Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 91

أَوۡ تَكُونَ لَكَ جَنَّةٞ مِّن نَّخِيلٖ وَعِنَبٖ فَتُفَجِّرَ ٱلۡأَنۡهَٰرَ خِلَٰلَهَا تَفۡجِيرًا

“Ko kuma ya zamana kana da wata gona ta dabinai da inabi, sai kuma ka vuvvugo da qoramu ta tsakiyarta su kwarara sosai



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 92

أَوۡ تُسۡقِطَ ٱلسَّمَآءَ كَمَا زَعَمۡتَ عَلَيۡنَا كِسَفًا أَوۡ تَأۡتِيَ بِٱللَّهِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ قَبِيلًا

“Ko kuma ka rufto da sama a kanmu, kamar yadda ka riya, ta faxo yanki-yanki, ko kuma ka zo da Allah da kuma mala’iku (mu gan su) ido-da-ido!



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 93

أَوۡ يَكُونَ لَكَ بَيۡتٞ مِّن زُخۡرُفٍ أَوۡ تَرۡقَىٰ فِي ٱلسَّمَآءِ وَلَن نُّؤۡمِنَ لِرُقِيِّكَ حَتَّىٰ تُنَزِّلَ عَلَيۡنَا كِتَٰبٗا نَّقۡرَؤُهُۥۗ قُلۡ سُبۡحَانَ رَبِّي هَلۡ كُنتُ إِلَّا بَشَرٗا رَّسُولٗا

“Ko kuma ya zamana kana da wani gida na zinari, ko kuma ka hau sama, ba kuwa za mu amince da hawan naka ba har sai ka saukar mana da wani littafi da za mu karanta shi.” Ka ce (da su): “Tsarki ya tabbata ga Ubangijina, ni ba kowa ba ne face mutum Manzo.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 94

وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤۡمِنُوٓاْ إِذۡ جَآءَهُمُ ٱلۡهُدَىٰٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓاْ أَبَعَثَ ٱللَّهُ بَشَرٗا رَّسُولٗا

Kuma babu abin da ya hana kafirai su yi imani lokacin da shiriya ta zo musu, sai cewar da suka yi: “Yanzu Allah ne zai aiko mutum a matsayin manzo?”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 95

قُل لَّوۡ كَانَ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَلَـٰٓئِكَةٞ يَمۡشُونَ مُطۡمَئِنِّينَ لَنَزَّلۡنَا عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَلَكٗا رَّسُولٗا

Ka ce: “Da mala’iku ne suke tafiya a natse a bayan qasa, to da lalle Mun aiko musu mala’ika daga sama a matsayin manzo.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 96

قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

Ka ce: “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku: Lalle Shi ya zamanto Masani ne ga bayinsa, kuma Mai ganin (abin da suke aikatawa) ne.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 97

وَمَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَلَن تَجِدَ لَهُمۡ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِهِۦۖ وَنَحۡشُرُهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ عُمۡيٗا وَبُكۡمٗا وَصُمّٗاۖ مَّأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ كُلَّمَا خَبَتۡ زِدۡنَٰهُمۡ سَعِيرٗا

Wanda kuwa Allah Ya shiryar to shi ne shiryayye; wanda kuwa Ya vatar to ba za ka sami wani mai taimakon su ba in ban da Shi; za kuma Mu tashe su ranar alqiyama a kan fuskokinsu suna makafi, kurame, bebaye; makomarsu Jahannama; duk sanda ta lafa sai Mu qara musu qunarta



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 98

ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُم بِأَنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَقَالُوٓاْ أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمٗا وَرُفَٰتًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ خَلۡقٗا جَدِيدًا

Wannan ne sakamakonsu saboda lalle sun kafirce wa ayoyinmu, suka kuma ce: “Yanzu idan muka zama qasusuwa kuma rududdugaggu, anya kuwa za a tashe mu a sabuwar halitta?”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 99

۞أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يَخۡلُقَ مِثۡلَهُمۡ وَجَعَلَ لَهُمۡ أَجَلٗا لَّا رَيۡبَ فِيهِ فَأَبَى ٱلظَّـٰلِمُونَ إِلَّا كُفُورٗا

Yanzu ba sa gani cewa Allah wanda Ya halicci sammai da qasa Mai iko ne a kan Ya halicci irinsu? Ya kuma sanya musu wani lokaci wanda ba kokwanto a cikinsa, sai azzalumai suka qi (yin imani) sai kafircewa



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 100

قُل لَّوۡ أَنتُمۡ تَمۡلِكُونَ خَزَآئِنَ رَحۡمَةِ رَبِّيٓ إِذٗا لَّأَمۡسَكۡتُمۡ خَشۡيَةَ ٱلۡإِنفَاقِۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ قَتُورٗا

Ka ce da su: “Idan da ku ne kuka mallaki taskokin rahamar Ubangijina to lalle da kun riqe su qam-qam don tsoron ciyarwa. Mutum kuwa ya tabbata mai tsananin rowa ne



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 101

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ تِسۡعَ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۖ فَسۡـَٔلۡ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ إِذۡ جَآءَهُمۡ فَقَالَ لَهُۥ فِرۡعَوۡنُ إِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰمُوسَىٰ مَسۡحُورٗا

Kuma haqiqa Mun bai wa Musa ayoyi tara bayyanannu; to ka tambayi Banu Isra’ila lokacin da ya zo musu, sai Fir’auna ya ce da shi: “Lalle ni fa ina tsammanin kai Musa sihirtacce ne!”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 102

قَالَ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَآ أَنزَلَ هَـٰٓؤُلَآءِ إِلَّا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ بَصَآئِرَ وَإِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰفِرۡعَوۡنُ مَثۡبُورٗا

(Musa) ya ce: “Haqiqa ka sani ba wanda ya saukar da waxannan (ayoyin) sai Ubangijin sammai da qasa don su zama hujjoji, kuma lalle ina tsammanin kai Fir’auna halakakke ne.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 103

فَأَرَادَ أَن يَسۡتَفِزَّهُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ فَأَغۡرَقۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ جَمِيعٗا

Sai ya yi nufin ya girgiza su a qasar (ta Masar don ya fitar da su daga ciki), to sai Muka nutsar da shi da duk wanda yake tare da shi gaba xaya



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 104

وَقُلۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِۦ لِبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱسۡكُنُواْ ٱلۡأَرۡضَ فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ ٱلۡأٓخِرَةِ جِئۡنَا بِكُمۡ لَفِيفٗا

Muka kuma ce da Banu Isra’ila: “Ku zauna a qasar (ta Falasxinu), to idan lokacin alqiyama ya zo za Mu tattaro ku gaba xaya



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 105

وَبِٱلۡحَقِّ أَنزَلۡنَٰهُ وَبِٱلۡحَقِّ نَزَلَۗ وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا مُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا

Kuma da gaskiya Muka saukar da shi (Alqur’ani), kuma da gaskiya ya sauko. Ba Mu kuma aiko ka ba sai mai yin albishir, mai kuma gargaxi



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 106

وَقُرۡءَانٗا فَرَقۡنَٰهُ لِتَقۡرَأَهُۥ عَلَى ٱلنَّاسِ عَلَىٰ مُكۡثٖ وَنَزَّلۡنَٰهُ تَنزِيلٗا

Kuma Mun saukar da Qur’ani, Mun bayyana shi don ka karanta wa mutane shi a sannu a hankali, Mun kuma saukar da shi daki-daki



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 107

قُلۡ ءَامِنُواْ بِهِۦٓ أَوۡ لَا تُؤۡمِنُوٓاْۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ مِن قَبۡلِهِۦٓ إِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ يَخِرُّونَۤ لِلۡأَذۡقَانِۤ سُجَّدٗاۤ

Ka ce da su: “Ko ku yi imani da shi ko kada ku yi imani da shi (duk xaya ne).” Lalle waxanda aka bai wa ilimi gabaninsa (Yahudu da Nasara)[1] idan ana karanta musu shi suna faxuwa da fuskokinsu suna masu sujjada


1- Watau mutanen kirki daga cikinsu.


Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 108

وَيَقُولُونَ سُبۡحَٰنَ رَبِّنَآ إِن كَانَ وَعۡدُ رَبِّنَا لَمَفۡعُولٗا

Suna kuma cewa: “Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu, lalle alqawarin Ubangijinmu tabbas ya zamanto abin aikatawa ne.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 109

وَيَخِرُّونَ لِلۡأَذۡقَانِ يَبۡكُونَ وَيَزِيدُهُمۡ خُشُوعٗا۩

Suna kuma faxuwa da fuskokinsu suna kuka, Yana kuma qara musu qasqantar da kai



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 110

قُلِ ٱدۡعُواْ ٱللَّهَ أَوِ ٱدۡعُواْ ٱلرَّحۡمَٰنَۖ أَيّٗا مَّا تَدۡعُواْ فَلَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَلَا تَجۡهَرۡ بِصَلَاتِكَ وَلَا تُخَافِتۡ بِهَا وَٱبۡتَغِ بَيۡنَ ذَٰلِكَ سَبِيلٗا

Ka ce: “Ku kira (sunan) Allah ko ku kira (sunan) Arrahaman; kowanne kuka kira to shi Yana da sunaye ne mafiya kyau.” Kada kuma ka xaga muryarka da (karatun) sallarka, kada kuma ka yi shi a voye, ka nemi tsaka-tsakin wannan



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 111

وَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي لَمۡ يَتَّخِذۡ وَلَدٗا وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٞ فِي ٱلۡمُلۡكِ وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلِيّٞ مِّنَ ٱلذُّلِّۖ وَكَبِّرۡهُ تَكۡبِيرَۢا

Kuma ka ce, “Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda bai riqi xa ba, kuma ba Shi da wani abokin tarayya a cikin mulki, kuma ba Shi da wani mataimaki don kare masa qasqanci.” Kuma ka girmama shi girmamawa ta sosai