Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحۡصُواْ ٱلۡعِدَّةَۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ رَبَّكُمۡۖ لَا تُخۡرِجُوهُنَّ مِنۢ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخۡرُجۡنَ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ لَا تَدۡرِي لَعَلَّ ٱللَّهَ يُحۡدِثُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ أَمۡرٗا

Ya kai wannan Annabi, (ka ce da jama’arka): “Idan za ku saki mata sai ku sake su a farkon iddarsu[1], kuma ku kula da kiyaye qidaya idda[2]; kuma ku kiyaye dokokin Ubangijinku; kada ku fitar da su daga xakunansu, su ma kada su fita sai dai idan sun aikata alfasha bayayyananna. Waxannan kuwa su ne iyakokin Allah. Wanda kuwa duk ya qetare iyakokin Allah, to haqiqa ya zalunci kansa. Ba ka sani ba ko Allah zai farar da wani al’amari bayan wannan[3]


1- Watau lokacin da suka yi tsarkin haila wanda kuma ba su sadu da su ba a cikinsa, ko kuma idan ciki ya bayyana.


2- Domin su iya dawo da matansu kafin qarewarta idan suna buqatar yin haka.


3- Watau Allah ya sake kawo jituwa a tsakanin mijin da matar su fahimci juna su mayar da aurensu.


Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 2

فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ فَارِقُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖ وَأَشۡهِدُواْ ذَوَيۡ عَدۡلٖ مِّنكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلشَّهَٰدَةَ لِلَّهِۚ ذَٰلِكُمۡ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مَخۡرَجٗا

Idan kuma sun kusa isa qarshen iddarsu, to ku riqe su da kyautatawa (ku yi kome), ko kuma ku rabu da su da kyautatawa, kuma ku kafa shaidar adilai guda biyu daga cikinku, ku kuma tsayar da shaidarku saboda Allah. Wannan shi ne ake yin wa’azi da shi ga wanda ya kasance yana yin imani da Allah da ranar lahira. Wanda kuma ya kiyaye dokokin Allah to zai sanya masa mafita



Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 3

وَيَرۡزُقۡهُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَحۡتَسِبُۚ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَهُوَ حَسۡبُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَٰلِغُ أَمۡرِهِۦۚ قَدۡ جَعَلَ ٱللَّهُ لِكُلِّ شَيۡءٖ قَدۡرٗا

Ya kuma arzuta shi ta inda ba ya tsammani. Duk wanda kuma ya dogara ga Allah to Shi Ya ishe shi. Lalle Allah Mai zartar da al’amarinsa ne. Haqiqa kuma Allah Ya sanya iyaka ga kowane abu



Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 4

وَٱلَّـٰٓـِٔي يَئِسۡنَ مِنَ ٱلۡمَحِيضِ مِن نِّسَآئِكُمۡ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَٰثَةُ أَشۡهُرٖ وَٱلَّـٰٓـِٔي لَمۡ يَحِضۡنَۚ وَأُوْلَٰتُ ٱلۡأَحۡمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مِنۡ أَمۡرِهِۦ يُسۡرٗا

Waxanda kuma suka xebe qauna ta yin al’ada daga matanku, idan kun yi kokwanto, to iddarsu wata uku ne, da kuma waxanda ba su tava yin al’ada ba. Mata masu ciki kuma qarewar iddarsu ita ce haife cikinsu[1]. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai sanya masa sauqi game da al’amarinsa


1- Hakanan iddar matar da mijinta ya rasu.


Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 5

ذَٰلِكَ أَمۡرُ ٱللَّهِ أَنزَلَهُۥٓ إِلَيۡكُمۡۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يُكَفِّرۡ عَنۡهُ سَيِّـَٔاتِهِۦ وَيُعۡظِمۡ لَهُۥٓ أَجۡرًا

Wannan shi ne hukuncin Allah da Ya saukar da shi a gare ku. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai kankare masa zunubbansa Ya kuma girmama masa lada



Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 6

أَسۡكِنُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ سَكَنتُم مِّن وُجۡدِكُمۡ وَلَا تُضَآرُّوهُنَّ لِتُضَيِّقُواْ عَلَيۡهِنَّۚ وَإِن كُنَّ أُوْلَٰتِ حَمۡلٖ فَأَنفِقُواْ عَلَيۡهِنَّ حَتَّىٰ يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ فَإِنۡ أَرۡضَعۡنَ لَكُمۡ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ وَأۡتَمِرُواْ بَيۡنَكُم بِمَعۡرُوفٖۖ وَإِن تَعَاسَرۡتُمۡ فَسَتُرۡضِعُ لَهُۥٓ أُخۡرَىٰ

Ku zaunar da su (matayen) a inda kuka zauna daidai da samunku, kada kuma ku cuce su don ku quntata musu. Idan kuwa sun kasance masu ciki to sai ku ciyar da su har sai sun haife cikinsu. Sannan idan sun shayar muku da (‘ya’yanku) sai ku ba su ladansu; ku kuma daidaita a tsakaninku ta hanya tagari; idan kuma kuka kasa daidaitawa, to wata mai shayarwar sai ta shayar masa



Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 7

لِيُنفِقۡ ذُو سَعَةٖ مِّن سَعَتِهِۦۖ وَمَن قُدِرَ عَلَيۡهِ رِزۡقُهُۥ فَلۡيُنفِقۡ مِمَّآ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُۚ لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا مَآ ءَاتَىٰهَاۚ سَيَجۡعَلُ ٱللَّهُ بَعۡدَ عُسۡرٖ يُسۡرٗا

Mawadaci ya ciyar daidai da wadatarsa; wanda kuwa aka quntata masa arzikinsa, to ya ciyar daidai da abin da Allah Ya ba shi. Allah ba Ya xora wa rai sai gwargwadon abin da Ya ba shi. Kuma da sannu Allah zai sanya sauqi bayan tsanani



Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 8

وَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ عَتَتۡ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهَا وَرُسُلِهِۦ فَحَاسَبۡنَٰهَا حِسَابٗا شَدِيدٗا وَعَذَّبۡنَٰهَا عَذَابٗا نُّكۡرٗا

Alqaryu da dama sun yi wa Ubangijinsu da manzanninsa taurin kai, sai Muka yi musu hisabi mai tsanani, Muka azabtar da su azaba mummuna



Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 9

فَذَاقَتۡ وَبَالَ أَمۡرِهَا وَكَانَ عَٰقِبَةُ أَمۡرِهَا خُسۡرًا

Saboda haka su xanxani qarshen al’amarinsu, qarshen al’amarin nasu kuma ya zama tavewa



Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 10

أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدٗاۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ يَـٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ قَدۡ أَنزَلَ ٱللَّهُ إِلَيۡكُمۡ ذِكۡرٗا

Allah Ya tanadar musu azaba mai tsanani; saboda haka ku kiyaye dokokin Allah ya ku ma’abota hankula waxanda suka yi imani. Haqiqa Allah Ya saukar muku da tunatarwa



Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 11

رَّسُولٗا يَتۡلُواْ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ مُبَيِّنَٰتٖ لِّيُخۡرِجَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۚ وَمَن يُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ وَيَعۡمَلۡ صَٰلِحٗا يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ قَدۡ أَحۡسَنَ ٱللَّهُ لَهُۥ رِزۡقًا

(Shi ne) Manzo da yake karanta muku ayoyin Allah bayyanannu, don ya fitar da waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari daga duffai zuwa haske. Duk kuwa wanda ya yi imani da Allah ya kuma yi aiki nagari to zai shigar da shi gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu suna masu dawwama a cikinsu har abada. (Wanda aka yi wa haka kuwa) haqiqa Allah Ya kyautata masa arzikinsa



Sourate: Suratux Xalaq

Verset : 12

ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖ وَمِنَ ٱلۡأَرۡضِ مِثۡلَهُنَّۖ يَتَنَزَّلُ ٱلۡأَمۡرُ بَيۡنَهُنَّ لِتَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ وَأَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَحَاطَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عِلۡمَۢا

Allah ne Wanda Ya halicci sammai bakwai, qasa ma Ya halicci kwatankwacinsu (watau sammai), umarni yana sauka a tsakaninsu, don ku san cewa, Allah Mai iko ne a kan komai, kuma haqiqa Allah iliminsa ya kewaye kowane abu