فَلَمَّا تَرَـٰٓءَا ٱلۡجَمۡعَانِ قَالَ أَصۡحَٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدۡرَكُونَ
To lokacin da jama’ar biyu suka ga juna, sai sahabban Musa suka ce: “Lalle tabbas mu za a cim mana.”
Partager :
قَالَ كَلَّآۖ إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهۡدِينِ
(Musa) ya ce: “A’a; Ubangijina Yana tare da ni, zai kuwa shiryar da ni (hanyar tsira).”
فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡبَحۡرَۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرۡقٖ كَٱلطَّوۡدِ ٱلۡعَظِيمِ
Sai Muka yi wahayi ga Musa cewa: “Ka bugi kogin da sandarka;” (da ya buge shi) sai ya dare, kowanne yanki sai ya zama kamar qaton dutse
وَأَزۡلَفۡنَا ثَمَّ ٱلۡأٓخَرِينَ
Muka kuma kusantar da waxancan (watau mutanen Fir’auna) zuwa can (kusa da kogin)
وَأَنجَيۡنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
Muka kuma tserar da Musa da waxanda suke tare da shi gaba xaya
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Sannan Muka nutsar da sauran mutanen (watau Fir’auna da mutanensa)
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma lalle Ubangijika tabbas Shi Mabuwayi ne, Mai rahama
وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ إِبۡرَٰهِيمَ
Kuma ka karanta musu labarin Ibrahimu?
إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَا تَعۡبُدُونَ
Lokacin da ya ce wa babansa da kuma mutanensa: “Me kuke bauta wa?”
قَالُواْ نَعۡبُدُ أَصۡنَامٗا فَنَظَلُّ لَهَا عَٰكِفِينَ
Suka ce: “Muna bauta wa gumaka ne, sai mukan duqufa wajen bautarsu.”
قَالَ هَلۡ يَسۡمَعُونَكُمۡ إِذۡ تَدۡعُونَ
(Ibrahimu) ya ce: “Shin suna jin ku kuwa lokacin da kuke kiran su?
أَوۡ يَنفَعُونَكُمۡ أَوۡ يَضُرُّونَ
“Ko kuwa suna amfanar ku ne, ko suna cutarwa?”
قَالُواْ بَلۡ وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا كَذَٰلِكَ يَفۡعَلُونَ
Suka ce: “A’a; mun sami iyayenmu ne suna aikata kamar haka.”
قَالَ أَفَرَءَيۡتُم مَّا كُنتُمۡ تَعۡبُدُونَ
(Ibrahimu) ya ce: “Yanzu kun ga abin nan da kuka kasance kuna bautawa
أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُمُ ٱلۡأَقۡدَمُونَ
“Ku da iyayenku da suka gabata
فَإِنَّهُمۡ عَدُوّٞ لِّيٓ إِلَّا رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“To lalle su abokan gabata ne sai fa Ubangijin talikai
ٱلَّذِي خَلَقَنِي فَهُوَ يَهۡدِينِ
“Wanda Ya halicce ni, to Shi ne Yake shiryar da ni
وَٱلَّذِي هُوَ يُطۡعِمُنِي وَيَسۡقِينِ
“Kuma wanda Shi ne Yake ciyar da ni kuma Yake shayar da ni
وَإِذَا مَرِضۡتُ فَهُوَ يَشۡفِينِ
“Idan kuma na yi rashin lafiya, to Shi ne zai warkar da ni
وَٱلَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحۡيِينِ
“Kuma wanda zai kashe ni sannan Ya (sake) raya ni
وَٱلَّذِيٓ أَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لِي خَطِيٓـَٔتِي يَوۡمَ ٱلدِّينِ
“Wanda kuma nake kwaxayin Ya gafarta min kurakuraina ranar sakamako
رَبِّ هَبۡ لِي حُكۡمٗا وَأَلۡحِقۡنِي بِٱلصَّـٰلِحِينَ
“Ubangijina Ka hore min ilimi, kuma Ka haxa ni da (bayinka) na gari
وَٱجۡعَل لِّي لِسَانَ صِدۡقٖ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
“Kuma Ka sanya min abin kyakkyawan ambato cikin ‘yan baya
وَٱجۡعَلۡنِي مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ ٱلنَّعِيمِ
“Kuma Ka sanya ni cikin magada Aljannar ni’ima
وَٱغۡفِرۡ لِأَبِيٓ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ
“Kuma Ka gafarta wa babana, lalle shi ya zamo cikin vatattu.[1]
1- Ya yi masa wannan addu’a ne tun gabanin a hana shi, kamar yadda ya zo a cikin Suratut Tauba, aya ta 114.
وَلَا تُخۡزِنِي يَوۡمَ يُبۡعَثُونَ
“Kada kuma Ka kunyata ni ranar da za a tashe su
يَوۡمَ لَا يَنفَعُ مَالٞ وَلَا بَنُونَ
“Ranar da dukiya da ‘ya’yaye ba sa amfani
إِلَّا مَنۡ أَتَى ٱللَّهَ بِقَلۡبٖ سَلِيمٖ
“Sai dai wanda ya zo wa Allah da lafiyayyar zuciya.”
وَأُزۡلِفَتِ ٱلۡجَنَّةُ لِلۡمُتَّقِينَ
Aka kuma kusantar da Aljanna ga masu taqawa