Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 31

أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَيَلۡبَسُونَ ثِيَابًا خُضۡرٗا مِّن سُندُسٖ وَإِسۡتَبۡرَقٖ مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِۚ نِعۡمَ ٱلثَّوَابُ وَحَسُنَتۡ مُرۡتَفَقٗا

Waxannan suna da gidajen Aljanna na dawwama waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, ana yi musu ado a cikinsu (watau gidajen) da awarwaro na zinare, suna kuma sanya tufafi koraye na alharini mai shara-shara da mai kauri, suna kwance a kan gadaje. Madalla (da wannan) lada, wurin hutu kuma ya kyautata



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 32

۞وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلٗا رَّجُلَيۡنِ جَعَلۡنَا لِأَحَدِهِمَا جَنَّتَيۡنِ مِنۡ أَعۡنَٰبٖ وَحَفَفۡنَٰهُمَا بِنَخۡلٖ وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُمَا زَرۡعٗا

Ka kuma ba su misali da wasu mutane su biyu da Muka tanadar wa xayansu gonakai biyu na inabi, Muka kuma kewaye su da dabinai, Muka kuma sanya wasu shukoki tsakaninsu



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 33

كِلۡتَا ٱلۡجَنَّتَيۡنِ ءَاتَتۡ أُكُلَهَا وَلَمۡ تَظۡلِم مِّنۡهُ شَيۡـٔٗاۚ وَفَجَّرۡنَا خِلَٰلَهُمَا نَهَرٗا

Kowace xaya daga gonakin ta ba da ‘ya’yanta kuma ba ta rage komai daga gare su ba. Muka kuma vuvvugo da qorama ta tsakiyarsu



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 34

وَكَانَ لَهُۥ ثَمَرٞ فَقَالَ لِصَٰحِبِهِۦ وَهُوَ يُحَاوِرُهُۥٓ أَنَا۠ أَكۡثَرُ مِنكَ مَالٗا وَأَعَزُّ نَفَرٗا

Ya zamanto yana da ‘ya’yan itace, sai ya ce da abokinsa yayin da yake mahawara da shi: “Ni na fi ka yawan dukiya da qarfin jama’a.”



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 35

وَدَخَلَ جَنَّتَهُۥ وَهُوَ ظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ قَالَ مَآ أَظُنُّ أَن تَبِيدَ هَٰذِهِۦٓ أَبَدٗا

Ya kuma shiga gonarsa yana kuwa mai zaluntar kansa[1], ya ce: “Ba na tsammanin cewa wannan za ta qare har abada.”


1- Yana alfahari da rashin nuna godiya ga Allah.


Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 36

وَمَآ أَظُنُّ ٱلسَّاعَةَ قَآئِمَةٗ وَلَئِن رُّدِدتُّ إِلَىٰ رَبِّي لَأَجِدَنَّ خَيۡرٗا مِّنۡهَا مُنقَلَبٗا

“Kuma ba na tsammanin alqiyama za ta tashi, kuma ko da an mayar da ni wurin Ubangijina to lalle zan sami canji fiye ma da ita.”



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 37

قَالَ لَهُۥ صَاحِبُهُۥ وَهُوَ يُحَاوِرُهُۥٓ أَكَفَرۡتَ بِٱلَّذِي خَلَقَكَ مِن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ سَوَّىٰكَ رَجُلٗا

Abokinsa ya ce da shi yana mai mahawara da shi: “Yanzu ka kafirce wa Wanda Ya halicce ka daga qasa, sannan (kuma) daga maniyyi, sannan Ya daidaita ka (ka zama) mutum?



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 38

لَّـٰكِنَّا۠ هُوَ ٱللَّهُ رَبِّي وَلَآ أُشۡرِكُ بِرَبِّيٓ أَحَدٗا

“Sai dai ni kam Allah Shi ne Ubangijina, ba kuwa zan haxa wani da Ubangijina ba



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 39

وَلَوۡلَآ إِذۡ دَخَلۡتَ جَنَّتَكَ قُلۡتَ مَا شَآءَ ٱللَّهُ لَا قُوَّةَ إِلَّا بِٱللَّهِۚ إِن تَرَنِ أَنَا۠ أَقَلَّ مِنكَ مَالٗا وَوَلَدٗا

“Kuma mai ya hana ka lokacin da ka shiga gonarka ka ce: ‘Abin da Allah Ya ga dama (shi zai kasance). Babu wani qarfi kuma babu dabara sai da Allah.’ Idan kana gani na na fi ka qarancin dukiya da ‘ya’ya



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 40

فَعَسَىٰ رَبِّيٓ أَن يُؤۡتِيَنِ خَيۡرٗا مِّن جَنَّتِكَ وَيُرۡسِلَ عَلَيۡهَا حُسۡبَانٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فَتُصۡبِحَ صَعِيدٗا زَلَقًا

“To ina fatan Ubangijina Ya ba ni fiye da gonarka, Ya kuma aiko mata (gonarka) da wani bala’i daga sama, sannan ta wayi gari ta zama qeqasasshiyar qasa mai santsi



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 41

أَوۡ يُصۡبِحَ مَآؤُهَا غَوۡرٗا فَلَن تَسۡتَطِيعَ لَهُۥ طَلَبٗا

“Ko kuma ruwanta ya zama ya qafe qarqaf, ba ko za ka sami hanyar samo shi ba.”



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 42

وَأُحِيطَ بِثَمَرِهِۦ فَأَصۡبَحَ يُقَلِّبُ كَفَّيۡهِ عَلَىٰ مَآ أَنفَقَ فِيهَا وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُشۡرِكۡ بِرَبِّيٓ أَحَدٗا

Aka kuwa hallaka ‘ya’yan itacen nasa, sannan ya wayi gari yana tafa hannayensa kan irin abin da ya vatar a kanta, ita kuwa ga ta ta zubo a kan dirkokinta, yana kuma cewa: “Kaicona, ina ma ban haxa wani da Ubangijina ba!”



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 43

وَلَمۡ تَكُن لَّهُۥ فِئَةٞ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مُنتَصِرًا

Ba shi kuwa da wata qungiya da za ta taimake shi ban da Allah, kuma bai zamo mai taimaka wa (kansa) ba



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 44

هُنَالِكَ ٱلۡوَلَٰيَةُ لِلَّهِ ٱلۡحَقِّۚ هُوَ خَيۡرٞ ثَوَابٗا وَخَيۡرٌ عُقۡبٗا

A wannan lokacin ne (ya bayyana) cewa taimako na Allah ne Tabbataccen (Sarki). Shi ne Fiyayyen Mai ba da lada kuma Fiyayyen Mai kyautata qarshe



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 45

وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ فَأَصۡبَحَ هَشِيمٗا تَذۡرُوهُ ٱلرِّيَٰحُۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقۡتَدِرًا

Kuma ka ba su misalin rayuwar duniya (wadda take) kamar ruwa ne da Muka saukar da shi daga sama, sai tsirran qasa suka cakuxa da shi, sannan ya zama busasshe, iska tana xaixaita shi. Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan komai



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 46

ٱلۡمَالُ وَٱلۡبَنُونَ زِينَةُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَٱلۡبَٰقِيَٰتُ ٱلصَّـٰلِحَٰتُ خَيۡرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَابٗا وَخَيۡرٌ أَمَلٗا

Dukiya da ‘ya’ya adon rayuwar duniya ne; wanzazzun ayyuka nagari kuwa su suka fi lada a wurin Ubangijinka kuma su ne buri mafi alheri



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 47

وَيَوۡمَ نُسَيِّرُ ٱلۡجِبَالَ وَتَرَى ٱلۡأَرۡضَ بَارِزَةٗ وَحَشَرۡنَٰهُمۡ فَلَمۡ نُغَادِرۡ مِنۡهُمۡ أَحَدٗا

Kuma ka tuna ranar da za Mu tafiyar da duwatsu kuma ka ga qasa a baje (ba tudu ba rafi), Mu kuma tattara su (gaba xaya), ba Mu bar xaya daga cikinsu ba



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 48

وَعُرِضُواْ عَلَىٰ رَبِّكَ صَفّٗا لَّقَدۡ جِئۡتُمُونَا كَمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةِۭۚ بَلۡ زَعَمۡتُمۡ أَلَّن نَّجۡعَلَ لَكُم مَّوۡعِدٗا

Aka kuma kawo su a gaban Ubangijinka sahu-sahu (a ce da su): “Haqiqa kun zo mana kamar yadda tun farko Muka halicce ku. Ba ma haka ba, kun riya cewa ba za Mu sanya muku wani wa’adi ba.”



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 49

وَوُضِعَ ٱلۡكِتَٰبُ فَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُشۡفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَٰوَيۡلَتَنَا مَالِ هَٰذَا ٱلۡكِتَٰبِ لَا يُغَادِرُ صَغِيرَةٗ وَلَا كَبِيرَةً إِلَّآ أَحۡصَىٰهَاۚ وَوَجَدُواْ مَا عَمِلُواْ حَاضِرٗاۗ وَلَا يَظۡلِمُ رَبُّكَ أَحَدٗا

Aka kuma ajiye littafin (ayyukansu), sannan sai ka ga masu laifi suna cike da tsoron abin da yake cikinsa, suna kuma cewa: “Kaiconmu, me ya sami wannan littafin, ba ya barin (aiki) qarami balle babba sai ya qididdige su. Suka kuma sami (duk) abubuwan da suka aikata an zo da su. Ubangijinka kuwa ba zai zalunci kowa ba



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 50

وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ كَانَ مِنَ ٱلۡجِنِّ فَفَسَقَ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِۦٓۗ أَفَتَتَّخِذُونَهُۥ وَذُرِّيَّتَهُۥٓ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِي وَهُمۡ لَكُمۡ عَدُوُّۢۚ بِئۡسَ لِلظَّـٰلِمِينَ بَدَلٗا

Kuma ka tuna lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu”, sai suka yi sujjadar in ban da Iblis, ya kasance kuwa daga cikin aljannu, sai ya sava wa umarnin Ubangijinsa. Yanzu kwa riqe shi shi da zurriyarsa masoya ba Ni ba, alhali kuwa su maqiyanku ne? Wannan canji na azzalumai ya munana



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 51

۞مَّآ أَشۡهَدتُّهُمۡ خَلۡقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَا خَلۡقَ أَنفُسِهِمۡ وَمَا كُنتُ مُتَّخِذَ ٱلۡمُضِلِّينَ عَضُدٗا

Ban halarto da su ba lokacin halittar sammai da qasa, ko ma halittar kawunansu, ban kuma kasance Mai riqon masu vatarwa mataimaka ba



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 52

وَيَوۡمَ يَقُولُ نَادُواْ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُم مَّوۡبِقٗا

Kuma (ka tuna) ranar da (Allah) zai ce (da kafirai): “Ku kirawo abokan tarayyar nawa waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku)”, to sai suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, Muka kuma sanya mahallaka a tsakaninsu



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 53

وَرَءَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ ٱلنَّارَ فَظَنُّوٓاْ أَنَّهُم مُّوَاقِعُوهَا وَلَمۡ يَجِدُواْ عَنۡهَا مَصۡرِفٗا

Masu laifi kuma suka ga wuta sai suka tabbatar da cewa lalle za su shige ta ba kuwa za su sami wata makauta ba daga gare ta



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 54

وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لِلنَّاسِ مِن كُلِّ مَثَلٖۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ أَكۡثَرَ شَيۡءٖ جَدَلٗا

Kuma haqiqa Mun sassarafa kowane irin misali ga mutane a cikin wannan Alqur’anin. Mutum kuwa ya kasance wanda ya fi komai yawan musu



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 55

وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤۡمِنُوٓاْ إِذۡ جَآءَهُمُ ٱلۡهُدَىٰ وَيَسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّهُمۡ إِلَّآ أَن تَأۡتِيَهُمۡ سُنَّةُ ٱلۡأَوَّلِينَ أَوۡ يَأۡتِيَهُمُ ٱلۡعَذَابُ قُبُلٗا

Ba kuwa abin da ya hana mutane su yi imani lokacin da shiriya ta zo musu, su kuma nemi gafarar Ubangijinsu har sai irin abin da ya zo wa mutanen farko ya zo musu, ko kuwa azaba ta zo musu gaba-da-gaba



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 56

وَمَا نُرۡسِلُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَۚ وَيُجَٰدِلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ لِيُدۡحِضُواْ بِهِ ٱلۡحَقَّۖ وَٱتَّخَذُوٓاْ ءَايَٰتِي وَمَآ أُنذِرُواْ هُزُوٗا

Ba Mu kuma aiko da manzanni ba sai don su zama masu albishir mai gargaxi. Su kuma waxanda suka kafirce sai su dinga jayayya da qarya don su kawar da gaskiya da ita; suka kuma riqi ayoyina da kuma abin da aka yi musu gargaxi da shi a matsayin abin izgili



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 57

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦ فَأَعۡرَضَ عَنۡهَا وَنَسِيَ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُۚ إِنَّا جَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۖ وَإِن تَدۡعُهُمۡ إِلَى ٱلۡهُدَىٰ فَلَن يَهۡتَدُوٓاْ إِذًا أَبَدٗا

Wane ne ya fi zalunci fiye da wanda aka yi masa gargaxi da ayoyin Ubangijinsa sannan ya bijire musu, ya kuma manta abin da hannayensa suka gabatar (na mugun aiki). Lalle Mun sanya rufi a zukatansu don kada su fahimce shi (Alqur’ani), a cikin kunnuwansu kuma (Muka sanya) wani nauyi. Idan kuwa ka kirawo su zuwa ga shiriya to ba za su yi imani ba har abada



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 58

وَرَبُّكَ ٱلۡغَفُورُ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۖ لَوۡ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُواْ لَعَجَّلَ لَهُمُ ٱلۡعَذَابَۚ بَل لَّهُم مَّوۡعِدٞ لَّن يَجِدُواْ مِن دُونِهِۦ مَوۡئِلٗا

Ubangijinka kuwa Mai yawan gafara ne Ma’abocin rahama; da Yana kama su da abin da suka aikata, to da Ya gaggauta musu azaba. A’a, (ba Ya yin haka), sai dai suna da qayyadajjen lokaci wanda ba za su sami wata makauta ba daga gare shi



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 59

وَتِلۡكَ ٱلۡقُرَىٰٓ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡ لَمَّا ظَلَمُواْ وَجَعَلۡنَا لِمَهۡلِكِهِم مَّوۡعِدٗا

Kuma waxancan alqaryu Mun hallakar da su yayin da suka yi zalunci, Muka kuma sanya qayyadajjen lokaci na hallakar da su



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 60

وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِفَتَىٰهُ لَآ أَبۡرَحُ حَتَّىٰٓ أَبۡلُغَ مَجۡمَعَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ أَوۡ أَمۡضِيَ حُقُبٗا

Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da yaronsa: “Ba zan dakata da (tafiyata) ba har sai na kai mahaxar kogunan nan biyu, ko kuwa in zarce har tsawon shekaru[1].”


1- Daga nan har zuwa qarshen aya ta 82 Allah () ya ba da labarin tafiyar Annabi Musa () neman ilimi wajen Annabi Khadir (). Yaronsa shi ne Annabi Yusha’u ().