إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ
Sai fa wata tsohuwa (watau matarsa) da ta (kasance tana) cikin hallakakku
Partager :
ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Sannan Muka hallaka sauran
وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرٗاۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلۡمُنذَرِينَ
Muka kuma saukar musu da ruwa na azaba; to ruwan azabar waxanda aka yi wa gargaxi ya munana
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; yawancinsu kuwa ba su zamanto muminai ba
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma lalle Ubangiijnka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin qai
كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ لۡـَٔيۡكَةِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Mutanen kurmi sun qaryata manzanni
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ شُعَيۡبٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da Shu’aibu ya ce da su: “Yanzu ba kwa kiyaye dokokin (Allah) ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai
۞أَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُخۡسِرِينَ
“Ku cika mudu kada kuma ku zamanto daga masu tauye (shi)
وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِ
“Kuma ku riqa yin awon nauyi da ma’auni na adalci
وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ
“Kada kuma ku tauye wa mutane kayayyakinsu, kuma kada ku yawaita varna a bayan qasa
وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلۡجِبِلَّةَ ٱلۡأَوَّلِينَ
“Kuma ku kiyaye dokokin (Allah) wanda Ya halicce ku da kuma al’ummu na farko.”
قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلۡمُسَحَّرِينَ
Suka ce: “Kai dai kana daga waxanda aka sihirce ne kawai
وَمَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا وَإِن نَّظُنُّكَ لَمِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
“Kuma kai ba kowa ba ne sai mutum kamarmu, kuma ma lalle muna zaton kana daga maqaryata!
فَأَسۡقِطۡ عَلَيۡنَا كِسَفٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
“Sai ka jeho mana da yankuna (na azaba) daga sama in ka kasance daga masu gaskiya!”
قَالَ رَبِّيٓ أَعۡلَمُ بِمَا تَعۡمَلُونَ
(Shu’aibu) Ya ce: “Ubangijina Ya fi kowa sanin abin da kuke aikatawa.”
فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمِ ٱلظُّلَّةِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٍ
Sai suka qaryata shi, sannan sai azabar yinin girgije (na wuta) ta kama su. Lalle ta kasance azabar wani yini ne mai girma
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; sai dai kuma yawancinsu ba su kasance muminai ba
Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai rahama
وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Kuma lalle shi (Alqur’ani) saukarwa ce ta Ubangijin talikai
نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلۡأَمِينُ
Ruhi amintacce (watau Jibrilu) ne ya sauko da shi
عَلَىٰ قَلۡبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُنذِرِينَ
A bisa zuciyarka don ka zamanto daga masu gargaxi
بِلِسَانٍ عَرَبِيّٖ مُّبِينٖ
(Ya saukar da shi) da harshen Larabci mabayyani
وَإِنَّهُۥ لَفِي زُبُرِ ٱلۡأَوَّلِينَ
Kuma lalle shi yana daga cikin littattafan farko
أَوَلَمۡ يَكُن لَّهُمۡ ءَايَةً أَن يَعۡلَمَهُۥ عُلَمَـٰٓؤُاْ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ
Yanzu bai ishe su aya ba cewa, malaman Banu- Isra’ila sun san shi?
وَلَوۡ نَزَّلۡنَٰهُ عَلَىٰ بَعۡضِ ٱلۡأَعۡجَمِينَ
Da kuwa Mun saukar da shi ga wani wanda ba Balarabe ba
فَقَرَأَهُۥ عَلَيۡهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ مُؤۡمِنِينَ
Sannan ya karanta musu shi, to da ba za su yi imani da shi ba
كَذَٰلِكَ سَلَكۡنَٰهُ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Kamar haka ne Muka shigar da shi (qaryata Annabi) cikin zukatan manyan masu laifi