Sourate: Suratul Anfal

Verset : 61

۞وَإِن جَنَحُواْ لِلسَّلۡمِ فَٱجۡنَحۡ لَهَا وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Idan kuma suka karkato ga sulhu, to sai kai ma ka karkato gare shi, ka kuma dogara ga Allah. Lalle Shi Mai ji ne Masani



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 62

وَإِن يُرِيدُوٓاْ أَن يَخۡدَعُوكَ فَإِنَّ حَسۡبَكَ ٱللَّهُۚ هُوَ ٱلَّذِيٓ أَيَّدَكَ بِنَصۡرِهِۦ وَبِٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Idan kuma suka yi niyyar yaudarar ka, to lalle Allah Ya ishe ka. Shi ne wanda Ya qarfafe ka da taimakonsa da kuma muminai



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 63

وَأَلَّفَ بَيۡنَ قُلُوبِهِمۡۚ لَوۡ أَنفَقۡتَ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا مَّآ أَلَّفۡتَ بَيۡنَ قُلُوبِهِمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ أَلَّفَ بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّهُۥ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Ya kuma haxa tsakanin zukatansu. Idan da za ka kashe duk abin da yake bayan qasa gaba xaya ba za ka iya haxa tsakanin zukatansu ba, amma kuma Allah Ya haxe tsakaninsu. Lalle Shi Mabuwayi ne Mai hikima



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 64

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ حَسۡبُكَ ٱللَّهُ وَمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Ya kai wannan Annabi, Allah Ya ishe ka, kai da kuma muminai waxanda suka bi ka



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 65

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ حَرِّضِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ عَلَى ٱلۡقِتَالِۚ إِن يَكُن مِّنكُمۡ عِشۡرُونَ صَٰبِرُونَ يَغۡلِبُواْ مِاْئَتَيۡنِۚ وَإِن يَكُن مِّنكُم مِّاْئَةٞ يَغۡلِبُوٓاْ أَلۡفٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَفۡقَهُونَ

Ya kai wannan Annabi, ka zaburar da muminai a kan yaqi. Idan daga cikinku akwai (mutum) ashirin masu haquri to za su rinjayi (mutum) xari biyu (kafirai). Idan kuma daga cikinku akwai (mutum) xari to za su rinjayi (mutum) dubu daga waxanda suka kafirta, saboda su mutane ne da ba sa ganewa



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 66

ٱلۡـَٰٔنَ خَفَّفَ ٱللَّهُ عَنكُمۡ وَعَلِمَ أَنَّ فِيكُمۡ ضَعۡفٗاۚ فَإِن يَكُن مِّنكُم مِّاْئَةٞ صَابِرَةٞ يَغۡلِبُواْ مِاْئَتَيۡنِۚ وَإِن يَكُن مِّنكُمۡ أَلۡفٞ يَغۡلِبُوٓاْ أَلۡفَيۡنِ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

Yanzu Allah Ya sassauta muku, Ya kuma san cewa a cikinku akwai raunana, saboda haka idan ya zamanto a cikinku akwai (mutum) xari masu haquri to za su rinjayi (mutum) xari biyu (kafirai). Idan kuma ya kasance akwai (mutum) dubu daga cikinku to za su rinjayi (kafirai) dubu biyu da izinin Allah. Allah kuma Yana tare da masu haquri



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 67

مَا كَانَ لِنَبِيٍّ أَن يَكُونَ لَهُۥٓ أَسۡرَىٰ حَتَّىٰ يُثۡخِنَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ تُرِيدُونَ عَرَضَ ٱلدُّنۡيَا وَٱللَّهُ يُرِيدُ ٱلۡأٓخِرَةَۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Bai kamata ga wani annabi ya kasance yana da wasu fursunonin yaqi ba har sai ya yi kisan (abokan gaba) sosai a bayan qasa. Kuna nufin abin duniya Allah kuma Yana nufin lahira. Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 68

لَّوۡلَا كِتَٰبٞ مِّنَ ٱللَّهِ سَبَقَ لَمَسَّكُمۡ فِيمَآ أَخَذۡتُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Ba don wani hukunci ya riga ya gabata daga Allah ba[1], tabbas da azaba mai girma ta shafe ku game da abin da kuka karva (na fansa)


1- Watau da cewa, Allah ba ya kama muminai da kuskuren da suka yi wajen qoqarin gano hukuncin Allah, sannan ya riga ya yafe wa duk muminan da suka je yaqin Badar.


Sourate: Suratul Anfal

Verset : 69

فَكُلُواْ مِمَّا غَنِمۡتُمۡ حَلَٰلٗا طَيِّبٗاۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

To sai ku ci daga abin da kuka samu na ganima halal, tsattsarka. Kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 70

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّمَن فِيٓ أَيۡدِيكُم مِّنَ ٱلۡأَسۡرَىٰٓ إِن يَعۡلَمِ ٱللَّهُ فِي قُلُوبِكُمۡ خَيۡرٗا يُؤۡتِكُمۡ خَيۡرٗا مِّمَّآ أُخِذَ مِنكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ya kai wannan Annabi, ka ce da fursunonin da suke a hannayenku: “Idan dai har Allah Ya san akwai wani alheri a zukatanku, to zai ba ku fiye da abin da aka karva daga wurinku Ya kuma gafarta muku. Allah kuwa Mai gafara ne Mai jin qai.”



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 71

وَإِن يُرِيدُواْ خِيَانَتَكَ فَقَدۡ خَانُواْ ٱللَّهَ مِن قَبۡلُ فَأَمۡكَنَ مِنۡهُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ

Idan kuwa suna nufin ha’intar ka ne, to haqiqa da can ma sun ha’inci Allah, saboda haka Ya xora (ka) a kansu. Allah kuwa Masani ne Mai hikima



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 72

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَواْ وَّنَصَرُوٓاْ أُوْلَـٰٓئِكَ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَمۡ يُهَاجِرُواْ مَا لَكُم مِّن وَلَٰيَتِهِم مِّن شَيۡءٍ حَتَّىٰ يُهَاجِرُواْۚ وَإِنِ ٱسۡتَنصَرُوكُمۡ فِي ٱلدِّينِ فَعَلَيۡكُمُ ٱلنَّصۡرُ إِلَّا عَلَىٰ قَوۡمِۭ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُم مِّيثَٰقٞۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Lalle waxanda suka yi imani kuma suka yi hijira, suka kuma yi yaqi da dukiyoyinsu da kuma rayukansu don Allah, da waxanda kuma suka sauki (muminai masu hijira) suka kuma taimaka (wajen yaqi), to waxannan masu qaunar juna ne. Waxanda kuma suka yi imani ba su kuma yi hijira ba, to babu jivintar al’amari a tsakaninku har sai sun yi hijira. Idan kuma suka nemi taimakonku cikin (al’amarin) addini to lalle ne ku taimake su, sai dai idan game da wasu mutane ne waxanda yake da akwai wani alqawari a tsakaninku da su. Allah kuma Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 73

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٍۚ إِلَّا تَفۡعَلُوهُ تَكُن فِتۡنَةٞ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَفَسَادٞ كَبِيرٞ

Waxanda kuwa suka kafirta, su masu qaunar juna ne. Idan ku ma ba ku aikata haka ba, to za a samu wata fitina a bayan qasa da kuma wata varna mai girma



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 74

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَواْ وَّنَصَرُوٓاْ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ حَقّٗاۚ لَّهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ

Waxanda kuma suka yi imani kuma suka yi hijira suka kuma yi yaqi saboda Allah, da waxanda kuma suka sauki (masu hijira) suka kuma taimaka, waxannan su ne muminai na gaskiya. Suna da (sakamakon) gafara da kuma arziki na karamci



Sourate: Suratul Anfal

Verset : 75

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنۢ بَعۡدُ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ مَعَكُمۡ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مِنكُمۡۚ وَأُوْلُواْ ٱلۡأَرۡحَامِ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلَىٰ بِبَعۡضٖ فِي كِتَٰبِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمُۢ

Waxanda kuma suka yi imani daga baya, suka kuma yi hijira, suka kuma yi yaqi tare da ku, to waxannan suna cikinku. ‘Yan’uwa na jini kuma su ne suka fi cancantar (gadon) junansu a cikin Littafin Allah. Lalle Allah Masani ne ga komai