قَالُواْ تَٱللَّهِ لَقَدۡ ءَاثَرَكَ ٱللَّهُ عَلَيۡنَا وَإِن كُنَّا لَخَٰطِـِٔينَ
Suka ce: “Wallahi haqiqa Allah Ya fifita ka a kanmu, mu kuma lalle mun tabbata masu kuskure!”
قَالَ لَا تَثۡرِيبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡيَوۡمَۖ يَغۡفِرُ ٱللَّهُ لَكُمۡۖ وَهُوَ أَرۡحَمُ ٱلرَّـٰحِمِينَ
Ya ce: “A yau babu wani zargi a kanku; Allah zai yafe muku, Shi ne Mafificin masu rahama
ٱذۡهَبُواْ بِقَمِيصِي هَٰذَا فَأَلۡقُوهُ عَلَىٰ وَجۡهِ أَبِي يَأۡتِ بَصِيرٗا وَأۡتُونِي بِأَهۡلِكُمۡ أَجۡمَعِينَ
“Ku tafi da rigata wannan sannan ku jefa ta a fuskar babana, zai dawo mai gani, ku kuma zo min da iyalanku gaba xaya.”
وَلَمَّا فَصَلَتِ ٱلۡعِيرُ قَالَ أَبُوهُمۡ إِنِّي لَأَجِدُ رِيحَ يُوسُفَۖ لَوۡلَآ أَن تُفَنِّدُونِ
Lokacin da ayarin ya baro (Masar) sai babansu ya ce: “Lalle ina jin qanshin Yusufu; ba don dai kada ku ce na susuce ba!”
قَالُواْ تَٱللَّهِ إِنَّكَ لَفِي ضَلَٰلِكَ ٱلۡقَدِيمِ
Suka ce: “Wallahi mun tabbata ba shakka (har yanzu) kana nan cikin daxaxxiyar rikicewar nan taka!”
فَلَمَّآ أَن جَآءَ ٱلۡبَشِيرُ أَلۡقَىٰهُ عَلَىٰ وَجۡهِهِۦ فَٱرۡتَدَّ بَصِيرٗاۖ قَالَ أَلَمۡ أَقُل لَّكُمۡ إِنِّيٓ أَعۡلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
To lokacin da mai albishir ya zo masa sai ya jefa ta (rigar) a fuskarsa, sai ya dawo yana gani. Ya ce: “Ban gaya muku ba cewa lalle ni na san abin da ku ba ku sani ba game da Allah?”
قَالُواْ يَـٰٓأَبَانَا ٱسۡتَغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَآ إِنَّا كُنَّا خَٰطِـِٔينَ
Suka ce: “Ya babanmu, ka nema mana gafarar zunubanmu, lalle mun zamanto masu kuskure!”
قَالَ سَوۡفَ أَسۡتَغۡفِرُ لَكُمۡ رَبِّيٓۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Ya ce: “Ba da daxewa ba zan nema muku gafarar Ubangijina; lalle Shi ne Mai yawan gafara, Mai jin qai.”
فَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَىٰ يُوسُفَ ءَاوَىٰٓ إِلَيۡهِ أَبَوَيۡهِ وَقَالَ ٱدۡخُلُواْ مِصۡرَ إِن شَآءَ ٱللَّهُ ءَامِنِينَ
Lokacin da suka shiga wurin Yusufu sai ya jawo iyayensa ya kuma ce: “Ku shigo Masar in Allah Ya ga dama kuna amintattu.”
وَرَفَعَ أَبَوَيۡهِ عَلَى ٱلۡعَرۡشِ وَخَرُّواْ لَهُۥ سُجَّدٗاۖ وَقَالَ يَـٰٓأَبَتِ هَٰذَا تَأۡوِيلُ رُءۡيَٰيَ مِن قَبۡلُ قَدۡ جَعَلَهَا رَبِّي حَقّٗاۖ وَقَدۡ أَحۡسَنَ بِيٓ إِذۡ أَخۡرَجَنِي مِنَ ٱلسِّجۡنِ وَجَآءَ بِكُم مِّنَ ٱلۡبَدۡوِ مِنۢ بَعۡدِ أَن نَّزَغَ ٱلشَّيۡطَٰنُ بَيۡنِي وَبَيۡنَ إِخۡوَتِيٓۚ إِنَّ رَبِّي لَطِيفٞ لِّمَا يَشَآءُۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ
Ya kuma xora mahaifansa a kan gadon mulki, suka kuma faxi suna masu gaisuwa a gare shi, ya kuma ce: “Ya babanmu, wannan shi ne fassarar mafarkina na tun tuni. Lalle Ubangijina Ya mai da shi gaskiya; haqiqa kuma Ya kyautata min lokacin da Ya fitar da ni daga kurkuku, Ya kuma zo da ku daga qauye bayan Shaixan ya shiga tsakanina da ‘yan’uwana. Lalle Ubangijina Mai tausasawa ne ga wanda Ya ga dama. Lalle Shi ne Masani, Mai hikima
۞رَبِّ قَدۡ ءَاتَيۡتَنِي مِنَ ٱلۡمُلۡكِ وَعَلَّمۡتَنِي مِن تَأۡوِيلِ ٱلۡأَحَادِيثِۚ فَاطِرَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ أَنتَ وَلِيِّۦ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ تَوَفَّنِي مُسۡلِمٗا وَأَلۡحِقۡنِي بِٱلصَّـٰلِحِينَ
“Ya Ubangijina, haqiqa Ka ba ni wani abu na mulki, Ka kuma sanar da ni wani abu daga fassarar mafarki; Ya Mahaliccin sammai da qasa, Kai ne Majivincina a duniya da lahira; ka karvi raina ina Musulmi, Ka kuma haxa ni da (mutane) salihai.”
ذَٰلِكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡغَيۡبِ نُوحِيهِ إِلَيۡكَۖ وَمَا كُنتَ لَدَيۡهِمۡ إِذۡ أَجۡمَعُوٓاْ أَمۡرَهُمۡ وَهُمۡ يَمۡكُرُونَ
Wannan yana daga labaran gaibu da Muke yi maka wahayinsa; ba ka kuma tare da su lokacin da suka haxa al’amarinsu suna qulle-qullen makirci
وَمَآ أَكۡثَرُ ٱلنَّاسِ وَلَوۡ حَرَصۡتَ بِمُؤۡمِنِينَ
Yawancin mutane ba za su yi imani ba, komai kwaxayinka (ga hakan)
وَمَا تَسۡـَٔلُهُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Kuma ba ka tambayar su lada a kansa (wato Alqur’ani). Shi ba wani abu ne daban ba in ban da gargaxi ga talikai
وَكَأَيِّن مِّنۡ ءَايَةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ يَمُرُّونَ عَلَيۡهَا وَهُمۡ عَنۡهَا مُعۡرِضُونَ
Kuma ayoyi nawa ne a sammai da qasa waxanda (kafirai) suke wucewa ta wajensu, amma suna bijire musu?
وَمَا يُؤۡمِنُ أَكۡثَرُهُم بِٱللَّهِ إِلَّا وَهُم مُّشۡرِكُونَ
Yawancinsu kuma ba sa yin imani da Allah sai (an same su) suna masu shirka (da Shi)
أَفَأَمِنُوٓاْ أَن تَأۡتِيَهُمۡ غَٰشِيَةٞ مِّنۡ عَذَابِ ٱللَّهِ أَوۡ تَأۡتِيَهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ
Yanzu sun amince ne wata azabar Allah mai lulluvewa ta zo musu, ko kuwa alqiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, alhalin su ba su sani ba?
قُلۡ هَٰذِهِۦ سَبِيلِيٓ أَدۡعُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِۚ عَلَىٰ بَصِيرَةٍ أَنَا۠ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِيۖ وَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Ka ce: “Wannan ce hanyata, ina yin kira zuwa ga Allah, bisa hujja, ni da wanda ya bi ni. Tsarki kuma ya tabbata ga Allah, ni kuwa ba na cikin masu shirka.”
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِم مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰٓۗ أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۗ وَلَدَارُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Ba Mu kuma aiko (manzanni) a gabaninka ba sai maza ‘yan birni waxanda Muke yi wa wahayi. Me ya sa (kafirai) ba za su yi tafiya ba a bayan qasa don su ga yadda qarshen waxanda suka rigaye su ya kasance? Lalle kuwa gidan lahira shi ya fi ga waxanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba?
حَتَّىٰٓ إِذَا ٱسۡتَيۡـَٔسَ ٱلرُّسُلُ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ قَدۡ كُذِبُواْ جَآءَهُمۡ نَصۡرُنَا فَنُجِّيَ مَن نَّشَآءُۖ وَلَا يُرَدُّ بَأۡسُنَا عَنِ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Har yayin da manzanni suka xebe qauna (da imanin mutanensu), su kuma (kafiran) suka yi zaton an faxa musu qarya ne (game da zuwan azabar Allah) sai taimakonmu ya zo musu, sai Muka tserar da wanda Muka ga dama; ba kuwa za a kawar da azabarmu daga mutane masu laifi ba
لَقَدۡ كَانَ فِي قَصَصِهِمۡ عِبۡرَةٞ لِّأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِۗ مَا كَانَ حَدِيثٗا يُفۡتَرَىٰ وَلَٰكِن تَصۡدِيقَ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَتَفۡصِيلَ كُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Haqiqa akwai izina a cikin labaransu (annabawa) ga ma’abota hankali. (Alqur’ani) bai zamanto zance ne da ake qirqirar sa ba, sai dai zance ne da yake gaskata abin da ya rigaye shi (na littattafai), da kuma bayanin komai; shiriya ne kuma da rahama ga mutanen da suke yin imani