ٱشۡدُدۡ بِهِۦٓ أَزۡرِي
“Ka qarfafa gwiwata da shi
وَأَشۡرِكۡهُ فِيٓ أَمۡرِي
“Kuma Ka shigar da shi cikin lamarina[1]
1- Watau shi ma ya ba shi annabta ya aiko su tare.
كَيۡ نُسَبِّحَكَ كَثِيرٗا
“Domin mu tsarkake Ka da yawa
وَنَذۡكُرَكَ كَثِيرًا
“Mu kuma ambace Ka da yawa
إِنَّكَ كُنتَ بِنَا بَصِيرٗا
“Lalle Kai Ka kasance Kana ganin mu.”
قَالَ قَدۡ أُوتِيتَ سُؤۡلَكَ يَٰمُوسَىٰ
(Allah) Ya ce: “Haqiqa an ba ka abin da ka tambaya, ya Musa
وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَيۡكَ مَرَّةً أُخۡرَىٰٓ
“Haqiqa kuma Mun yi ni’ima a gare ka a wani lokaci
إِذۡ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ أُمِّكَ مَا يُوحَىٰٓ
“Sanda Muka yiwo wahayi ga mahaifiyarka da abin da ake yin wahayi da shi
أَنِ ٱقۡذِفِيهِ فِي ٱلتَّابُوتِ فَٱقۡذِفِيهِ فِي ٱلۡيَمِّ فَلۡيُلۡقِهِ ٱلۡيَمُّ بِٱلسَّاحِلِ يَأۡخُذۡهُ عَدُوّٞ لِّي وَعَدُوّٞ لَّهُۥۚ وَأَلۡقَيۡتُ عَلَيۡكَ مَحَبَّةٗ مِّنِّي وَلِتُصۡنَعَ عَلَىٰ عَيۡنِيٓ
“Cewa, ‘ki saka shi (jinjirin) a cikin akwatu, sannan ki jefa shi cikin kogi, to sai kogin ya jefa shi a gava, sai maqiyina kuma maqiyinsa ya xauke shi.’ Na kuma sanya maka farin jini daga gare Ni, don kuma a yi tarbiyar ka a gaban idona
إِذۡ تَمۡشِيٓ أُخۡتُكَ فَتَقُولُ هَلۡ أَدُلُّكُمۡ عَلَىٰ مَن يَكۡفُلُهُۥۖ فَرَجَعۡنَٰكَ إِلَىٰٓ أُمِّكَ كَيۡ تَقَرَّ عَيۡنُهَا وَلَا تَحۡزَنَۚ وَقَتَلۡتَ نَفۡسٗا فَنَجَّيۡنَٰكَ مِنَ ٱلۡغَمِّ وَفَتَنَّـٰكَ فُتُونٗاۚ فَلَبِثۡتَ سِنِينَ فِيٓ أَهۡلِ مَدۡيَنَ ثُمَّ جِئۡتَ عَلَىٰ قَدَرٖ يَٰمُوسَىٰ
“Lokacin da ‘yar’uwarka take tafiya tana cewa (da su): ‘Yanzu ba na haxa ku da wadda za ta raine shi ba?’ Sai Muka komo da kai zuwa ga mahaifiyarka don zuciyarta ta yi sanyi, kada kuma ta yi baqin ciki. Kuma ka kashe wani mutum[1] sannan Muka tserar da kai daga uquba, Muka kuma jarrabe ka da jarrabobi daban-daban. Sannan ka zauna shekaru a cikin mutanen Madyana, sannan ka zo (nan) daidai lokacin da Na qadarta (maka annabta) ya Musa
1- Shi ne Baqibxen da Annabi Musa ya naushe shi ya faxi nan take ya mutu.
وَٱصۡطَنَعۡتُكَ لِنَفۡسِي
“Kuma Na zave ka don kaina[1]
1- Watau Allah () ya zave shi domin ya yi magana da shi, ya aika shi zuwa Fir’auna da mutanensa.
ٱذۡهَبۡ أَنتَ وَأَخُوكَ بِـَٔايَٰتِي وَلَا تَنِيَا فِي ذِكۡرِي
“Ka tafi kai da xan’uwanka da ayoyina, kada kuwa ku sassauta game da ambatona
ٱذۡهَبَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
“Ku tafi wurin Fir’auna, don ko lalle ya wuce iyaka
فَقُولَا لَهُۥ قَوۡلٗا لَّيِّنٗا لَّعَلَّهُۥ يَتَذَكَّرُ أَوۡ يَخۡشَىٰ
“Sai ku gaya masa magana mai taushi, ko wataqila zai wa’azantu ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah).”
قَالَا رَبَّنَآ إِنَّنَا نَخَافُ أَن يَفۡرُطَ عَلَيۡنَآ أَوۡ أَن يَطۡغَىٰ
(Musa da Haruna) suka ce: “Ya Ubangijinmu, lalle mu muna tsoron ya far mana ko kuma ya wuce iyaka (wajen yi mana uquba).”
قَالَ لَا تَخَافَآۖ إِنَّنِي مَعَكُمَآ أَسۡمَعُ وَأَرَىٰ
Ya ce: “Kada ku ji tsoro; haqiqa Ni ina tare da ku, ina ji kuma ina ganin (komai)
فَأۡتِيَاهُ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولَا رَبِّكَ فَأَرۡسِلۡ مَعَنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَلَا تُعَذِّبۡهُمۡۖ قَدۡ جِئۡنَٰكَ بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكَۖ وَٱلسَّلَٰمُ عَلَىٰ مَنِ ٱتَّبَعَ ٱلۡهُدَىٰٓ
“Sai ku tafi wajensa sannan ku ce (da shi): “Lalle mu manzannin Ubangijinka ne, sai ka sakar mana Banu-Isra’ila, kada kuma ka azabtar da su; haqiqa mun zo maka da aya daga Ubangijinka; aminci kuwa ya tabbata ga wanda ya bi shiriya
إِنَّا قَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡنَآ أَنَّ ٱلۡعَذَابَ عَلَىٰ مَن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
“Lalle mu an yi mana wahayi cewa, ita azaba lalle tana nan ga wanda ya qaryata ya kuma ba da baya.”
قَالَ فَمَن رَّبُّكُمَا يَٰمُوسَىٰ
(Fir’auna) ya ce: “Wane ne Ubangijin naku ya Musa?”
قَالَ رَبُّنَا ٱلَّذِيٓ أَعۡطَىٰ كُلَّ شَيۡءٍ خَلۡقَهُۥ ثُمَّ هَدَىٰ
(Musa) ya ce: “Ubangijinmu (Shi ne) Wanda Ya bai wa kowane abu surar halittarsa sannan Ya shiryar (da shi yadda zai yi tasarrufi).”
قَالَ فَمَا بَالُ ٱلۡقُرُونِ ٱلۡأُولَىٰ
(Fir’auna) ya ce: “To mene ne halin da al’ummun farko suke ciki?”
قَالَ عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّي فِي كِتَٰبٖۖ لَّا يَضِلُّ رَبِّي وَلَا يَنسَى
(Musa) ya ce: “Saninsu yana wurin Ubangijina a cikin Lauhul-Mahafuzu; Ubangijina kuma ba Ya kuskure (cikin iliminsa) kuma ba Ya mantuwa
ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مَهۡدٗا وَسَلَكَ لَكُمۡ فِيهَا سُبُلٗا وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّن نَّبَاتٖ شَتَّىٰ
“(Shi ne) Wanda Ya sanya muku qasa a shimfixe, Ya kuma sanya muku hanyoyi na tafiya cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama”, sannan Muka fitar da dangogin shuke-shuke iri-iri da shi (ruwa)
كُلُواْ وَٱرۡعَوۡاْ أَنۡعَٰمَكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلنُّهَىٰ
Ku ci (daga tsirran) kuma ku yi kiwon dabbobinku. Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga ma’abota hankula
۞مِنۡهَا خَلَقۡنَٰكُمۡ وَفِيهَا نُعِيدُكُمۡ وَمِنۡهَا نُخۡرِجُكُمۡ تَارَةً أُخۡرَىٰ
Daga ita (qasar) Muka halicce ku, kuma a cikinta za Mu mayar da ku, daga ita kuma za Mu fito da ku a wani karon
وَلَقَدۡ أَرَيۡنَٰهُ ءَايَٰتِنَا كُلَّهَا فَكَذَّبَ وَأَبَىٰ
Kuma haqiqa Mun nuna masa (Fir’auna) ayoyinmu dukkansu, sai ya qaryata kuma ya qi (ba da gaskiya)
قَالَ أَجِئۡتَنَا لِتُخۡرِجَنَا مِنۡ أَرۡضِنَا بِسِحۡرِكَ يَٰمُوسَىٰ
(Fir’auna) ya ce: “Yanzu ka zo mana ne don ka fitar da mu daga qasarmu da sihirinka, ya Musa?
فَلَنَأۡتِيَنَّكَ بِسِحۡرٖ مِّثۡلِهِۦ فَٱجۡعَلۡ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكَ مَوۡعِدٗا لَّا نُخۡلِفُهُۥ نَحۡنُ وَلَآ أَنتَ مَكَانٗا سُوٗى
“To lalle kuwa za mu zo maka da wani sihirin irinsa; sai ka sanya lokaci na musamman tsakaninmu da kai wanda mu ba za mu sava masa ba, kai ma haka, (ya zama) wuri ne tsaka-tsaki”
قَالَ مَوۡعِدُكُمۡ يَوۡمُ ٱلزِّينَةِ وَأَن يُحۡشَرَ ٱلنَّاسُ ضُحٗى
(Musa) ya ce: “Lokacin (da na sanya) muku shi ne ranar idi, kuma a tattara mutane da hantsi.”
فَتَوَلَّىٰ فِرۡعَوۡنُ فَجَمَعَ كَيۡدَهُۥ ثُمَّ أَتَىٰ
Sai Fir’auna ya juya, sai ya haxa makircinsa, sannan ya zo (wurin da aka shirya)