كَذَّبَتۡ ثَمُودُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Samudawa sun qaryata manzanni[1]
1- Domin qaryata Annabi Salihu () daidai yake da qaryata duk manzannin Allah, saboda saqo iri xaya suke xauke da shi.
Partager :
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ صَٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da xan’uwansu Salihu ya ce da su: “Yanzu ba kwa yi taqawa ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai
أَتُتۡرَكُونَ فِي مَا هَٰهُنَآ ءَامِنِينَ
“Yanzu (zatonku) za a bar ku ne cikin abin da yake a nan (duniya) cikin kwanciyar hankali?
فِي جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ
“(Watau) a cikin gonaki da idandunan ruwa?
وَزُرُوعٖ وَنَخۡلٖ طَلۡعُهَا هَضِيمٞ
“Da shuke-shuke da dabinai masu taushin ‘ya’ya?
وَتَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتٗا فَٰرِهِينَ
“Kuma kuna fafe duwatsu kuna yin gidaje kuna masu nuna qwarewa?
وَلَا تُطِيعُوٓاْ أَمۡرَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
“Kada kuma ku bi umarnin mavarnata
ٱلَّذِينَ يُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا يُصۡلِحُونَ
“Waxanda suke varna a bayan qasa, kuma ba sa gyara.”
قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلۡمُسَحَّرِينَ
Suka ce: “Lalle kai kana daga waxanda aka sihirce ne kawai
مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا فَأۡتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
“Kai ba kowa ba ne sai mutum kamarmu, to ka zo mana da aya idan ka kasance daga masu gaskiya.”
قَالَ هَٰذِهِۦ نَاقَةٞ لَّهَا شِرۡبٞ وَلَكُمۡ شِرۡبُ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ
(Salihu) ya ce: “Wannan taguwa ce[1], tana da (ranar) shanta ku ma kuna da rana sananniya ta shanku
1- Watau a matsayin mu’ujiza ga Annabi Salihu ().
وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
“Kada kuwa ku shafe ta da mugun abu, sai azabar wani yini mai girma ta kama ku.”
فَعَقَرُوهَا فَأَصۡبَحُواْ نَٰدِمِينَ
Sai suka soke ta, sai kuwa suka wayi gari suna masu nadama
فَأَخَذَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Sai azaba ta kama su. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin qai
كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Mutanen Luxu sun qaryata manzanni
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da xan’uwansu Luxu ya ce da su: “Yanzu ba kwa kiyaye dokokin Allah ba?
أَتَأۡتُونَ ٱلذُّكۡرَانَ مِنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“Yanzu kwa riqa zaike wa maza daga halittu?
وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُمۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٌ عَادُونَ
“Kuma ku bar abin da Ubangijinku Ya halitta na matanku dominku? A’a, ku dai mutane ne masu qetare iyaka.”
قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُخۡرَجِينَ
Suka ce: “Tabbas Luxu idan ba ka bar (faxar abin da kake faxa ba) haqiqa za ka kasance daga korarru (daga garin nan).”
قَالَ إِنِّي لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلۡقَالِينَ
(Luxu) ya ce: “Lalle ni ina cikin masu qyamar aikin nan naku
رَبِّ نَجِّنِي وَأَهۡلِي مِمَّا يَعۡمَلُونَ
“Ya Ubangijina, Ka tserar da ni da iyalina daga (sakamakon) abin da suke aikatawa.”
فَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
Sai Muka tserar da shi da iyalinsa gaba xaya