Sourate: Suratul Muxaffifin

Verset : 31

وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓاْ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمُ ٱنقَلَبُواْ فَكِهِينَ

Idan kuma sun koma wurin iyalinsu sai su komo suna masu farin ciki[1]


1- Watau saboda izgili da dariya da suka yi wa muminai.


Sourate: Suratul Muxaffifin

Verset : 32

وَإِذَا رَأَوۡهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ

Kuma idan sun gan su sai su ce: “Lalle waxannan vatattu ne.”



Sourate: Suratul Muxaffifin

Verset : 33

وَمَآ أُرۡسِلُواْ عَلَيۡهِمۡ حَٰفِظِينَ

Ba a kuwa aiko su don su zama masu tsaron su ba



Sourate: Suratul Muxaffifin

Verset : 34

فَٱلۡيَوۡمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنَ ٱلۡكُفَّارِ يَضۡحَكُونَ

To a wannan rana ne[1] waxanda suka yi imani za su yi wa kafirai dariya


1- Watau ranar alqiyama.


Sourate: Suratul Muxaffifin

Verset : 35

عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ

Daga kan gadaje suna kallo



Sourate: Suratul Muxaffifin

Verset : 36

هَلۡ ثُوِّبَ ٱلۡكُفَّارُ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ

Shin an saka wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa?