۞يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ خُذُواْ زِينَتَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ وَلَا تُسۡرِفُوٓاْۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Ya ku ‘yan’adam, ku yi adonku a wurin kowane masallaci[1], ku ci, kuma ku sha, amma kada ku yi almubazzaranci. Lalle Shi (Allah) ba ya son masu almubazzaranci
1- Wannan ayar ta sauka ne game da mushirikai masu yin xawafi tsirara, suna cewa, wai bai dace su bauta wa Allah da tufafin da suka yi savo da su ba.
قُلۡ مَنۡ حَرَّمَ زِينَةَ ٱللَّهِ ٱلَّتِيٓ أَخۡرَجَ لِعِبَادِهِۦ وَٱلطَّيِّبَٰتِ مِنَ ٱلرِّزۡقِۚ قُلۡ هِيَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا خَالِصَةٗ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
Ka ce: “Wane ne ya haramta kayan ado na Allah waxanda (Allah) Ya fitar domin bayinsa da kuma daxaxan abubuwa na arziki?” Ka ce: “Waxannan abubuwa na waxanda suka yi imani ne a nan duniya, kuma nasu ne a kevance a ranar lahira.” Kamar haka ne Muke rarrabe ayoyi ga mutanen da suke da sani
قُلۡ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ ٱلۡفَوَٰحِشَ مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَمَا بَطَنَ وَٱلۡإِثۡمَ وَٱلۡبَغۡيَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَأَن تُشۡرِكُواْ بِٱللَّهِ مَا لَمۡ يُنَزِّلۡ بِهِۦ سُلۡطَٰنٗا وَأَن تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Ka ce, “Ubangijina kawai Ya haramta munanan ayyuka na sarari da na voye da savo da cutar wani ba da haqqi ba, kuma (Ya haramta) ku haxa Allah da wani, irin abin da bai saukar da wani dalili a kai ba, kuma (Ya haramta) ku faxi wani abu game da Allah wanda ba ku sani ba.”
وَلِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٞۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ لَا يَسۡتَأۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ
Kuma kowace al’umma tana da lokaci qayyadajje; don haka idan ajalinsu ya zo, ba za a yi musu jinkirin sa’a xaya ba; ba kuma za a gaggauta musu ba
يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ إِمَّا يَأۡتِيَنَّكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَقُصُّونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِي فَمَنِ ٱتَّقَىٰ وَأَصۡلَحَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Ya ku ‘yan’adam, idan har manzanni suka zo muku daga cikinku, suna karanta muku ayoyina, to duk wanda ya yi taqawa, kuma ya kyautata aiki, to babu jin tsoro tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba
وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَٱسۡتَكۡبَرُواْ عَنۡهَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Waxanda kuwa suka qaryata ayoyinmu, kuma suka yi girman kai gare su, waxannan su ne ma’abota wuta; suna masu dawwama a cikinta
فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ يَنَالُهُمۡ نَصِيبُهُم مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُنَا يَتَوَفَّوۡنَهُمۡ قَالُوٓاْ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالُواْ ضَلُّواْ عَنَّا وَشَهِدُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ كَٰفِرِينَ
To wa ya fi wanda ya yi wa Allah qarya zalunci, ko ya qaryata ayoyinsa? Waxannan rabonsu da aka rubuta a cikin littafi zai same su; har ya zuwa lokacin da manzannimu za su zo su karvi ransu, sai su ce: “Ina waxanda kuka kasance kuna kira ba Allah ba?” Sai su ce: “Sun vace mana.” Kuma za su ba da shaida a kansu cewa, lalle su sun kasance kafirai
قَالَ ٱدۡخُلُواْ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِكُم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ فِي ٱلنَّارِۖ كُلَّمَا دَخَلَتۡ أُمَّةٞ لَّعَنَتۡ أُخۡتَهَاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا ٱدَّارَكُواْ فِيهَا جَمِيعٗا قَالَتۡ أُخۡرَىٰهُمۡ لِأُولَىٰهُمۡ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ أَضَلُّونَا فَـَٔاتِهِمۡ عَذَابٗا ضِعۡفٗا مِّنَ ٱلنَّارِۖ قَالَ لِكُلّٖ ضِعۡفٞ وَلَٰكِن لَّا تَعۡلَمُونَ
Sai Ya ce: “Ku shiga cikin jerin al’ummomin da suka shuxe kafinku na aljannu da mutane a cikin wuta.” Ko da yaushe wata al’umma ta shiga (wutar) sai ta la’anci ‘yar’uwarta; har sai lokacin da suka haxu a cikinta gaba xaya, sai na qarshensu su ce wa na farkonsu: “Ya Ubangijinmu, waxannan ne suka vatar da mu, don haka Ka ninka musu azabar wuta.” Sai Ya ce: “Kowanne yana da ninki, sai dai ku ba ku sani ba ne.”
وَقَالَتۡ أُولَىٰهُمۡ لِأُخۡرَىٰهُمۡ فَمَا كَانَ لَكُمۡ عَلَيۡنَا مِن فَضۡلٖ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡسِبُونَ
Sai kuma na farkonsu su ce wa na qarshensu: “Ai ba ku da wani fifiko a kanmu; to ku xanxani azaba saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.”
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَٱسۡتَكۡبَرُواْ عَنۡهَا لَا تُفَتَّحُ لَهُمۡ أَبۡوَٰبُ ٱلسَّمَآءِ وَلَا يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ حَتَّىٰ يَلِجَ ٱلۡجَمَلُ فِي سَمِّ ٱلۡخِيَاطِۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Lalle waxanda suka qaryata ayoyinmu, kuma suka yi girman kai gare su, ba za a buxe musu qofofin sama ba, ba kuma za su shiga Aljanna ba, har sai raqumi ya shige ta qofar allura. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu laifi
لَهُم مِّن جَهَنَّمَ مِهَادٞ وَمِن فَوۡقِهِمۡ غَوَاشٖۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّـٰلِمِينَ
Suna da shimfixa a cikin Jahannama daga samansu kuma akwai wuta mai lulluve su. Kuma kamar haka ne Muke saka wa azzalumai
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Waxanda kuwa suka yi imani, kuma suka aikata kyawawan ayyuka, ba ma xora wa rai, sai abin da zai iya, waxannan su ne ‘yan Aljanna, su masu dawwama ne a cikinta
وَنَزَعۡنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنۡ غِلّٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَقَالُواْ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي هَدَىٰنَا لِهَٰذَا وَمَا كُنَّا لِنَهۡتَدِيَ لَوۡلَآ أَنۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُۖ لَقَدۡ جَآءَتۡ رُسُلُ رَبِّنَا بِٱلۡحَقِّۖ وَنُودُوٓاْ أَن تِلۡكُمُ ٱلۡجَنَّةُ أُورِثۡتُمُوهَا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Muka kuma cire abin da yake cikin qirazansu na qullata, qoramu suna gudana ta qarqashinsu; kuma za su ce: “Yabo ya tabbata ga Allah da Ya shiryar da mu ga wannan, kuma da ba za mu tava shiryuwa ba ba don Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle haqiqa manzannin Ubangijinmu sun zo da gaskiya.” Sai a kira su da cewa: “Waccan Aljannar an gadar muku da ita saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.”
وَنَادَىٰٓ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ أَصۡحَٰبَ ٱلنَّارِ أَن قَدۡ وَجَدۡنَا مَا وَعَدَنَا رَبُّنَا حَقّٗا فَهَلۡ وَجَدتُّم مَّا وَعَدَ رَبُّكُمۡ حَقّٗاۖ قَالُواْ نَعَمۡۚ فَأَذَّنَ مُؤَذِّنُۢ بَيۡنَهُمۡ أَن لَّعۡنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma ‘yan Aljanna za su kira ‘yan wuta cewa: “Haqiqa mu kam mun samu abin da Ubangijinmu Ya yi mana alqawari gaskiya ne, shin ku ma kun sami abin da Ubangijinku Ya yi muku alqawari gaskiya ne?” Sai su ce, “E.” Sai wani mai shela ya yi shela a tsakankaninsu cewa: “La’anar Allah ta tabbata a kan azzalumai
ٱلَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَيَبۡغُونَهَا عِوَجٗا وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ كَٰفِرُونَ
“(Su ne) waxanda suke hana mutane bin tafarkin Allah, kuma suke neman ya zama karkatacce, alhali su masu kafircewa ne da ranar lahira.”
وَبَيۡنَهُمَا حِجَابٞۚ وَعَلَى ٱلۡأَعۡرَافِ رِجَالٞ يَعۡرِفُونَ كُلَّۢا بِسِيمَىٰهُمۡۚ وَنَادَوۡاْ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ أَن سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡۚ لَمۡ يَدۡخُلُوهَا وَهُمۡ يَطۡمَعُونَ
A tsakaninsu kuma akwai wani shamaki. Kuma a kan tozon La’arafi akwai waxansu mazaje suna gane kowane (xan Aljanna da xan wuta) da alamominsu[1]. Kuma sai su kira ‘yan Aljanna cewa: “Amincin Allah ya tabbata a gare ku.” (Lokacin) ba su shige ta ba, amma suna kwaxayin (shigar ta)
1- Waxannan mazaje su ne waxanda kyawawan ayyukansu suka yi daidai da munanansu.
۞وَإِذَا صُرِفَتۡ أَبۡصَٰرُهُمۡ تِلۡقَآءَ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِ قَالُواْ رَبَّنَا لَا تَجۡعَلۡنَا مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Idan kuma an juyar da idanuwansu vangaren ‘yan wuta sai su ce: “Ya Ubangijinmu, kada Ka sanya mu tare da mutane azzalumai.”
وَنَادَىٰٓ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأَعۡرَافِ رِجَالٗا يَعۡرِفُونَهُم بِسِيمَىٰهُمۡ قَالُواْ مَآ أَغۡنَىٰ عَنكُمۡ جَمۡعُكُمۡ وَمَا كُنتُمۡ تَسۡتَكۡبِرُونَ
Sai ‘yan tozon La’arafi su kira waxansu mazaje da suke gane su da alamominsu[1], sai su ce: “Taronku bai wadatar da ku da komai ba, da girman kan da kuka kasance kuna yi
1- Su ne shugabannin mushirikai waxanda sun san su tun a duniya, kuma a nan ma lahira sun shaida su da alamominsu na ‘yan wuta.
أَهَـٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَقۡسَمۡتُمۡ لَا يَنَالُهُمُ ٱللَّهُ بِرَحۡمَةٍۚ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ لَا خَوۡفٌ عَلَيۡكُمۡ وَلَآ أَنتُمۡ تَحۡزَنُونَ
“Shin waxannan ne waxanda kuka riqa yin rantsuwa cewa Allah ba zai sadar da rahamarsa zuwa gare su ba?” Ku shiga Aljanna babu wani tsoro tare da ku, kuma ba za ku yi baqin ciki ba
وَنَادَىٰٓ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ أَنۡ أَفِيضُواْ عَلَيۡنَا مِنَ ٱلۡمَآءِ أَوۡ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُۚ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ حَرَّمَهُمَا عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ
Sai ‘yan wuta su kira ‘yan Aljanna cewa: “Ku kwararo mana ruwa ko abin da Allah Ya arzuta ku da shi.” Sai su ce: “Lalle Allah Ya haramta su ga kafirai.”
ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ دِينَهُمۡ لَهۡوٗا وَلَعِبٗا وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَاۚ فَٱلۡيَوۡمَ نَنسَىٰهُمۡ كَمَا نَسُواْ لِقَآءَ يَوۡمِهِمۡ هَٰذَا وَمَا كَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَجۡحَدُونَ
(Su ne) waxanda suka xauki addininsu sharholiya da wargi, kuma rayuwar duniya ta ruxe su. To a yau za Mu manta da su, kamar yadda suka manta da saduwa da wannan yinin nasu, da kuma jayayya da suka kasance suna yi da ayoyinmu
وَلَقَدۡ جِئۡنَٰهُم بِكِتَٰبٖ فَصَّلۡنَٰهُ عَلَىٰ عِلۡمٍ هُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Lalle haqiqa kuma Mun zo musu da littafin[1] da Muka bayyana shi filla-filla bisa ilimi da shiriya da rahama ga mutanen da suke yin imani
1- Watau Alqur’ani mai girma.
هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا تَأۡوِيلَهُۥۚ يَوۡمَ يَأۡتِي تَأۡوِيلُهُۥ يَقُولُ ٱلَّذِينَ نَسُوهُ مِن قَبۡلُ قَدۡ جَآءَتۡ رُسُلُ رَبِّنَا بِٱلۡحَقِّ فَهَل لَّنَا مِن شُفَعَآءَ فَيَشۡفَعُواْ لَنَآ أَوۡ نُرَدُّ فَنَعۡمَلَ غَيۡرَ ٱلَّذِي كُنَّا نَعۡمَلُۚ قَدۡ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Shin akwai abin da suke jira ne in ba aukuwar abin da ya labarta ba[1]?. Ranar da haqiqanin al’amarin zai zo, waxanda a da suka manta da shi za su ce: “Haqiqa manzannin Ubangijinmu sun zo da gaskiya, shin za mu samu masu ceto da za su cece mu, ko kuma za a mayar da mu, sai mu yi aiki ba irin wanda muka kasance muna yi ba?” Haqiqa sun yi hasarar rayuwarsu, kuma abin da suka kasance suna qirqira ya vace musu
1- Watau zuwan ranar alqiyama.
إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يُغۡشِي ٱلَّيۡلَ ٱلنَّهَارَ يَطۡلُبُهُۥ حَثِيثٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ وَٱلنُّجُومَ مُسَخَّرَٰتِۭ بِأَمۡرِهِۦٓۗ أَلَا لَهُ ٱلۡخَلۡقُ وَٱلۡأَمۡرُۗ تَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Lalle Ubangijinku shi ne Allah wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwanaki shida, sannan sai Ya daidaita a kan Al’arshi[1], Yana lulluve (duhun) dare da (hasken) yini, (kowannensu) yana neman sa (xan’uwansa) a gurguje, da rana da wata da taurari kuma abubuwan horewa ne da umarninsa. Haqiqa halitta da umarni nasa ne. Albarkatun Allah Ubangijin talikai sun yawaita
1- Allah mai girma da buwaya ya daidaita a kan Al’arshi daidaiton da ya dace da girmansa.
ٱدۡعُواْ رَبَّكُمۡ تَضَرُّعٗا وَخُفۡيَةًۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُعۡتَدِينَ
Ku roqi Ubangijinku kuna masu qasqantar da kai, kuma a voye. Lalle Shi ba ya son masu qetare iyaka
وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَا وَٱدۡعُوهُ خَوۡفٗا وَطَمَعًاۚ إِنَّ رَحۡمَتَ ٱللَّهِ قَرِيبٞ مِّنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Kuma kada ku yi varna a bayan qasa bayan gyara ta, kuma ku bauta masa kuna masu tsoro da kwaxayi. Lalle rahamar Allah a kusa take da masu kyautatawa
وَهُوَ ٱلَّذِي يُرۡسِلُ ٱلرِّيَٰحَ بُشۡرَۢا بَيۡنَ يَدَيۡ رَحۡمَتِهِۦۖ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَقَلَّتۡ سَحَابٗا ثِقَالٗا سُقۡنَٰهُ لِبَلَدٖ مَّيِّتٖ فَأَنزَلۡنَا بِهِ ٱلۡمَآءَ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦ مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِۚ كَذَٰلِكَ نُخۡرِجُ ٱلۡمَوۡتَىٰ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Kuma Shi ne Wanda yake aiko da iska don albishir kafin zuwan rahamarsa; har lokacin da ta xauko gizagizai masu nauyi (cike da ruwa), sai Mu kora shi ga wani gari matacce, sai Mu saukar da ruwa da shi, Mu kuma fitar da dukkan ‘ya‘yan itace a sanadiyyarsa. Kamar haka ne Muke fito da matattu don ku wa’azantu
وَٱلۡبَلَدُ ٱلطَّيِّبُ يَخۡرُجُ نَبَاتُهُۥ بِإِذۡنِ رَبِّهِۦۖ وَٱلَّذِي خَبُثَ لَا يَخۡرُجُ إِلَّا نَكِدٗاۚ كَذَٰلِكَ نُصَرِّفُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَشۡكُرُونَ
Wuri kuma mai kyau, tsironsa yana fitowa (kyakkyawa) da izinin Ubangijinsa. Wuri kuwa lalatacce (shukarsa) ba ta fita sai da kyar. Kamar haka ne Muke sarrafa ayoyi ga mutanen da suke yin godiya
لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَقَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
Lalle haqiqa Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya ce: “Ya ku mutanena, ku bautata wa Allah, ba ku da wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, lalle ni ina ji muku tsoron azabar wani yini mai girma.”
قَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِهِۦٓ إِنَّا لَنَرَىٰكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Sai manyan gari cikin mutanensa suka ce: “Lalle mu tabbas muna ganin kana cikin vata mabayyani.”