وَٱلۡعَٰدِيَٰتِ ضَبۡحٗا
Na rantse da (dawaki) masu sukuwa suna kukan ciki
Partager :
فَٱلۡمُورِيَٰتِ قَدۡحٗا
Sannan masu bugun qyastu da kofatai[1]
1- Watau suna qyasta wuta da kofatansu idan suka daki duwatsu da su.
فَٱلۡمُغِيرَٰتِ صُبۡحٗا
Sannan masu kai hari da asuba
فَأَثَرۡنَ بِهِۦ نَقۡعٗا
Sai suka tayar da qura da ita (sukawar tasu)
فَوَسَطۡنَ بِهِۦ جَمۡعًا
Sai kuma suka shiga tsakiyar taro (da mahayansu)
إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٞ
Lalle mutum tabbas mai yawan butulci ne ga Ubangijinsa
وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٞ
Lalle kuma shi shaida ne a kan haka
وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلۡخَيۡرِ لَشَدِيدٌ
Lalle shi kuma mai tsananin son alheri ne[1]
1- Watau yana da tsananin son dukiya, wannan ne kuma yake sanya shi rowa.
۞أَفَلَا يَعۡلَمُ إِذَا بُعۡثِرَ مَا فِي ٱلۡقُبُورِ
Shin bai sani ba ne idan aka bankaxo abubuwan da suke cikin qaburbura?
وَحُصِّلَ مَا فِي ٱلصُّدُورِ
Aka kuma tattaro abubuwan da suke cikin qiraza?
إِنَّ رَبَّهُم بِهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّخَبِيرُۢ
Lalle a wannan ranar tabbas Ubangijinsu Masani ne game da su