Sourate: Suratul A’araf

Verset : 151

قَالَ رَبِّ ٱغۡفِرۡ لِي وَلِأَخِي وَأَدۡخِلۡنَا فِي رَحۡمَتِكَۖ وَأَنتَ أَرۡحَمُ ٱلرَّـٰحِمِينَ

Sai ya ce: “Ya Ubangijina, Ka gafarta mini ni da xan’uwana, kuma Ka shigar da mu cikin rahamarka; kuma Kai ne Fiyayyen masu jin qai.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 152

إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ ٱلۡعِجۡلَ سَيَنَالُهُمۡ غَضَبٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَذِلَّةٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُفۡتَرِينَ

Lalle waxannan da suka riqi xan maraqi (abin bauta) fushin Ubangijinsu zai same su da qasqanci a cikin rayuwar duniya. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu qage



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 153

وَٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ ثُمَّ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِهَا وَءَامَنُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ

Waxanda kuma suka aikata munanan ayyuka, sannan suka tuba daga baya, kuma suka yi imani, lalle Ubangijinka bayansa (tuban), tabbas Mai gafara ne, Mai jin qai



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 154

وَلَمَّا سَكَتَ عَن مُّوسَى ٱلۡغَضَبُ أَخَذَ ٱلۡأَلۡوَاحَۖ وَفِي نُسۡخَتِهَا هُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلَّذِينَ هُمۡ لِرَبِّهِمۡ يَرۡهَبُونَ

Yayin kuma da Musa ya huce, sai ya xauki allunan nan (na Attaura); kuma abin da aka rubuta a cikinsu shiriya ne da rahama ga waxanda suke tsoron Ubangijinsu



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 155

وَٱخۡتَارَ مُوسَىٰ قَوۡمَهُۥ سَبۡعِينَ رَجُلٗا لِّمِيقَٰتِنَاۖ فَلَمَّآ أَخَذَتۡهُمُ ٱلرَّجۡفَةُ قَالَ رَبِّ لَوۡ شِئۡتَ أَهۡلَكۡتَهُم مِّن قَبۡلُ وَإِيَّـٰيَۖ أَتُهۡلِكُنَا بِمَا فَعَلَ ٱلسُّفَهَآءُ مِنَّآۖ إِنۡ هِيَ إِلَّا فِتۡنَتُكَ تُضِلُّ بِهَا مَن تَشَآءُ وَتَهۡدِي مَن تَشَآءُۖ أَنتَ وَلِيُّنَا فَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَاۖ وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡغَٰفِرِينَ

Musa kuma ya zavi mutanensa, maza (na musamman) su saba’in don alqawarinmu[1]; to yayin da wata tsawa ta kama su, sai ya ce: “Ya Ubangijina, idan da Ka ga dama da tun tuni Ka hallakar da su har da ni kaina. Yanzu Ka halaka mu saboda abin da wasu wawaye daga cikinmu suka aikata? Lalle wannan ba komai ba ne face jarrabawa daga gare Ka, Kana vatar da wanda Ka ga dama; Kana kuma shiryar da wanda Ka ga dama; Kai ne Majivincin lamarinmu, don haka Ka gafarta mana, kuma Ka ji qan mu, kuma Kai ne Fiyayyen masu gafara


1- Watau ganawa da Allah don su gabatar da uzurinsu game da bautar xan maraqi da suka yi, su wakilci ‘yan’uwansu wajen neman gafarar Allah.


Sourate: Suratul A’araf

Verset : 156

۞وَٱكۡتُبۡ لَنَا فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِنَّا هُدۡنَآ إِلَيۡكَۚ قَالَ عَذَابِيٓ أُصِيبُ بِهِۦ مَنۡ أَشَآءُۖ وَرَحۡمَتِي وَسِعَتۡ كُلَّ شَيۡءٖۚ فَسَأَكۡتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِنَا يُؤۡمِنُونَ

“Kuma Ka rubuta mana kyakkyawan abu a cikin wannan duniyar, haka ma a lahira, lalle mu mun tuba zuwa gare Ka.” (Allah) Ya ce: “Ina saukar da azabata a kan wanda Na ga dama; rahamata kuwa ta yalwaci komai. Don haka da sannu zan rubuta ta ga waxanda suke kiyaye dokokin Allah, kuma suke bayar da zakka da kuma waxanda suke yin imani da ayoyinmu



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 157

ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلرَّسُولَ ٱلنَّبِيَّ ٱلۡأُمِّيَّ ٱلَّذِي يَجِدُونَهُۥ مَكۡتُوبًا عِندَهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ يَأۡمُرُهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَىٰهُمۡ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡخَبَـٰٓئِثَ وَيَضَعُ عَنۡهُمۡ إِصۡرَهُمۡ وَٱلۡأَغۡلَٰلَ ٱلَّتِي كَانَتۡ عَلَيۡهِمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِهِۦ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَٱتَّبَعُواْ ٱلنُّورَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ مَعَهُۥٓ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

“(Su ne) waxanda suke bin Manzo Annabi Ummiyyi, wanda suke samun sa a rubuce a wurinsu a cikin Attaura da Linjila, yana umartar su da kyakkyawan abu, kuma yana hana su mummuna, kuma yana halatta musu daxaxan abubuwa, yana kuma haramta musu qazantattu, kuma yana sauke musu nauyaye-nauyayensu da ququmce-ququmcen da suka kasance a kansu[1]. Don haka waxanda suka yi imani da shi, kuma suka qarfafe shi, suka kuma taimake shi, suka bi hasken da aka saukar tare da shi, waxannan su ne masu rabauta.”


1- Nauyaye-nauyayensu su ne abubuwa masu wuya da aka wajabta musu aiki da su a littafin Attaura. Ququmce-ququmcensu kuwa su ne abubuwan da aka tsananta musu haramcinsu masu kama da ququmi.


Sourate: Suratul A’araf

Verset : 158

قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ

Ka ce: “Ya ku mutane, lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku gaba xaya, wanda Yake da mallakar sammai da qasa, babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Shi ne Yake rayawa, kuma Shi Yake kashewa; don haka ku yi imani da Allah da Manzonsa Annabi Ummiyyi, wanda yake yin imani da Allah da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku zama shiryayyu.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 159

وَمِن قَوۡمِ مُوسَىٰٓ أُمَّةٞ يَهۡدُونَ بِٱلۡحَقِّ وَبِهِۦ يَعۡدِلُونَ

Kuma daga cikin mutanen Musa akwai wata jama’a waxanda suke shiryarwa da gaskiya, da kuma ita ne suke yin hukunci na adalci[1]


1- Su ne waxanda suka yi Imani da Annabi Muhammadu ().


Sourate: Suratul A’araf

Verset : 160

وَقَطَّعۡنَٰهُمُ ٱثۡنَتَيۡ عَشۡرَةَ أَسۡبَاطًا أُمَمٗاۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ إِذِ ٱسۡتَسۡقَىٰهُ قَوۡمُهُۥٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡحَجَرَۖ فَٱنۢبَجَسَتۡ مِنۡهُ ٱثۡنَتَا عَشۡرَةَ عَيۡنٗاۖ قَدۡ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٖ مَّشۡرَبَهُمۡۚ وَظَلَّلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلۡغَمَٰمَ وَأَنزَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَنَّ وَٱلسَّلۡوَىٰۖ كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

Mun kuma karkasa su qabilu goma sha biyu daban-daban[1], sai Muka kuma yi wahayi ga Musa yayin da mutanensa suka nemi ya shayar da su ruwa cewa: “Ka doki dutse da sandarka,” sai idanun ruwa goma sha biyu suka vuvvugo daga jikinsa. Haqiqa kowace qabila ta san mashayarta. Muka kuma yi musu inuwa da girgije, kuma Muka saukar musu da darva da tsuntsayen salwa; (muka ce:) “Ku ci daga daddaxan abin da Muka arzurta ku da shi.” Kuma ba su zalunce Mu ba, sai dai kansu suka kasance suna zalunta


1- Su ne zuriyyar ‘ya’yan Annabi Ya’aqub () goma sha biyu.


Sourate: Suratul A’araf

Verset : 161

وَإِذۡ قِيلَ لَهُمُ ٱسۡكُنُواْ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةَ وَكُلُواْ مِنۡهَا حَيۡثُ شِئۡتُمۡ وَقُولُواْ حِطَّةٞ وَٱدۡخُلُواْ ٱلۡبَابَ سُجَّدٗا نَّغۡفِرۡ لَكُمۡ خَطِيٓـَٰٔتِكُمۡۚ سَنَزِيدُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma ka tuna lokacin da aka ce musu: “Ku zauna a wannan alqarya, kuma ku ci daga gare ta a duk inda kuka ga dama, ku kuma ce: Hixxa (wato Allah Ka share mana laifukanmu), ku kuma shiga ta qofar alqaryar kuna masu sujjada, za Mu gafarta muku zunubanku, kuma za Mu qara wa masu kyautatawa.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 162

فَبَدَّلَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡهُمۡ قَوۡلًا غَيۡرَ ٱلَّذِي قِيلَ لَهُمۡ فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِجۡزٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُواْ يَظۡلِمُونَ

Sai waxanda suka yi zalunci a cikinsu suka canja magana daban da wadda aka faxa musu, sai Muka aiko musu da wata azaba daga sama, saboda abin da suka kasance suna yi na zalunci



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 163

وَسۡـَٔلۡهُمۡ عَنِ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِي كَانَتۡ حَاضِرَةَ ٱلۡبَحۡرِ إِذۡ يَعۡدُونَ فِي ٱلسَّبۡتِ إِذۡ تَأۡتِيهِمۡ حِيتَانُهُمۡ يَوۡمَ سَبۡتِهِمۡ شُرَّعٗا وَيَوۡمَ لَا يَسۡبِتُونَ لَا تَأۡتِيهِمۡۚ كَذَٰلِكَ نَبۡلُوهُم بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ

Kuma ka tambaye su game da (mutanen) alqaryar nan wadda take dab da gavar teku, yayin da suke qetare iyaka a ranar Asabar, yayin da kifayensu suke zuwa a ranar Asabar baja-baja, amma ranar da ba Asabar ba kuwa ba sa zuwa. Kamar haka ne muka jarrabe su saboda abin da suka kasance suna yi na fasiqanci



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 164

وَإِذۡ قَالَتۡ أُمَّةٞ مِّنۡهُمۡ لِمَ تَعِظُونَ قَوۡمًا ٱللَّهُ مُهۡلِكُهُمۡ أَوۡ مُعَذِّبُهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدٗاۖ قَالُواْ مَعۡذِرَةً إِلَىٰ رَبِّكُمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ

Kuma ka tuna lokacin da wata jama’a cikinsu suka ce: “Don me za ku riqa wa’azi ga waxansu mutanen da idan Allah Ya ga dama sai Ya hallakar da su ko Ya yi musu azaba mai tsanani?” Sai suka ce: “Don yanke hanzari ne a wurin Ubangijinku ko watakila kuma sa kiyaye dokokin Allah.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 165

فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِۦٓ أَنجَيۡنَا ٱلَّذِينَ يَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلسُّوٓءِ وَأَخَذۡنَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ بِعَذَابِۭ بَـِٔيسِۭ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ

To yayin da suka yi watsi da abin da aka yi musu wa’azi da shi, sai Muka tserar da waxanda suke hana mummunan aiki, Muka kuma kama waxanda suka yi zalunci, da wata mummunar azaba, saboda abin da suka riqa yi na fasiqanci



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 166

فَلَمَّا عَتَوۡاْ عَن مَّا نُهُواْ عَنۡهُ قُلۡنَا لَهُمۡ كُونُواْ قِرَدَةً خَٰسِـِٔينَ

To yayin da suka yi tsaurin kai a kan abin da aka hana su, sai Muka ce da su: “Ku zama birrai, qasqantattu.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 167

وَإِذۡ تَأَذَّنَ رَبُّكَ لَيَبۡعَثَنَّ عَلَيۡهِمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَن يَسُومُهُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِۗ إِنَّ رَبَّكَ لَسَرِيعُ ٱلۡعِقَابِ وَإِنَّهُۥ لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ

Kuma ka tuna lokacin da Ubangijinka Ya yi shela, lalle zai aiko musu da wanda zai xanxana musu mummunar azaba, har ya zuwa ranar tashin alqiyama. Lalle Ubangijinka Mai gaggawar uquba ne, kuma lalle shi tabbas Mai gafara ne, Mai jin qai



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 168

وَقَطَّعۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ أُمَمٗاۖ مِّنۡهُمُ ٱلصَّـٰلِحُونَ وَمِنۡهُمۡ دُونَ ذَٰلِكَۖ وَبَلَوۡنَٰهُم بِٱلۡحَسَنَٰتِ وَٱلسَّيِّـَٔاتِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

Kuma Mun rarraba su qabilu daban-daban a bayan qasa; a cikinsu akwai salihai, kuma daga cikinsu akwai koma bayan haka; kuma Mun jarrabe su da kyawawan abubuwa da munana, don su komo (zuwa hanya)



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 169

فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٞ وَرِثُواْ ٱلۡكِتَٰبَ يَأۡخُذُونَ عَرَضَ هَٰذَا ٱلۡأَدۡنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغۡفَرُ لَنَا وَإِن يَأۡتِهِمۡ عَرَضٞ مِّثۡلُهُۥ يَأۡخُذُوهُۚ أَلَمۡ يُؤۡخَذۡ عَلَيۡهِم مِّيثَٰقُ ٱلۡكِتَٰبِ أَن لَّا يَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّ وَدَرَسُواْ مَا فِيهِۗ وَٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Sai waxansu bara-gurbi suka maye bayansu, sun gaji littafin (Attaura), suna karvar abin duniya, suna kuma cewa: “Za a gafarta mana.” Kuma idan wani abin duniyar irinsa ya zo musu sai su sake karvar sa. Shin yanzu ba a xauki alqawari daga wurinsu ba a cikin littafin (Attaura) cewa, kada su faxi wata magana game da Allah sai gaskiya, kuma sun karanta abin da yake cikinsa? Kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga dukkan waxanda suke da taqawa. Shin ba za ku hankalta ba?



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 170

وَٱلَّذِينَ يُمَسِّكُونَ بِٱلۡكِتَٰبِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُصۡلِحِينَ

Waxanda kuwa suke riqo da Littafi, kuma suke tsayar da salla, to lalle Mu ba ma tozarta ladan masu gyara



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 171

۞وَإِذۡ نَتَقۡنَا ٱلۡجَبَلَ فَوۡقَهُمۡ كَأَنَّهُۥ ظُلَّةٞ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُۥ وَاقِعُۢ بِهِمۡ خُذُواْ مَآ ءَاتَيۡنَٰكُم بِقُوَّةٖ وَٱذۡكُرُواْ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ

Ka tuna kuma lokacin da Muka xaga dutse a samansu kamar girgije, kuma suka sakankance cewa zai rikito musu, (Muka ce da su): “Ku riqe abin da Muka ba ku da kyau, kuma ku tuna abin da yake cikinsa, don su zamo masu kiyaye dokokin Allah.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 172

وَإِذۡ أَخَذَ رَبُّكَ مِنۢ بَنِيٓ ءَادَمَ مِن ظُهُورِهِمۡ ذُرِّيَّتَهُمۡ وَأَشۡهَدَهُمۡ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ أَلَسۡتُ بِرَبِّكُمۡۖ قَالُواْ بَلَىٰ شَهِدۡنَآۚ أَن تَقُولُواْ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ إِنَّا كُنَّا عَنۡ هَٰذَا غَٰفِلِينَ

Ka tuna kuma lokacin da Ubangijinka Ya fitar da zurriyar ’yan’adam daga tsatsonsu[1], Ya kuma sa su suka yi wa kansu shaida, (Ya ce da su): “Yanzu ba Ni ne Ubangijinku ba?” Suka ce: “E Kai ne, mun shaida.” Don kada a ranar alqiyama ku ce: “Lalle mu mun kasance gafalallu a kan wannan.”


1- Bayan Allah () ya halicci Adamu () sai ya shafa bayansa sai duk wani rai da Allah zai halicce shi daga cikin zuriyyarsa har zuwa tashin qiyama ya fito daga tsatsonsa.


Sourate: Suratul A’araf

Verset : 173

أَوۡ تَقُولُوٓاْ إِنَّمَآ أَشۡرَكَ ءَابَآؤُنَا مِن قَبۡلُ وَكُنَّا ذُرِّيَّةٗ مِّنۢ بَعۡدِهِمۡۖ أَفَتُهۡلِكُنَا بِمَا فَعَلَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ

Ko kuma ku ce: “Iyayenmu da suka gabace mu kawai suka yi shirka, mu kuma zurriya ce da muka kasance a bayansu; yanzu Ka hallakar da mu saboda abin da mavarnata suka yi?”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 174

وَكَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ وَلَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

Kuma kamar haka ne Muke bayyana ayoyi, don su komo wa (gaskiya)



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 175

وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ ٱلَّذِيٓ ءَاتَيۡنَٰهُ ءَايَٰتِنَا فَٱنسَلَخَ مِنۡهَا فَأَتۡبَعَهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَكَانَ مِنَ ٱلۡغَاوِينَ

Ka kuma karanta musu labarin wannan da Muka ba shi ayoyinmu, sai ya saluve (jikinsa) daga gare su, sai Shaixan ya bi shi, don haka ya kasance cikin halakakku



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 176

وَلَوۡ شِئۡنَا لَرَفَعۡنَٰهُ بِهَا وَلَٰكِنَّهُۥٓ أَخۡلَدَ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُۚ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ ٱلۡكَلۡبِ إِن تَحۡمِلۡ عَلَيۡهِ يَلۡهَثۡ أَوۡ تَتۡرُكۡهُ يَلۡهَثۚ ذَّـٰلِكَ مَثَلُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَاۚ فَٱقۡصُصِ ٱلۡقَصَصَ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

Kuma da Mun ga dama da Mun xaukaka shi a sanadiyyarsu, amma kuma shi ya karkata zuwa ga duniya, don haka ya biye wa son zuciyarsa. To misalinsa kamar misalin kare ne, idan ka kai masa xauki ya yi lallage, idan ma ka qyale shi zai yi lallage, wannan shi ne misalin waxanda suka qaryata ayoyinmu. Don haka ka ba da labari don su yi tunani



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 177

سَآءَ مَثَلًا ٱلۡقَوۡمُ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَأَنفُسَهُمۡ كَانُواْ يَظۡلِمُونَ

Misalin waxanda suka qaryata ayoyinmu ya munana, kuma kawunansu suka kasance suna zalunta



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 178

مَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِيۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Wanda Allah Ya shiryar, to wannan shi ne shiryayye; wanda kuwa Ya vatar, to waxannan su ne hasararru



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 179

وَلَقَدۡ ذَرَأۡنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ لَهُمۡ قُلُوبٞ لَّا يَفۡقَهُونَ بِهَا وَلَهُمۡ أَعۡيُنٞ لَّا يُبۡصِرُونَ بِهَا وَلَهُمۡ ءَاذَانٞ لَّا يَسۡمَعُونَ بِهَآۚ أُوْلَـٰٓئِكَ كَٱلۡأَنۡعَٰمِ بَلۡ هُمۡ أَضَلُّۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡغَٰفِلُونَ

Kuma lalle haqiqa Mun halitta wa Jahannama da yawa daga cikin aljannu da mutane; ga su da zukata da ba sa hankalta da su, ga kuma idanu da ba sa kallo da su, ga kunnuwa da ba sa sauraro da su. Waxannan kamar dabbobi suke; a’a, sun ma fi (dabbobi) vacewa. Waxannan su ne gafalallu



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 180

وَلِلَّهِ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ فَٱدۡعُوهُ بِهَاۖ وَذَرُواْ ٱلَّذِينَ يُلۡحِدُونَ فِيٓ أَسۡمَـٰٓئِهِۦۚ سَيُجۡزَوۡنَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Allah kuma Yana da sunaye mafiya kyau, don haka ku roqe Shi da su; kuma ku rabu da waxanda suke fanxarewa game da sunayensa; da sannu za a yi musu sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa