إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتۡ
Idan sama ta tsattsage[1]
1- Watau mala’iku suka yi ta saukowa.
Partager :
وَأَذِنَتۡ لِرَبِّهَا وَحُقَّتۡ
Ta kuma saurari Ubangijinta, kuma ya wajaba (ta saurara)
وَإِذَا ٱلۡأَرۡضُ مُدَّتۡ
Kuma idan qasa aka miqe ta
وَأَلۡقَتۡ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتۡ
Ta kuma jefar da abin da yake cikinta ta wofinta[1]
1- Watau cikinta ya koma fayau babu sauran wani abu.
Ta kuma saurari Ubangijinta kuma ya wajaba (ta saurara)
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدۡحٗا فَمُلَٰقِيهِ
Ya kai mutum, lalle kai mai yin aiki ne tuquru zuwa ga Ubangijinka, to mai haxuwa da Shi ne
فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ
To amma duk wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama
فَسَوۡفَ يُحَاسَبُ حِسَابٗا يَسِيرٗا
To za a yi masa hisabi mai sauqi[1]
1- Watau ta hanyar bijiro ayyukansa a dunqule ba tare da binciken qwaqwaf ba.
وَيَنقَلِبُ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ مَسۡرُورٗا
Ya kuma juyo zuwa ga iyalinsa yana farin ciki
وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ وَرَآءَ ظَهۡرِهِۦ
Amma wanda kuwa aka bai wa littafinsa ta bayan bayansa
فَسَوۡفَ يَدۡعُواْ ثُبُورٗا
To zai yi kiran halaka
وَيَصۡلَىٰ سَعِيرًا
Zai kuma shiga (wutar) Sa’ira
إِنَّهُۥ كَانَ فِيٓ أَهۡلِهِۦ مَسۡرُورًا
Lalle a da shi ya kasance mai farin ciki ne cikin iyalinsa
إِنَّهُۥ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ
Lalle ya yi zaton ba zai koma (ga Allah) ba
بَلَىٰٓۚ إِنَّ رَبَّهُۥ كَانَ بِهِۦ بَصِيرٗا
Haka yake, (zai koma), lalle Ubangijinsa Ya kasance Mai ganin sa ne
فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلشَّفَقِ
To ina rantsuwa da shafaqi
وَٱلَّيۡلِ وَمَا وَسَقَ
Da kuma dare da abin da ya tattara
وَٱلۡقَمَرِ إِذَا ٱتَّسَقَ
Da kuma wata idan ya cika
لَتَرۡكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٖ
Tabbas za ku hau wani mataki bayan wani mataki[1]
1- Watau na halittarsu, sai sun kasance xigon maniyyi, sannan su zama gudan jini sai kuma gudar tsoka, har zuwa cikar halittarsu.
فَمَا لَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
To me ya same su ne ba sa yin imani?
وَإِذَا قُرِئَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقُرۡءَانُ لَا يَسۡجُدُونَۤ۩
Idan kuma an karanta musu Alqur’ani ba sa yin sujjada?
بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُكَذِّبُونَ
A’a, su dai waxanda suka kafirce suna qaryatawa ne
وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يُوعُونَ
Allah kuwa (Shi) Ya fi sanin abin da suke voyewa (a zukatansu)
فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
To ka yi musu albishir da azaba mai raxaxi
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونِۭ
Sai dai waxanda suka yi imani, suka kuma yi ayyuka nagari, to suna da lada marar yankewa