Sourate: Suratul Ahqaf 

Verset : 31

يَٰقَوۡمَنَآ أَجِيبُواْ دَاعِيَ ٱللَّهِ وَءَامِنُواْ بِهِۦ يَغۡفِرۡ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمۡ وَيُجِرۡكُم مِّنۡ عَذَابٍ أَلِيمٖ

“Ya ku mutanenmu, ku amsa wa mai kira (zuwa ga) Allah[1], kuma ku yi imani da shi, (Allah) zai gafarta muku zunubanku ya kuma tsare ku daga azaba mai raxaxi


1- Watau Annabi Muhammad ().


Sourate: Suratul Ahqaf 

Verset : 32

وَمَن لَّا يُجِبۡ دَاعِيَ ٱللَّهِ فَلَيۡسَ بِمُعۡجِزٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَيۡسَ لَهُۥ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءُۚ أُوْلَـٰٓئِكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

“Duk wanda kuwa bai amsa wa mai kira (zuwa ga) Allah ba, to ba zai gagara ba a bayan qasa, kuma ba shi da wasu mataimaka in ba shi ba. Waxannan suna cikin vata mabayyani



Sourate: Suratul Ahqaf 

Verset : 33

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَلَمۡ يَعۡيَ بِخَلۡقِهِنَّ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰۚ بَلَىٰٓۚ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Ba sa ganin cewa Allah wanda Ya halicci sammai da qasa, Bai kuma gajiya ba wajen halittar su, Mai iko ne kan Ya raya matattu? Haka ne, lalle Shi Mai iko ne a kan komai



Sourate: Suratul Ahqaf 

Verset : 34

وَيَوۡمَ يُعۡرَضُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَلَى ٱلنَّارِ أَلَيۡسَ هَٰذَا بِٱلۡحَقِّۖ قَالُواْ بَلَىٰ وَرَبِّنَاۚ قَالَ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ

Kuma a ranar da za a bijiro da waxanda suka kafirta a gaban wuta (a ce da su): “Yanzu wannan ba gaskiya ba ne?” Suka ce: “Haka ne (gaskiya ne) Mun rantse da Ubangijinmu.” Sai Ya ce: “To ku xanxani azaba saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci.”



Sourate: Suratul Ahqaf 

Verset : 35

فَٱصۡبِرۡ كَمَا صَبَرَ أُوْلُواْ ٱلۡعَزۡمِ مِنَ ٱلرُّسُلِ وَلَا تَسۡتَعۡجِل لَّهُمۡۚ كَأَنَّهُمۡ يَوۡمَ يَرَوۡنَ مَا يُوعَدُونَ لَمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا سَاعَةٗ مِّن نَّهَارِۭۚ بَلَٰغٞۚ فَهَلۡ يُهۡلَكُ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

To ka yi haquri kamar yadda masu azama daga manzanni suka yi haquri, kada kuma ka nemi gaggauto musu (azaba). Kai ka ce ranar da za su ga abin da ake yi musu alqawarinsa kamar ba su zauna (a duniya) ba sai wani xan lokaci na wuni. (Wannan) isar da saqo ne. To akwai waxanda za a halakar in ba mutane fasiqai ba?