۞وَلَقَدۡ وَصَّلۡنَا لَهُمُ ٱلۡقَوۡلَ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
Haqiqa kuma Mun saukar musu da Alqur’ani (guntu-guntu) don su wa’azantu
ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِهِۦ هُم بِهِۦ يُؤۡمِنُونَ
Waxanda Muka bai wa littafi a gabaninsa (Alqur’ani) (suka tsaya a kansa) su suna yin imani da shi (Alqur’ani)
وَإِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِهِۦٓ إِنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّنَآ إِنَّا كُنَّا مِن قَبۡلِهِۦ مُسۡلِمِينَ
Idan kuma ana karanta musu (Alqur’anin) sai su ce: “Mun yi imani da shi, lalle shi gaskiya ne daga Ubangijinmu, lalle mu mun kasance Musulmi tun gabaninsa.”
أُوْلَـٰٓئِكَ يُؤۡتَوۡنَ أَجۡرَهُم مَّرَّتَيۡنِ بِمَا صَبَرُواْ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Waxannan (su ne) za a ba su ladansu ninki biyu saboda haqurin da suka yi. Kuma suna kawar da mummunan aiki da kyakkyawa, suna kuma ciyarwa daga abin da Muka arzuta su (da shi)
وَإِذَا سَمِعُواْ ٱللَّغۡوَ أَعۡرَضُواْ عَنۡهُ وَقَالُواْ لَنَآ أَعۡمَٰلُنَا وَلَكُمۡ أَعۡمَٰلُكُمۡ سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡ لَا نَبۡتَغِي ٱلۡجَٰهِلِينَ
Idan kuma suka ji maganar banza sai su kau da kai daga gare ta, sai kuma su ce: “(Sakamakon) ayyukanmu yana gare mu, ku kuma na ayyukanku yana gare ku, kun kuvuta daga gare mu, ba ruwanmu da wawaye!”
إِنَّكَ لَا تَهۡدِي مَنۡ أَحۡبَبۡتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ
Lalle kai ba ka iya shiryar da wanda ka so, sai dai Allah ne Yana shiryar da wanda Ya ga dama. Shi kuma ne Ya san masu shiryuwa
وَقَالُوٓاْ إِن نَّتَّبِعِ ٱلۡهُدَىٰ مَعَكَ نُتَخَطَّفۡ مِنۡ أَرۡضِنَآۚ أَوَلَمۡ نُمَكِّن لَّهُمۡ حَرَمًا ءَامِنٗا يُجۡبَىٰٓ إِلَيۡهِ ثَمَرَٰتُ كُلِّ شَيۡءٖ رِّزۡقٗا مِّن لَّدُنَّا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Suka kuma ce: “Idan har Muka bi shiriya tare da kai, to za a kame mu (ribatattu) daga qasarmu[1]”. (Ka ce da su): “Yanzu ashe ba Mu ne Muka ba su ikon Harami amintacce ba da ake kawo kowanne irin (nau’i) na ‘ya’yan itace gare shi don arzutawa daga gare Mu?” Sai dai kuma yawancinsu ba sa sanin (haka)
1- Watau za a fincike su daga qasarsu Makka, su zama ribatattun yaqi a hannun maqiyansu.
وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةِۭ بَطِرَتۡ مَعِيشَتَهَاۖ فَتِلۡكَ مَسَٰكِنُهُمۡ لَمۡ تُسۡكَن مِّنۢ بَعۡدِهِمۡ إِلَّا قَلِيلٗاۖ وَكُنَّا نَحۡنُ ٱلۡوَٰرِثِينَ
Kuma al’umma nawa ce Muka hallakar wadda ta butulce wa rayuwarta? To ga gidajensu can ba a zaune su ba a bayansu sai kaxan[1]; Mu ne Muka kasance magadan
1- Watau daga matafiya da sukan ya da zango su zauna na xan lokaci.
وَمَا كَانَ رَبُّكَ مُهۡلِكَ ٱلۡقُرَىٰ حَتَّىٰ يَبۡعَثَ فِيٓ أُمِّهَا رَسُولٗا يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِنَاۚ وَمَا كُنَّا مُهۡلِكِي ٱلۡقُرَىٰٓ إِلَّا وَأَهۡلُهَا ظَٰلِمُونَ
Kuma Ubangijinka bai zamanto Mai hallakar da alqaryu ba har sai Ya aiko da manzo a cikin manyan biranensu, yana karanta musu ayoyinmu. Kuma ba Mu kasance Masu hallaka alqaryu ba sai idan mutanensu sun zama azzalumai
وَمَآ أُوتِيتُم مِّن شَيۡءٖ فَمَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَزِينَتُهَاۚ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Kuma duk irin abin da aka ba ku, to jin daxin rayuwar duniya ne da adonta. Abin da yake wurin Allah kuwa (shi) ya fi alhairi ya fi kuma wanzuwa. Yanzu ba kwa hankalta ba?
أَفَمَن وَعَدۡنَٰهُ وَعۡدًا حَسَنٗا فَهُوَ لَٰقِيهِ كَمَن مَّتَّعۡنَٰهُ مَتَٰعَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا ثُمَّ هُوَ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ مِنَ ٱلۡمُحۡضَرِينَ
Yanzu wanda Muka yi wa alqawari kyakkyawa da zai same shi, zai zama kamar wanda Muka jiyar da shi daxin rayuwar duniya, sannan kuma shi yana daga waxanda za a kai su wuta a ranar alqiyama?
وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ فَيَقُولُ أَيۡنَ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Kuma ka tuna ranar da (Allah) zai kirawo su sai Ya ce: “Ina abokan tarayyar nawa waxanda kuka kasance kuna riyawa?”
قَالَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَغۡوَيۡنَآ أَغۡوَيۡنَٰهُمۡ كَمَا غَوَيۡنَاۖ تَبَرَّأۡنَآ إِلَيۡكَۖ مَا كَانُوٓاْ إِيَّانَا يَعۡبُدُونَ
Sai waxanda alqawarin Allah (na azaba) ya tabbata a kansu su ce: “Ya Ubangijinmu, waxannan da muka vatar, mun vatar da su ne kamar yadda mu ma muka vata; ba ruwanmu da kowa sai kai; don kuwa ba su kasance mu suke bauta wa ba.”
وَقِيلَ ٱدۡعُواْ شُرَكَآءَكُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَرَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۚ لَوۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ يَهۡتَدُونَ
Kuma aka ce: “Ku kirawo abokan tarayyar naku”, sannan suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, suka kuma ga azaba. (Suka riqa burin) ina ma sun kasance shiryayyu!
وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ فَيَقُولُ مَاذَآ أَجَبۡتُمُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
(Ka tuna) kuma ranar da (Allah) zai kirawo su sannan Ya ce: “Me kuka amsa wa manzanni (da shi?)”
فَعَمِيَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَنۢبَآءُ يَوۡمَئِذٖ فَهُمۡ لَا يَتَسَآءَلُونَ
Sai abubuwan da za su faxa suka vace musu a wannan ranar, don haka su ba za su iya tambayar junansu ba
فَأَمَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَعَسَىٰٓ أَن يَكُونَ مِنَ ٱلۡمُفۡلِحِينَ
To amma wanda ya tuba ya kuma yi imani ya kuma yi aiki nagari, to ana fatan ya zama cikin masu samun babban rabo
وَرَبُّكَ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَخۡتَارُۗ مَا كَانَ لَهُمُ ٱلۡخِيَرَةُۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Kuma Ubangijinka Yana halittar abin da Ya ga dama Yana kuma zavar (abin da Ya ga dama). Ba su suke da zavi ba. Tsarki ya tabbata ga Allah kuma Ya xaukaka daga abin da suke yin shirka (da shi)
وَرَبُّكَ يَعۡلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمۡ وَمَا يُعۡلِنُونَ
Kuma Ubangijinka Ya san abin da zukatansu suke voyewa da kuma abin da suke bayyanawa
وَهُوَ ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ لَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلۡأُولَىٰ وَٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Kuma Shi ne Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; yabo ya tabbata a gare Shi a duniya da lahira; hukunci kuma nasa ne, kuma zuwa gare Shi ne kawai za a mayar da ku
قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمُ ٱلَّيۡلَ سَرۡمَدًا إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَنۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَأۡتِيكُم بِضِيَآءٍۚ أَفَلَا تَسۡمَعُونَ
Ka ce: “Ku ba ni labari, (yanzu) idan Allah Ya sanya muku dare tutur har zuwa ranar alqiyama, wane abin bauta ne ba Allah ba zai zo muku da wani haske? To me ya sa ba kwa ji?”
قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمُ ٱلنَّهَارَ سَرۡمَدًا إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَنۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَأۡتِيكُم بِلَيۡلٖ تَسۡكُنُونَ فِيهِۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ
Ka ce: “Ku ba ni labari, (yanzu) idan Allah Ya sanya muku rana tutur har zuwa ranar alqiyama, wane abin bauta ne ba Allah ba zai zo muku da dare da za ku samu nutsuwa a cikinsa? To me ya sa ba kwa gani?”
وَمِن رَّحۡمَتِهِۦ جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Daga rahamarsa ne kuma Ya sanya muku dare da rana don ku samu nutsuwa a cikinsa (wato dare) kuma don ku nema daga falalarsa (da rana), don kuma ku riqa yin godiya
وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ فَيَقُولُ أَيۡنَ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Ka kuma (tuna) ranar da (Allah) zai kirawo su, sai Ya ce: “Ina abokan tarayyar nawa waxanda kuka kasance kuna riyawa?”
وَنَزَعۡنَا مِن كُلِّ أُمَّةٖ شَهِيدٗا فَقُلۡنَا هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡ فَعَلِمُوٓاْ أَنَّ ٱلۡحَقَّ لِلَّهِ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Muka kuma ware wani shaida daga kowacce al’umma (watau annabinsu) sai Muka ce: “To ku kawo dalilinku (na yin tarayya da Allah).” Sai suka san cewa lalle gaskiya tana ga Allah, kuma abin da suka kasance suna qirqira ya vace musu
۞إِنَّ قَٰرُونَ كَانَ مِن قَوۡمِ مُوسَىٰ فَبَغَىٰ عَلَيۡهِمۡۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡكُنُوزِ مَآ إِنَّ مَفَاتِحَهُۥ لَتَنُوٓأُ بِٱلۡعُصۡبَةِ أُوْلِي ٱلۡقُوَّةِ إِذۡ قَالَ لَهُۥ قَوۡمُهُۥ لَا تَفۡرَحۡۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡفَرِحِينَ
Lalle Qaruna yana daga mutanen Musa, sai ya yi musu girman kai, Muka kuma ba shi taskokin (dukiya) wadda lalle makullansu suna yi wa tarin jama’a qarfafa nauyin (xauka), yayin da mutanensa suka ce da shi: “Kada ka yi fariya, lalle Allah ba Ya son masu fariya
وَٱبۡتَغِ فِيمَآ ءَاتَىٰكَ ٱللَّهُ ٱلدَّارَ ٱلۡأٓخِرَةَۖ وَلَا تَنسَ نَصِيبَكَ مِنَ ٱلدُّنۡيَاۖ وَأَحۡسِن كَمَآ أَحۡسَنَ ٱللَّهُ إِلَيۡكَۖ وَلَا تَبۡغِ ٱلۡفَسَادَ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
“Kuma ka nemi gidan lahira ta hanyar abin da Allah Ya ba ka; kada kuma ka manta rabonka na duniya; kuma ka kyautata kamar yadda Allah Ya kyautata maka, kada kuma ka nemi yin varna a bayan qasa. Lalle Allah ba Ya son masu varna.”
قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمٍ عِندِيٓۚ أَوَلَمۡ يَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَهۡلَكَ مِن قَبۡلِهِۦ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مَنۡ هُوَ أَشَدُّ مِنۡهُ قُوَّةٗ وَأَكۡثَرُ جَمۡعٗاۚ وَلَا يُسۡـَٔلُ عَن ذُنُوبِهِمُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Ya ce: “Ai ni an ba ni ita (wato dukiyar) ta hanyar ilimin da nake da shi ne.” Shin yanzu bai sani ba ne cewa haqiqa Allah Ya hallaka wasu al’ummun da suke a gabaninsa waxanda suka fi shi qarfi da kuma yawan tarin (dukiya)? Ba kuwa za a tambayi masu laifi game da laifinsu ba[1]
1- Watau zai hallaka su kawai ba tare da tsayawa a yi musu tambayoyi a kan laifukansu ba, ballantana a saurari hanzarinsu.
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ فِي زِينَتِهِۦۖ قَالَ ٱلَّذِينَ يُرِيدُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا يَٰلَيۡتَ لَنَا مِثۡلَ مَآ أُوتِيَ قَٰرُونُ إِنَّهُۥ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٖ
Sai ya fito wa mutanensa a cikin adonsa; sai waxanda suke burin rayuwar duniya suka ce: “Ina ma da za mu mallaki irin abin da aka bai wa Qaruna? Lalle shi mai babban rabo ne.”
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَيۡلَكُمۡ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّمَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗاۚ وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّـٰبِرُونَ
Waxanda kuwa aka bai wa ilimi sai suka ce: “Kaiconku, ai ladan Allah shi ya fi alheri ga wanda ya yi imani, ya kuma yi aiki na gari. Ba kuwa wanda ake yi wa katari da shi sai masu haquri.”