Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 61

وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ قَالَ ءَأَسۡجُدُ لِمَنۡ خَلَقۡتَ طِينٗا

Kuma (ka tuna) lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu.” Sai suka yi sujjadar in ban da Iblis da ya ce: “Yanzu na yi sujjada ga wanda Ka halitta da tavo?”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 62

قَالَ أَرَءَيۡتَكَ هَٰذَا ٱلَّذِي كَرَّمۡتَ عَلَيَّ لَئِنۡ أَخَّرۡتَنِ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَأَحۡتَنِكَنَّ ذُرِّيَّتَهُۥٓ إِلَّا قَلِيلٗا

Ya ce: “Ka gan Ka, wannan da Ka fifita shi a kaina, tabbas idan Ka jinkirta min har zuwa ranar alqiyama to lalle zan karkatar da zuriyarsa, sai dai kaxan (daga cikinsu).”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 63

قَالَ ٱذۡهَبۡ فَمَن تَبِعَكَ مِنۡهُمۡ فَإِنَّ جَهَنَّمَ جَزَآؤُكُمۡ جَزَآءٗ مَّوۡفُورٗا

(Allah) Ya ce: “Je ka (an jinkirta maka xin), sai dai (duk) wanda ya bi ka daga cikinsu to lalle Jahannama ce sakamakonku, wanda yake sakamako ne cikakke



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 64

وَٱسۡتَفۡزِزۡ مَنِ ٱسۡتَطَعۡتَ مِنۡهُم بِصَوۡتِكَ وَأَجۡلِبۡ عَلَيۡهِم بِخَيۡلِكَ وَرَجِلِكَ وَشَارِكۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَوۡلَٰدِ وَعِدۡهُمۡۚ وَمَا يَعِدُهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ إِلَّا غُرُورًا

“Ka kuma yi wasa da hankalin wanda ka sami dama daga cikinsu da muryarka ka kuma jawo su da rundunarka mahaya da na qasa; ka kuma yi tarayya da su cikin dukiyoyi da ‘ya’yaye; ka kuma yi musu alqawari.” Shaixan kuwa ba wani alqawari da yake yi musu sai na ruxi



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 65

إِنَّ عِبَادِي لَيۡسَ لَكَ عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٞۚ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ وَكِيلٗا

“Lalle bayina ba ka da iko a kansu.” Kuma Ubangijinka Ya isa zama Wakili



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 66

رَّبُّكُمُ ٱلَّذِي يُزۡجِي لَكُمُ ٱلۡفُلۡكَ فِي ٱلۡبَحۡرِ لِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا

Ubangijinku Shi ne wanda Yake tafiyar da jirgi a kan kogi don ku nemi falalarsa. Lalle Shi Ya kasance Mai rahama ne a gare ku



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 67

وَإِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فِي ٱلۡبَحۡرِ ضَلَّ مَن تَدۡعُونَ إِلَّآ إِيَّاهُۖ فَلَمَّا نَجَّىٰكُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ أَعۡرَضۡتُمۡۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ كَفُورًا

Idan kuma bala’i ya same ku a cikin kogi sai duk waxanda kuke kira su vace (muku) sai Shi kawai; sannan lokacin da Ya tserar da ku zuwa sarari sai kuka bijire. Kai mutum ya tabbata butulu!



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 68

أَفَأَمِنتُمۡ أَن يَخۡسِفَ بِكُمۡ جَانِبَ ٱلۡبَرِّ أَوۡ يُرۡسِلَ عَلَيۡكُمۡ حَاصِبٗا ثُمَّ لَا تَجِدُواْ لَكُمۡ وَكِيلًا

Yanzu kun amince da cewa (Allah) ba zai rufto muku da wani vangare na tudu ba, ko kuma Ya aiko muku da jifa ta manya-manyan tsakuwoyi, sannan ba za ku sami wani mai tsaro ba?



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 69

أَمۡ أَمِنتُمۡ أَن يُعِيدَكُمۡ فِيهِ تَارَةً أُخۡرَىٰ فَيُرۡسِلَ عَلَيۡكُمۡ قَاصِفٗا مِّنَ ٱلرِّيحِ فَيُغۡرِقَكُم بِمَا كَفَرۡتُمۡ ثُمَّ لَا تَجِدُواْ لَكُمۡ عَلَيۡنَا بِهِۦ تَبِيعٗا

Ko kuma kun amince cewa ba zai mai da ku cikinsa ba (kogin) a karo na biyu, sai Ya aiko muku da qaqqarfar iska, sai Ya nutsar da ku saboda kafircewar da kuka yi, sannan kuma ba za ku sami wani mai nema muku haqqinku ba a wajenmu saboda (halakarwar da Muka yi muku)?



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 70

۞وَلَقَدۡ كَرَّمۡنَا بَنِيٓ ءَادَمَ وَحَمَلۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَفَضَّلۡنَٰهُمۡ عَلَىٰ كَثِيرٖ مِّمَّنۡ خَلَقۡنَا تَفۡضِيلٗا

Haqiqa Mun girmama ‘yan’adam, Muka kuma xauke su (kan ababen hawa) na sarari da na ruwa, Muka kuma arzuta su daga tsarkakan (abubuwa) kuma Muka fifita su a kan wasu da yawa daga abin da Muka halitta nesa ba kusa ba



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 71

يَوۡمَ نَدۡعُواْ كُلَّ أُنَاسِۭ بِإِمَٰمِهِمۡۖ فَمَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَقۡرَءُونَ كِتَٰبَهُمۡ وَلَا يُظۡلَمُونَ فَتِيلٗا

Ranar da za Mu kirawo kowanne (jinsin) mutane da shugabansu, sannan wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama to waxannan za su karanta littafinsu, sannan ba za a zalunce su ko da gwargwadon zaren qwallon dabino ne ba



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 72

وَمَن كَانَ فِي هَٰذِهِۦٓ أَعۡمَىٰ فَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ أَعۡمَىٰ وَأَضَلُّ سَبِيلٗا

To wanda kuwa ya zamanto makaho[1] a wannan (duniya), to shi a lahira ma makaho ne kuma mafi vacewa daga hanyar (gaskiya)


1- Watau ya qi ganin gaskiya ya bi ta.


Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 73

وَإِن كَادُواْ لَيَفۡتِنُونَكَ عَنِ ٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ لِتَفۡتَرِيَ عَلَيۡنَا غَيۡرَهُۥۖ وَإِذٗا لَّٱتَّخَذُوكَ خَلِيلٗا

Ba shakka kuwa sun kusa su fitine ka game da abin da Muka yi maka wahayinsa don ka qaga mana waninsa; da kuwa haka ta faru, to da lalle sun xauke ka masoyi



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 74

وَلَوۡلَآ أَن ثَبَّتۡنَٰكَ لَقَدۡ كِدتَّ تَرۡكَنُ إِلَيۡهِمۡ شَيۡـٔٗا قَلِيلًا

Ba don kuwa Mun tabbatar da kai (a kan umarninmu) ba, haqiqa da saura qiris ka xan karkata gare su



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 75

إِذٗا لَّأَذَقۡنَٰكَ ضِعۡفَ ٱلۡحَيَوٰةِ وَضِعۡفَ ٱلۡمَمَاتِ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ عَلَيۡنَا نَصِيرٗا

To da lalle kuwa Mun xanxana maka ninkin (azabar) rayuwa da kuma ninkin (azabar) mutuwa, sannan ba za ka samu wani mai taimakon ka a kanmu ba



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 76

وَإِن كَادُواْ لَيَسۡتَفِزُّونَكَ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ لِيُخۡرِجُوكَ مِنۡهَاۖ وَإِذٗا لَّا يَلۡبَثُونَ خِلَٰفَكَ إِلَّا قَلِيلٗا

Ba shakka sun kusa su tunzura ka daga qasar (ta Makka) don su fitar da kai daga cikinta; da kuwa sun aikata haka to da ba za su zauna (a cikinta) ba bayanka sai xan lokaci qanqani[1]


1- To amma ba su iya korar sa ba har zuwa lokacin da Allah ya umarce shi da hijira.


Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 77

سُنَّةَ مَن قَدۡ أَرۡسَلۡنَا قَبۡلَكَ مِن رُّسُلِنَاۖ وَلَا تَجِدُ لِسُنَّتِنَا تَحۡوِيلًا

(Wannan ita ce) irin al’adar waxanda Muka aiko gabaninka daga manzanninmu; ba kuwa za ka sami canji a al’adarmu ba



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 78

أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِدُلُوكِ ٱلشَّمۡسِ إِلَىٰ غَسَقِ ٱلَّيۡلِ وَقُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِۖ إِنَّ قُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِ كَانَ مَشۡهُودٗا

Ka tsayar da salla lokacin zawalin rana zuwa duhun dare[1], da kuma karatun sallar Asuba. Lalle (lokacin) karatun sallar asuba ya kasance lokacin halartar (mala’iku)


1- Wannan lokaci ya qunshi sallar azahar da la’asar da magriba da isha’i.


Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 79

وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَتَهَجَّدۡ بِهِۦ نَافِلَةٗ لَّكَ عَسَىٰٓ أَن يَبۡعَثَكَ رَبُّكَ مَقَامٗا مَّحۡمُودٗا

Da daddare kuwa sai ka yi tsayuwar dare da shi (Alqur’anin) qarin (daraja) ne gare ka, tare da qaunar Ubangijinka ya tashe ka a matsayin sha-yabo (watau matsayin mai ceto)



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 80

وَقُل رَّبِّ أَدۡخِلۡنِي مُدۡخَلَ صِدۡقٖ وَأَخۡرِجۡنِي مُخۡرَجَ صِدۡقٖ وَٱجۡعَل لِّي مِن لَّدُنكَ سُلۡطَٰنٗا نَّصِيرٗا

Kuma ka ce: “Ubangijina Ka shigar da ni mashiga ta gaskiya, kuma Ka fitar da ni mafita ta gaskiya, kuma Ka ba ni wata hujja mai taimakawa daga gare ka.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 81

وَقُلۡ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَزَهَقَ ٱلۡبَٰطِلُۚ إِنَّ ٱلۡبَٰطِلَ كَانَ زَهُوقٗا

Kuma ka ce: “Gaskiya ta zo, varna kuma ta watse. Lalle da ma can ita varna ai watsattsiya ce.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 82

وَنُنَزِّلُ مِنَ ٱلۡقُرۡءَانِ مَا هُوَ شِفَآءٞ وَرَحۡمَةٞ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ وَلَا يَزِيدُ ٱلظَّـٰلِمِينَ إِلَّا خَسَارٗا

Kuma daga Alqur’ani Muna saukar da abin da yake shi waraka ne da kuma rahama ga muminai; ba kuma zai qari azzalumai (da komai) ba sai tavewa



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 83

وَإِذَآ أَنۡعَمۡنَا عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ أَعۡرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ كَانَ يَـُٔوسٗا

Kuma idan Muka yi wa mutum ni’ima sai ya bijire ya kuma juya kwivinsa; idan kuwa sharri ne ya same shi sai ya zama mai yawan yanke qauna



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 84

قُلۡ كُلّٞ يَعۡمَلُ عَلَىٰ شَاكِلَتِهِۦ فَرَبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَنۡ هُوَ أَهۡدَىٰ سَبِيلٗا

Ka ce: “Kowa ya yi aiki bisa hanyarsa sai dai Ubangijinku (Shi ne) Mafi sanin wanda ya fi shiriya a kan madaidaiciyar hanya.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 85

وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلرُّوحِۖ قُلِ ٱلرُّوحُ مِنۡ أَمۡرِ رَبِّي وَمَآ أُوتِيتُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ إِلَّا قَلِيلٗا

Suna kuma tambayar ka game da ruhi. Ka ce da su: “Shi ruhi yana daga al’amarin Ubangijina, ba abin da aka ba ku na ilimi sai xan kaxan.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 86

وَلَئِن شِئۡنَا لَنَذۡهَبَنَّ بِٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ بِهِۦ عَلَيۡنَا وَكِيلًا

Kuma tabbas da Mun ga dama lalle da Mun tafiyar da abin da Muka yo maka wahayi, sannan ba za ka sami wani mataimaki ba a kanmu (game) da shi



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 87

إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ إِنَّ فَضۡلَهُۥ كَانَ عَلَيۡكَ كَبِيرٗا

Sai dai rahama daga Ubangijinka. Lalle falalarsa gare ka ta zamo mai girma ce



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 88

قُل لَّئِنِ ٱجۡتَمَعَتِ ٱلۡإِنسُ وَٱلۡجِنُّ عَلَىٰٓ أَن يَأۡتُواْ بِمِثۡلِ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لَا يَأۡتُونَ بِمِثۡلِهِۦ وَلَوۡ كَانَ بَعۡضُهُمۡ لِبَعۡضٖ ظَهِيرٗا

Ka ce da su: “Lalle da mutane da aljannu sun haxu kan su kawo irin wannan Alqur’anin, to ba za su zo da irinsa ba, ko da kuwa wasu sun zamanto suna taimaka wa wasu.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 89

وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٖ فَأَبَىٰٓ أَكۡثَرُ ٱلنَّاسِ إِلَّا كُفُورٗا

Kuma haqiqa Mun sarrafa wa mutane kowanne irin misali a cikin wannan Alqur’ani, sai dai yawancin mutane sun qi (komai) sai kafircewa



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 90

وَقَالُواْ لَن نُّؤۡمِنَ لَكَ حَتَّىٰ تَفۡجُرَ لَنَا مِنَ ٱلۡأَرۡضِ يَنۢبُوعًا

Suka kuma ce: “Ba za mu yi imani da kai ba har sai ka vuvvugo mana da idon ruwa daga qasa