsa, kuma suna masu yin albishir ga waxanda ba su riga sun riske su ba daga bayansu cewa, babu jin tsoro a gare su, kuma ba za su yi baqin ciki ba