يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُدَّثِّرُ
Ya kai mai lulluva[1]
1- Shi ne Annabi () wanda ya lulluva da tufafinsa don tsoron mala’ikan da ya yi idon huxu da shi a karon farko a kogon Hira.
Partager :
قُمۡ فَأَنذِرۡ
Tashi ka yi gargaxi
وَرَبَّكَ فَكَبِّرۡ
Kuma ka girmama Ubangijinka
وَثِيَابَكَ فَطَهِّرۡ
Ka kuma tsarkake tufafinka
وَٱلرُّجۡزَ فَٱهۡجُرۡ
Ka kuma qaurace wa (bautar) gumaka
وَلَا تَمۡنُن تَسۡتَكۡثِرُ
Kada kuma ka goranta wa (Ubangijinka) da ganin yawan (ayyukanka na qwarai)[1]
1- Watau kada yawansu ya ruxe shi har ya yi rauni wajen tsayuwa da ayyukan da’awa.
وَلِرَبِّكَ فَٱصۡبِرۡ
Ka kuma yi haquri game da Ubangijinka
فَإِذَا نُقِرَ فِي ٱلنَّاقُورِ
To idan an busa qaho
فَذَٰلِكَ يَوۡمَئِذٖ يَوۡمٌ عَسِيرٌ
To wannan ranar rana ce mai tsanani
عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ غَيۡرُ يَسِيرٖ
A kan kafirai, ba mai sauqi ba ce
ذَرۡنِي وَمَنۡ خَلَقۡتُ وَحِيدٗا
Ka bar Ni da wanda Na halitta shi kaxai[1]
1- Watau a cikin mahaifiyarsa ba tare da dukiya ko ‘ya’ya ba. Shi ne Al-Walidu xan Mugira wanda ya addabi Annabi ().
وَجَعَلۡتُ لَهُۥ مَالٗا مَّمۡدُودٗا
Na kuma yi masa baiwa da dukiya maxuxuwa
وَبَنِينَ شُهُودٗا
Da kuma ‘ya’ya masu halartar (tarurruka tare da shi)
وَمَهَّدتُّ لَهُۥ تَمۡهِيدٗا
Na kuma shimfixa masa (kyakkyawar rayuwa) iyakar shinfixawa
ثُمَّ يَطۡمَعُ أَنۡ أَزِيدَ
Sannan yake kwaxayin in qara (masa)
كَلَّآۖ إِنَّهُۥ كَانَ لِأٓيَٰتِنَا عَنِيدٗا
Faufau! Lalle shi ya kasance mai tsaurin kai ne ga ayoyinmu
سَأُرۡهِقُهُۥ صَعُودًا
Ba da daxewa ba zan xora masa (azaba) mai matsananciyar wahala
إِنَّهُۥ فَكَّرَ وَقَدَّرَ
Lalle shi ya yi tunani, ya kuma auna (a ransa)
فَقُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ
Sai aka la’ane shi, yaya ya yi irin wannan awon?
ثُمَّ قُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ
Sannan aka kuma la’antar sa, yaya ya yi wannan awon?
ثُمَّ نَظَرَ
Sannan ya yi nazari
ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَ
Sannan ya xaure fuska, ya kuma murtuke
ثُمَّ أَدۡبَرَ وَٱسۡتَكۡبَرَ
Sannan ya ba da baya (daga imani) ya kuma yi girman kai
فَقَالَ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ يُؤۡثَرُ
Sai ya ce: “Wannan (Alqur’ani) ba komai ba ne sai sihiri da aka samo (daga wasu)
إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا قَوۡلُ ٱلۡبَشَرِ
“Wannan ba komai ba ne sai magana irin ta mutane.”
سَأُصۡلِيهِ سَقَرَ
(Allah ya ce): Da sannu zan shigar da shi (wutar) Saqara
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سَقَرُ
Me ya sanar da kai abin da ake ce wa Saqara?
لَا تُبۡقِي وَلَا تَذَرُ
Ba ta ragewa kuma ba ta barin (komai)
لَوَّاحَةٞ لِّلۡبَشَرِ
Mai xaxxaye fata ce
عَلَيۡهَا تِسۡعَةَ عَشَرَ
Akwai (mala’iku) goma sha tara suna tsaron ta