الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ وَقُرۡءَانٖ مُّبِينٖ
ALIF LAM RA[1]. Waxannan ayoyin Littafi ne, kuma abin karatu ne mabayyani
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
Partager :
رُّبَمَا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ كَانُواْ مُسۡلِمِينَ
Waxanda suka kafirta za su riqa burin ina ma da sun zama Musulmai[1]
1- Watau a ranar alqiyama ko kuma lokacin mutuwarsa.
ذَرۡهُمۡ يَأۡكُلُواْ وَيَتَمَتَّعُواْ وَيُلۡهِهِمُ ٱلۡأَمَلُۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ
Bar su su ci kuma su ji daxi, buri kuma ya shagaltar da su ; sai dai ba da daxewa ba za su sani
وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا وَلَهَا كِتَابٞ مَّعۡلُومٞ
Ba wata alqarya da Muka hallakar face tana da wani sanannen lokaci (a wurin Allah)
مَّا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ
Ba wata al’umma da za ta riga lokacin da aka iyakance mata ko su jinkirta bayansa
وَقَالُواْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِي نُزِّلَ عَلَيۡهِ ٱلذِّكۡرُ إِنَّكَ لَمَجۡنُونٞ
Suka kuma ce: “Ya kai wanda aka saukar wa da Alqur’ani, lalle kai tabbas mahaukaci ne
لَّوۡمَا تَأۡتِينَا بِٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
“Me zai hana ka zo mana da mala’iku idan kana daga cikin masu gaskiya?”
مَا نُنَزِّلُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَمَا كَانُوٓاْ إِذٗا مُّنظَرِينَ
(Allah ya ce): “Ba ma saukar da mala’iku sai da gaskiya[1]; inda kuwa haka ya faru, to ba za a saurara musu ba.”
1- Watau sai idan lokacin da za a hallaka su ya zo.
إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا ٱلذِّكۡرَ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ
Lalle Mu Muka saukar da Alqur’ani, lalle kuma tabbas Mu za Mu kiyaye shi
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ فِي شِيَعِ ٱلۡأَوَّلِينَ
Haqiqa kuma Mun aiko (manzanni) a gabaninka cikin al’ummun farko
وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Ba kuwa wani manzo da zai zo musu sai sun zamanto suna yi masa izgili
كَذَٰلِكَ نَسۡلُكُهُۥ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Kamar haka ne Muke shigar da shi cikin zukatan kafirai
لَا يُؤۡمِنُونَ بِهِۦ وَقَدۡ خَلَتۡ سُنَّةُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Ba za su yi imani da shi ba; haqiqa kuma hanyar (sakamakon) mutanen farko ta gabata (wato hallakarwa)
وَلَوۡ فَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَابٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فَظَلُّواْ فِيهِ يَعۡرُجُونَ
Idan da Mun buxe musu qofar sama har suka dinga hawa ta cikinta
لَقَالُوٓاْ إِنَّمَا سُكِّرَتۡ أَبۡصَٰرُنَا بَلۡ نَحۡنُ قَوۡمٞ مَّسۡحُورُونَ
Tabbas da sun ce: “Ai an yi mana rufa-ido ne kawai; a’a, kai mu dai mutane ne da aka sihirce.”
وَلَقَدۡ جَعَلۡنَا فِي ٱلسَّمَآءِ بُرُوجٗا وَزَيَّنَّـٰهَا لِلنَّـٰظِرِينَ
Haqiqa kuma Mun sanya taurari a sama, Muka kuma qawata ta ga masu gani
وَحَفِظۡنَٰهَا مِن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٍ
Kuma Muka kiyaye ta daga duk wani shaixani la’ananne
إِلَّا مَنِ ٱسۡتَرَقَ ٱلسَّمۡعَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ مُّبِينٞ
Sai dai wanda ya yi satar sauraro, sannan sai tauraro mai harshen wuta ya biyo shi
وَٱلۡأَرۡضَ مَدَدۡنَٰهَا وَأَلۡقَيۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ شَيۡءٖ مَّوۡزُونٖ
Qasa kuma Mun shimfixa ta Muka sanya manyan duwatsu a cikinta, Muka kuma tsiro da kowane abu a cikinta qayyadajje
وَجَعَلۡنَا لَكُمۡ فِيهَا مَعَٰيِشَ وَمَن لَّسۡتُمۡ لَهُۥ بِرَٰزِقِينَ
Muka kuma sanya muku kayan rayuwa a cikinta, da kuma wanda ba ku ne kuke arzuta shi ba (wato bayi da dabbobi)
وَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا عِندَنَا خَزَآئِنُهُۥ وَمَا نُنَزِّلُهُۥٓ إِلَّا بِقَدَرٖ مَّعۡلُومٖ
Babu wani abu wanda taskokinsa ba a wurinmu suke ba, kuma ba ma saukar da shi sai daidai wani gwargwado sananne
وَأَرۡسَلۡنَا ٱلرِّيَٰحَ لَوَٰقِحَ فَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَسۡقَيۡنَٰكُمُوهُ وَمَآ أَنتُمۡ لَهُۥ بِخَٰزِنِينَ
Muka kuma aiko da iska mai yin barbara (ga giza-gizai), sai Muka saukar da ruwa daga sama Muka shayar da ku da shi, ba kuma ku ne masu taskance shi ba
وَإِنَّا لَنَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَنَحۡنُ ٱلۡوَٰرِثُونَ
Lalle kuma tabbas Mu Muke rayawa kuma Muke kashewa, Mu ne kuma Masu gaje (komai)
وَلَقَدۡ عَلِمۡنَا ٱلۡمُسۡتَقۡدِمِينَ مِنكُمۡ وَلَقَدۡ عَلِمۡنَا ٱلۡمُسۡتَـٔۡخِرِينَ
Haqiqa kuma Mun san marigaya daga cikinku kuma haqiqa Mun san masu biyowa baya[1]
1- Watau Allah () ya san waxanda za a riga haihuwarsu su riga mutuwa, ya san kuma waxanda za a haife su, daga baya su mutu.
وَإِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَحۡشُرُهُمۡۚ إِنَّهُۥ حَكِيمٌ عَلِيمٞ
Lalle Ubangijinka kuma Shi zai tattara su. Lalle shi Mai hikima ne, Masani
وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن صَلۡصَٰلٖ مِّنۡ حَمَإٖ مَّسۡنُونٖ
Kuma haqiqa Mun halicci mutum daga busasshen tavo mai amo na wani yumvu mai wari
وَٱلۡجَآنَّ خَلَقۡنَٰهُ مِن قَبۡلُ مِن نَّارِ ٱلسَّمُومِ
Aljani kuwa Mun halicce shi ne gabanin (halittar mutum) daga wuta mai tsananin zafi
وَإِذۡ قَالَ رَبُّكَ لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ إِنِّي خَٰلِقُۢ بَشَرٗا مِّن صَلۡصَٰلٖ مِّنۡ حَمَإٖ مَّسۡنُونٖ
Kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka ya ce da mala’iku: “Lalle Ni zan halicci mutum daga busasshen tavo mai amo na wani yumvu mai wari
فَإِذَا سَوَّيۡتُهُۥ وَنَفَخۡتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُواْ لَهُۥ سَٰجِدِينَ
“To idan Na daidaita shi Na kuma busa masa daga ruhina, to ku faxi kuna masu sujjada a gare shi.”
فَسَجَدَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ كُلُّهُمۡ أَجۡمَعُونَ
Sai mala’iku dukkaninsu suka yi sujjada gaba xaya