Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 61

ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ

Allah ne wanda Ya halitta muku dare don ku natsu a cikinsa, rana kuma don ku ga (yadda za ku yi harka). Lalle Allah Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 62

ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ

Wannan Shi ne Allah Ubangijinku, Mahaliccin komai, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi; to ina ne ake kautar da ku?



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 63

كَذَٰلِكَ يُؤۡفَكُ ٱلَّذِينَ كَانُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ يَجۡحَدُونَ

Kamar haka ne ake karkatar da waxanda suka zamanto suna musanta ayoyin Allah



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 64

ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ قَرَارٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَصَوَّرَكُمۡ فَأَحۡسَنَ صُوَرَكُمۡ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡۖ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Allah ne wanda Ya sanya muku qasa ta zama wurin zama, sama kuma ta zama rufi, Ya kuma suranta ku, sai Ya kyautata surorinku, Ya kuma arzuta ku da daxaxan abubuwa. Wannan fa Shi ne Allah Ubangijinku. To Allah Ubangijin talikai albarkatunsa sun yawaita



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 65

هُوَ ٱلۡحَيُّ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۗ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Shi Rayayye ne, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, sai ku roqe Shi kuna masu tsantsanta addini a gare Shi. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 66

۞قُلۡ إِنِّي نُهِيتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَمَّا جَآءَنِيَ ٱلۡبَيِّنَٰتُ مِن رَّبِّي وَأُمِرۡتُ أَنۡ أُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ka ce: “Lalle ni an hana ni in bauta wa waxanda kuke bauta wa ba Allah ba a yayin da (ayoyi) bayyanannu suka zo min daga Ubangijina, an kuma umarce ni da in miqa wuya ga Ubangijin talikai



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 67

هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ يُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡ ثُمَّ لِتَكُونُواْ شُيُوخٗاۚ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ مِن قَبۡلُۖ وَلِتَبۡلُغُوٓاْ أَجَلٗا مُّسَمّٗى وَلَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

“Shi ne wanda Ya halicce ku daga qasa, sannan daga xigon maniyyi, sannan daga gudan jini, daga nan Ya fito da ku kuna jarirai, sannan don ku kai qarfinku, sannan kuma ku zama tsofaffi. Daga cikinku kuma akwai wanda ake karvar ransa kafin wannan; don kuma ku isa zuwa wani lokaci qayyadajje[1], don kuma ku hankalta


1- Wanda ba za su rage ba ba kuma za su qara ba, watau lokacin mutuwarsu.


Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 68

هُوَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَإِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

“Shi ne wanda Yake rayawa Yake kuma kashewa; to idan zai hukunta wani al’amari sai kawai Ya ce da shi: ‘Kasance’, sai ya kasance.”



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 69

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ أَنَّىٰ يُصۡرَفُونَ

Ba ka ganin waxanda suke jayayya game da ayoyin Allah, to ta yaya ake kautar da su?



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 70

ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِٱلۡكِتَٰبِ وَبِمَآ أَرۡسَلۡنَا بِهِۦ رُسُلَنَاۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

(Su ne) waxanda suka qaryata Alqur’ani da kuma abin da Muka aiko manzanninmu da shi; to ba da daxewa ba za su sani



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 71

إِذِ ٱلۡأَغۡلَٰلُ فِيٓ أَعۡنَٰقِهِمۡ وَٱلسَّلَٰسِلُ يُسۡحَبُونَ

A yayin da ququmai suke a wuyoyinsu, da kuma sarqoqi ana jan su



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 72

فِي ٱلۡحَمِيمِ ثُمَّ فِي ٱلنَّارِ يُسۡجَرُونَ

A cikin tafasasshen ruwan, sannan kuma ana qona su a cikin wuta



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 73

ثُمَّ قِيلَ لَهُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تُشۡرِكُونَ

Sannan kuma a ce da su: “Ina abin da kuka kasance kuna shirka da shi?



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 74

مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالُواْ ضَلُّواْ عَنَّا بَل لَّمۡ نَكُن نَّدۡعُواْ مِن قَبۡلُ شَيۡـٔٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ ٱلۡكَٰفِرِينَ

“Wanda ba Allah ba?” Suka ce: “Sun vace mana; ai ba mu kasance muna bauta wa wani abu ba a da”. Kamar haka ne Allah Yake vatar da kafirai



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 75

ذَٰلِكُم بِمَا كُنتُمۡ تَفۡرَحُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَبِمَا كُنتُمۡ تَمۡرَحُونَ

Wannan fa (ya same ku ne) saboda abin da kuka kasance kuna yin girman kai da shi a bayan qasa ba da wata hujja ba, da kuma abin da kuka kasance kuna yin walwala da shi



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 76

ٱدۡخُلُوٓاْ أَبۡوَٰبَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ فَبِئۡسَ مَثۡوَى ٱلۡمُتَكَبِّرِينَ

(Za a ce da su): “Ku shiga qofofin Jahannama kuna masu dawwama a cikinta”; to makomar masu girman kai ta munana



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 77

فَٱصۡبِرۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۚ فَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيۡنَا يُرۡجَعُونَ

Sai ka yi haquri, lalle alqawarin Allah gaskiya ne. To idan Mun nuna maka sashin abin da Muke yi musu alqawari da shi na narko; ko kuma Mun karvi ranka, to zuwa gare Mu dai za a dawo da su



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 78

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ مِنۡهُم مَّن قَصَصۡنَا عَلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّن لَّمۡ نَقۡصُصۡ عَلَيۡكَۗ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأۡتِيَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ فَإِذَا جَآءَ أَمۡرُ ٱللَّهِ قُضِيَ بِٱلۡحَقِّ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ

Haqiqa Mun aiko manzanni a gabaninka, daga cikinsu akwai waxanda Muka labarta maka akwai kuma daga cikinsu waxanda ba Mu labarta maka ba. Ba zai yiwu ba ga wani manzo ya zo da wata aya sai da izinin Allah. Sannan idan al’amarin Allah ya zo, to sai a yi hukunci da gaskiya, kuma a nan ne mavarnata za su yi asara



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 79

ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَنۡعَٰمَ لِتَرۡكَبُواْ مِنۡهَا وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ

Allah ne wanda Ya halitta muku dabbobin ni’ima don ku hau wasu daga cikinsu, kuma daga cikinsu kuke ci



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 80

وَلَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ وَلِتَبۡلُغُواْ عَلَيۡهَا حَاجَةٗ فِي صُدُورِكُمۡ وَعَلَيۡهَا وَعَلَى ٱلۡفُلۡكِ تُحۡمَلُونَ

Kuna kuma da wasu abubuwan amfani game da su, don kuma ku isa (wurin) da kuke da buqatar isa a cikin zukatanku a kansu, kuma a kansu ne da kuma a kan jiragen ruwa ake xaukar ku



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 81

وَيُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ فَأَيَّ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ تُنكِرُونَ

Yana kuma nuna muku ayoyinsa, to wacce (aya) ce (daga) ayoyin Allah kuke musawa?



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 82

أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوٓاْ أَكۡثَرَ مِنۡهُمۡ وَأَشَدَّ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Shin ba za su yi tafiya ba a bayan qasa sannan su duba yadda qarshen waxanda suke gabaninsu ya zama? Sun zamanto sun fi su yawa, sun kuma fi su tsananin qarfi da barin gurabe a bayan qasa; to abin da suka kasance suna aikatawa bai wadatar musu da komai ba



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 83

فَلَمَّا جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَرِحُواْ بِمَا عِندَهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Sannan lokacin da manzanninsu suka zo musu da (ayoyi) bayyanannu, sai suka nuna farin ciki da ilimin da ke gare su, abin kuma da suka kasance suna yi wa izgili ya saukar musu



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 84

فَلَمَّا رَأَوۡاْ بَأۡسَنَا قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَحۡدَهُۥ وَكَفَرۡنَا بِمَا كُنَّا بِهِۦ مُشۡرِكِينَ

To lokacin da suka ga azabarmu sai suka ce: “Mun yi imani da Allah Shi kaxai, mun kuma kafirce wa abin da muka kasance muna yin shirka da shi.”



Sourate: Suratu Ghafir

Verset : 85

فَلَمۡ يَكُ يَنفَعُهُمۡ إِيمَٰنُهُمۡ لَمَّا رَأَوۡاْ بَأۡسَنَاۖ سُنَّتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي قَدۡ خَلَتۡ فِي عِبَادِهِۦۖ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلۡكَٰفِرُونَ

To imaninsu bai zamanto zai amfane su ba yayin da suka ga azabarmu; wannan sunna ce ta Allah wadda ta shuxe a kan bayinsa. Kafirai kuma sun yi asara a nan