۞قَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلۡأَرۡذَلُونَ
Suka ce: “Yanzu ma yi imani da kai alhali qasqantattu ne mabiyanka?”
Partager :
قَالَ وَمَا عِلۡمِي بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Ya ce: “Ba ni da sani game da abin da suka zamanto suna aikatawa
إِنۡ حِسَابُهُمۡ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّيۖ لَوۡ تَشۡعُرُونَ
“Hisabinsu kawai yana wajen Ubangijina ne; da za ku gane
وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
“Ni kuma ba mai korar muminai ba ne
إِنۡ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٞ
“Ni kawai mai gargaxi ne mai bayyanawa.”
قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمَرۡجُومِينَ
Suka ce: “Ya Nuhu, mun rantse idan ba ka daina (faxar abin da kake faxa) ba, tabbas za ka zamanto daga cikin jefaffu!”
قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوۡمِي كَذَّبُونِ
Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun qaryata ni
فَٱفۡتَحۡ بَيۡنِي وَبَيۡنَهُمۡ فَتۡحٗا وَنَجِّنِي وَمَن مَّعِيَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
“Ka yi hukunci tsakanina da su, kuma Ka tserar da ni tare da muminan da suke tare da ni.”
فَأَنجَيۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ
Sai Muka tserar da shi da waxanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwan da ke maqare (da mutane da dabbobi)
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا بَعۡدُ ٱلۡبَاقِينَ
Sannan bayan haka Muka nutsar da sauran
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin qai
كَذَّبَتۡ عَادٌ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Adawa (ma) sun qaryata manzanni[1]
1- Domin qaryata Annabi Hudu () daidai yake da qaryata duk manzannin Allah, saboda saqo iri xaya suke xauke da shi.
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da xan’uwansu Hudu ya ce da su: “Yanzu ba kwa riqa kiyaye dokokin (Allah) ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai
أَتَبۡنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةٗ تَعۡبَثُونَ
“Yanzu kwa riqa yin dogayen gine-gine a kan tuddai kuna sharholiya?
وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمۡ تَخۡلُدُونَ
“Kuma ku riqa gina ganuwoyi da maka-makan gidaje kamar za ku dawwama?
وَإِذَا بَطَشۡتُم بَطَشۡتُمۡ جَبَّارِينَ
“Idan kuma kuka yi damqa sai kukan yi damqa da tsanani
وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِيٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعۡلَمُونَ
“Kuma ku kiyaye dokokin (Allah) wanda Ya ni’imta ku da abin da kuka sani
أَمَدَّكُم بِأَنۡعَٰمٖ وَبَنِينَ
“Ya ni’imta ku da dabbobin ni’ima da ‘ya’ya
وَجَنَّـٰتٖ وَعُيُونٍ
“Da kuma gonakai da idanuwan ruwa
إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
“Lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma.”
قَالُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡنَآ أَوَعَظۡتَ أَمۡ لَمۡ تَكُن مِّنَ ٱلۡوَٰعِظِينَ
Suka ce: “Mu duk xaya ne a wajenmu; ko ka yi wa’azi ko kuwa kada ka zamanto daga masu wa’azi
إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلۡأَوَّلِينَ
“Wannan ba wani abu ba ne in ban da halayyar mutanen farko
وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ
“Mu kuma ba waxanda za a yi wa azaba ba ne.”
فَكَذَّبُوهُ فَأَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Sai suka qaryata shi, sannan Muka hallaka su. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba