إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَكَانُواْ كَهَشِيمِ ٱلۡمُحۡتَظِرِ
Lalle Mun aika musu da tsawa guda xaya, sai suka zamo kamar duddugar ciyawa a garken makiyayi
Partager :
وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Haqiqa kuma Mun sauqaqe Alqur’ani don tunatarwa, to ko akwai mai wa’azantuwa?
كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطِۭ بِٱلنُّذُرِ
Mutanen Luxu sun qaryata gargaxi
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ حَاصِبًا إِلَّآ ءَالَ لُوطٖۖ نَّجَّيۡنَٰهُم بِسَحَرٖ
Lalle Mun aika musu da iska cike da duwatsu (ta hallaka su), sai dai iyalin Luxu kaxai Muka tserar da su a lokacin asuba
نِّعۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَاۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي مَن شَكَرَ
(Wannan) ni’ima ce daga wurinmu. Kamar haka Muke saka wa wanda ya yi godiya
وَلَقَدۡ أَنذَرَهُم بَطۡشَتَنَا فَتَمَارَوۡاْ بِٱلنُّذُرِ
Kuma haqiqa ya tsoratar da su irin damqarmu, sai suka yi jayayya da gargaxin (da ya yi musu)
وَلَقَدۡ رَٰوَدُوهُ عَن ضَيۡفِهِۦ فَطَمَسۡنَآ أَعۡيُنَهُمۡ فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ
Haqiqa kuma sun nemi baqinsa[1] da lalata, sai Muka shafe idanuwansu, (Muka ce da su): “Sai ku xanxani azabata da gargaxina.
1- Su ne mala’iku da suka zo masa a siffar mutane matasa kyawawa.
وَلَقَدۡ صَبَّحَهُم بُكۡرَةً عَذَابٞ مُّسۡتَقِرّٞ
Haqiqa kuma azaba matabbaciya ta yi musu sammako da asuba.
فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ
Saboda haka ku xanxani azabata da gargaxina.”
وَلَقَدۡ جَآءَ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ ٱلنُّذُرُ
Kuma haqiqa gargaxi ya zo wa mutanen Fir’auna
كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذۡنَٰهُمۡ أَخۡذَ عَزِيزٖ مُّقۡتَدِرٍ
Suka qaryata ayoyinmu dukkaninsu, sai Muka kama su irin kamu na Mabuwayi, Mai iko
أَكُفَّارُكُمۡ خَيۡرٞ مِّنۡ أُوْلَـٰٓئِكُمۡ أَمۡ لَكُم بَرَآءَةٞ فِي ٱلزُّبُرِ
Yanzu kafiranku (ku mutanen Makka) su ne suka fi waxancan alheri, ko kuwa kuna da wata hanya ta kuvuta ne a cikin littattafan da aka saukar?
أَمۡ يَقُولُونَ نَحۡنُ جَمِيعٞ مُّنتَصِرٞ
A’a, suna dai cewa ne: “Mu jama’a ce wadda za ta ci nasara.”
سَيُهۡزَمُ ٱلۡجَمۡعُ وَيُوَلُّونَ ٱلدُّبُرَ
To ba da daxewa ba za a karya jama’ar tasu[1], su kuma su ba da baya
1- Haka kuwa ya faru a yaqin Badar lokacin da aka karya lagon kafiran Makka, aka kashe manyansu da dama.
بَلِ ٱلسَّاعَةُ مَوۡعِدُهُمۡ وَٱلسَّاعَةُ أَدۡهَىٰ وَأَمَرُّ
A’a, alqiyama ita ce lokacin yi musu azaba, alqiyama kuwa ita ta fi bala’i, ta kuma fi xaci
إِنَّ ٱلۡمُجۡرِمِينَ فِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٖ
Lalle masu manyan laifuka suna cikin vata da azabar wuta
يَوۡمَ يُسۡحَبُونَ فِي ٱلنَّارِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ ذُوقُواْ مَسَّ سَقَرَ
Ranar da za a ja su cikin wuta a kan fuskokinsu (a ce da su): “Ku xanxani azabar wutar Saqara.”
إِنَّا كُلَّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَٰهُ بِقَدَرٖ
Lalle Mu, kowane abu Mun halitta shi da qaddara
وَمَآ أَمۡرُنَآ إِلَّا وَٰحِدَةٞ كَلَمۡحِۭ بِٱلۡبَصَرِ
Kuma al’amarinmu bai zamanto ba face kalma xaya kamar qiftawar ido
وَلَقَدۡ أَهۡلَكۡنَآ أَشۡيَاعَكُمۡ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Haqiqa kuma Mun hallakar da ire-irenku[1], to ko akwai mai wa’azantuwa?
1- Watau kafirai irinsu masu taurin kai.
وَكُلُّ شَيۡءٖ فَعَلُوهُ فِي ٱلزُّبُرِ
Kuma kowane abu da suka aikata yana cikin littattafai
وَكُلُّ صَغِيرٖ وَكَبِيرٖ مُّسۡتَطَرٌ
Kowane qaramin abu da babba kuma suna nan a rubuce
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَنَهَرٖ
Lalle masu taqawa suna cikin gidajen Aljanna da qoramu
فِي مَقۡعَدِ صِدۡقٍ عِندَ مَلِيكٖ مُّقۡتَدِرِۭ
A mazauni na gaskiya a wurin Mai mulki, Mai iko