Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 31

ثُمَّ إِنَّكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عِندَ رَبِّكُمۡ تَخۡتَصِمُونَ

Sannan kuma lalle ku xin nan a ranar alqiyama a wurin Ubangijinku za ku yi husuma



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 32

۞فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَذَبَ عَلَى ٱللَّهِ وَكَذَّبَ بِٱلصِّدۡقِ إِذۡ جَآءَهُۥٓۚ أَلَيۡسَ فِي جَهَنَّمَ مَثۡوٗى لِّلۡكَٰفِرِينَ

Wane ne ya fi zalunci fiye da wanda ya yi wa Allah qarya, ya kuma qaryata gaskiya lokacin da ta zo masa? Yanzu a cikin wutar Jahannama babu wurin zaman kafirai?



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 33

وَٱلَّذِي جَآءَ بِٱلصِّدۡقِ وَصَدَّقَ بِهِۦٓ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُتَّقُونَ

Wanda kuwa ya zo da gaskiya ya kuma gaskata ta, waxannan su ne masu taqawa



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 34

لَهُم مَّا يَشَآءُونَ عِندَ رَبِّهِمۡۚ ذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Suna da (sakamakon) abin da suke so daga wurin Ubangijinsu. Wannan shi ne sakamakon masu kyautatawa



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 35

لِيُكَفِّرَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ أَسۡوَأَ ٱلَّذِي عَمِلُواْ وَيَجۡزِيَهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ ٱلَّذِي كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Don Allah Ya kankare musu mafi munin abin da suka aikata, Ya kuma saka musu ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 36

أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِكَافٍ عَبۡدَهُۥۖ وَيُخَوِّفُونَكَ بِٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦۚ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٖ

Yanzu Allah bai ishi bawansa ba? Suna kuma tsorata ka da waxanda suke ba Shi ba. Wanda kuwa Allah Ya vatar to babu wani mai shiryar da shi



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 37

وَمَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن مُّضِلٍّۗ أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِعَزِيزٖ ذِي ٱنتِقَامٖ

Wanda kuma Allah Ya shiryar da shi to babu wani mai vatar da shi. Yanzu Allah ba Mabuwayi ba ne, Mai ramuwar gayya?



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 38

وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۚ قُلۡ أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ إِنۡ أَرَادَنِيَ ٱللَّهُ بِضُرٍّ هَلۡ هُنَّ كَٰشِفَٰتُ ضُرِّهِۦٓ أَوۡ أَرَادَنِي بِرَحۡمَةٍ هَلۡ هُنَّ مُمۡسِكَٰتُ رَحۡمَتِهِۦۚ قُلۡ حَسۡبِيَ ٱللَّهُۖ عَلَيۡهِ يَتَوَكَّلُ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ

Tabbas da za ka tambaye su wanda ya halicci sammai da qasa, lalle za su ce: “Allah ne.” Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, idan Allah Ya nufe ni da wata cuta, yanzu za su iya yaye cutar tasa, ko kuwa idan Ya nufe ni da rahama yanzu za su iya riqe rahamarsa?” Ka ce: “Allah Ya ishe ni; a gare Shi ne kawai masu dogaro suke dogaro.”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 39

قُلۡ يَٰقَوۡمِ ٱعۡمَلُواْ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمۡ إِنِّي عَٰمِلٞۖ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

Ka ce: “Ya ku mutanena, ku yi aiki a kan irin hanyarku, ni ma kuma zan yi aiki ne (a kan irin tawa), sannu ba da daxewa ba za ku sani



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 40

مَن يَأۡتِيهِ عَذَابٞ يُخۡزِيهِ وَيَحِلُّ عَلَيۡهِ عَذَابٞ مُّقِيمٌ

“Wanda azabar da za ta kunyata shi za ta zo masa, kuma azaba madawwamiya za ta sauka a kansa.”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 41

إِنَّآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ لِلنَّاسِ بِٱلۡحَقِّۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِوَكِيلٍ

Lalle Mu Mun saukar maka da Littafi da gaskiya ga mutane; saboda haka duk wanda ya shiriya to ya yi wa kansa alheri, wanda kuwa ya vata, to lalle ya vata ne don kansa; kuma kai ba wakili ba ne a kansu



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 42

ٱللَّهُ يَتَوَفَّى ٱلۡأَنفُسَ حِينَ مَوۡتِهَا وَٱلَّتِي لَمۡ تَمُتۡ فِي مَنَامِهَاۖ فَيُمۡسِكُ ٱلَّتِي قَضَىٰ عَلَيۡهَا ٱلۡمَوۡتَ وَيُرۡسِلُ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمًّىۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

Allah Yana karvar rayuka lokacin mutuwarsu, da waxanda kuma ba su mutu ba a lokacin baccinsu; sai Ya riqe waxanda Ya qaddara wa mutuwa, Ya kuma saki sauran har zuwa wani lokaci qayyadadde. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu tunani



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 43

أَمِ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ شُفَعَآءَۚ قُلۡ أَوَلَوۡ كَانُواْ لَا يَمۡلِكُونَ شَيۡـٔٗا وَلَا يَعۡقِلُونَ

Tabbas sun dai riqi wasu masu ceto ne ba Allah ba. Ka ce: “Yanzu (kwa yi haka) ko da kuwa sun kasance ba sa mallakin komai, kuma ba sa hankalta?”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 44

قُل لِّلَّهِ ٱلشَّفَٰعَةُ جَمِيعٗاۖ لَّهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Ka ce: “Ceto gaba xaya na Allah ne; mulkin sammai da qasa nasa ne Shi kaxai; sannan kuma wurinsa ne kawai za a komar da ku.”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 45

وَإِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَحۡدَهُ ٱشۡمَأَزَّتۡ قُلُوبُ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِۖ وَإِذَا ذُكِرَ ٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦٓ إِذَا هُمۡ يَسۡتَبۡشِرُونَ

Idan kuma aka ambaci Allah Shi kaxai sai zukatan waxanda ba sa ba da gaskiya da ranar lahira su takura; idan kuwa aka ambaci waxanda suke ba Shi ba sai ka gan su suna ta walwala



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 46

قُلِ ٱللَّهُمَّ فَاطِرَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ عَٰلِمَ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ أَنتَ تَحۡكُمُ بَيۡنَ عِبَادِكَ فِي مَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Ka ce: “Ya Allah Mahaliccin sammai da qasa, Masanin voye da sarari, Kai ne za Ka yi hukunci tsakanin bayinka game da abin da suka kasance suna yin savani a kansa.”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 47

وَلَوۡ أَنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفۡتَدَوۡاْ بِهِۦ مِن سُوٓءِ ٱلۡعَذَابِ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَبَدَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مَا لَمۡ يَكُونُواْ يَحۡتَسِبُونَ

Da a ce waxanda suka yi zalunci za su mallaki abin da yake bayan qasa baki xaya har da wani kamarsa a tare da shi, to da sun fanshi kansu da shi saboda munin azabar ranar lahira. Abin da kuma ba su kasance suna tsammani daga Allah ba ya bayyana a gare su



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 48

وَبَدَا لَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُواْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Kuma munanan abubuwan da suka aikata suka bayyana a gare su, abin kuma da suka kasance suna yi wa izgili ya auka musu



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 49

فَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَانَا ثُمَّ إِذَا خَوَّلۡنَٰهُ نِعۡمَةٗ مِّنَّا قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمِۭۚ بَلۡ هِيَ فِتۡنَةٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

To idan wata cuta ta samu mutum sai ya roqe Mu, sannan idan Mun ba shi wata ni’ima daga gare Mu sai ya ce: “Ai an ba ni ita ne kawai don sanin (cancantata)”. Ba haka ba ne, ita wata jarrabawa ce kawai, sai dai yawancinsu ba sa sanin (haka)



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 50

قَدۡ قَالَهَا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Haqiqa waxanda suke gabaninsu sun faxe ita (wannan maganar), to abin da suka kasance suna aikatawa bai wadatar da su (komai) ba



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 51

فَأَصَابَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُواْۚ وَٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡ هَـٰٓؤُلَآءِ سَيُصِيبُهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُواْ وَمَا هُم بِمُعۡجِزِينَ

Saboda haka sai (sakamakon) mummunan abin da suka aikata ya same su. Waxanda ma suka yi zalunci daga waxannan[1], (sakamakon) munanan abubuwan da suka aikata zai same su, kuma ba za su gagara ba


1- Su ne masu aikata shirka da savon Allah cikin al’ummar Annabi ().


Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 52

أَوَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu ba su sani ba ne cewa, Allah Yana shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Yana kuma quntata wa (ga wanda ya ga dama)? Lalle a game da waxannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu yin imani



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 53

۞قُلۡ يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ أَسۡرَفُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُواْ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Ka ce[1]: “Ya ku bayina waxanda suka vata kawunansu sosai (da kafirci da savon Allah), kada ku xebe qauna daga rahamar Allah. Lalle Allah Yana gafarta zunubai baki xaya[2]. Lalle Shi Mai gafara ne, Mai rahama


1- Allah ne yake umartar Manzonsa () da ya faxa wa muminai bayin Allah.


2- Watau ga wanda ya tuba.


Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 54

وَأَنِيبُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ وَأَسۡلِمُواْ لَهُۥ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلۡعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ

“Ku kuma koma zuwa ga Ubangijinku, ku kuma miqa wuya gare Shi tun gabanin azaba ta zo muku sannan ba za a taimake ku ba



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 55

وَٱتَّبِعُوٓاْ أَحۡسَنَ مَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلۡعَذَابُ بَغۡتَةٗ وَأَنتُمۡ لَا تَشۡعُرُونَ

“Kuma ku bi mafi kyan abin da aka saukar muku daga Ubangijinku tun gabanin azaba ta zo muku ba zato ba tsammani, alhali ku ba ku sani ba



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 56

أَن تَقُولَ نَفۡسٞ يَٰحَسۡرَتَىٰ عَلَىٰ مَا فَرَّطتُ فِي جَنۢبِ ٱللَّهِ وَإِن كُنتُ لَمِنَ ٱلسَّـٰخِرِينَ

“Don kada wani rai ya ce: ‘Kaicona game da abin da na yi sakaci na haqqin Allah, ni tabbas na kasance daga masu yin izgili.’



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 57

أَوۡ تَقُولَ لَوۡ أَنَّ ٱللَّهَ هَدَىٰنِي لَكُنتُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِينَ

“Ko kuma ya ce: ‘Da Allah Ya shirye ni da tabbas na kasance daga masu taqawa.’



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 58

أَوۡ تَقُولَ حِينَ تَرَى ٱلۡعَذَابَ لَوۡ أَنَّ لِي كَرَّةٗ فَأَكُونَ مِنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

“Ko kuma ya ce lokacin da ya ga azaba: ‘Ina ma da ina da damar komawa duniya, don in kasance daga masu kyautatawa?’”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 59

بَلَىٰ قَدۡ جَآءَتۡكَ ءَايَٰتِي فَكَذَّبۡتَ بِهَا وَٱسۡتَكۡبَرۡتَ وَكُنتَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

(Sai a ce da shi): “A’a, haqiqa ayoyina sun zo maka sai ka qaryata su ka kuma yi girman kai ka kasance daga kafirai.”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 60

وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ تَرَى ٱلَّذِينَ كَذَبُواْ عَلَى ٱللَّهِ وُجُوهُهُم مُّسۡوَدَّةٌۚ أَلَيۡسَ فِي جَهَنَّمَ مَثۡوٗى لِّلۡمُتَكَبِّرِينَ

A ranar alqiyama kuwa za ka ga waxanda suka yi wa Allah qarya fuskokinsu baqi qirin. Yanzu a cikin wutar Jahannama ashe babu mazaunar masu girman kai?