Sourate: Suratu Yunus

Verset : 31

قُلۡ مَن يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ أَمَّن يَمۡلِكُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَمَن يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَمَن يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَۚ فَسَيَقُولُونَ ٱللَّهُۚ فَقُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ

Ka ce: “Wane ne yake arzuta ku ta sama da qasa? Ko kuma wane ne mamallakin ji da gani? Kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wane ne kuma yake tsara al’amura?” To ai za su ce: “Allah ne.” To ka ce: “Yanzu ba za ku kiyaye dokokinsa ba?”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 32

فَذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمُ ٱلۡحَقُّۖ فَمَاذَا بَعۡدَ ٱلۡحَقِّ إِلَّا ٱلضَّلَٰلُۖ فَأَنَّىٰ تُصۡرَفُونَ

To wannan Shi ne Allah Ubangijinku na gaskiya. Bayan gaskiya kuwa babu wani abu sai vata. To yaya ake karkatar da ku?



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 33

كَذَٰلِكَ حَقَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى ٱلَّذِينَ فَسَقُوٓاْ أَنَّهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Kamar haka ne kalmar Ubangijinka ta tabbata a kan waxanda suka yi fasiqanci cewa su ba za su yi imani ba



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 34

قُلۡ هَلۡ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥۚ قُلِ ٱللَّهُ يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ

Ka ce: “Shin daga cikin abokan tarayyarku ko akwai wanda yake qaga halitta, sannan ya maimaita ta?” Ka ce: “Allah Shi ne Wanda Yake qaga halitta sannan Ya maimaita ta. To ta yaya ake kautar da ku?”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 35

قُلۡ هَلۡ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلۡحَقِّۚ قُلِ ٱللَّهُ يَهۡدِي لِلۡحَقِّۗ أَفَمَن يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلۡحَقِّ أَحَقُّ أَن يُتَّبَعَ أَمَّن لَّا يَهِدِّيٓ إِلَّآ أَن يُهۡدَىٰۖ فَمَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ

Ka ce: “Shin daga abokan tarayyarku ko akwai wanda yake shiryarwa zuwa gaskiya?” Ka ce: “Allah Shi ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. To yanzu wanda yake shiryarwa zuwa gaskiya shi ya fi cancanta a bi, ko kuwa wanda ba ya shiryarwa sai dai a shiryar da shi? To me ya same ku ne? Yaya kuke wannan hukuncin?



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 36

وَمَا يَتَّبِعُ أَكۡثَرُهُمۡ إِلَّا ظَنًّاۚ إِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغۡنِي مِنَ ٱلۡحَقِّ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا يَفۡعَلُونَ

Yawancinsu kuma ba abin da suke bi sai zato. Lalle zato ba ya wadatar da komai game da gaskiya. Lalle Allah Masanin abin da suke aikatawa ne



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 37

وَمَا كَانَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ أَن يُفۡتَرَىٰ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِن تَصۡدِيقَ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَتَفۡصِيلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا رَيۡبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Wannan Alqur’ani bai yiwuwa a qage shi daga (tunanin) wani wanda ba Allah ba, sai dai (shi) gaskatawa ne ga abin da ya gabace shi (na littattafan da aka saukar), kuma bayani ne dalla-dalla na hukunce-hukuncen (da Allah ya saukar); babu kokwanto a cikinsa cewa daga Ubangijin talikai yake



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 38

أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ فَأۡتُواْ بِسُورَةٖ مِّثۡلِهِۦ وَٱدۡعُواْ مَنِ ٱسۡتَطَعۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ko kuma cewa suke yi: “Qagar sa ya yi ne?” Ka ce: “To ku kawo sura (xaya tal) irinsa, kuma ku kirawo wanda duk za ku iya (ya taimaka muku) wanda ba Allah ba idan kun kasance masu gaskiya!”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 39

بَلۡ كَذَّبُواْ بِمَا لَمۡ يُحِيطُواْ بِعِلۡمِهِۦ وَلَمَّا يَأۡتِهِمۡ تَأۡوِيلُهُۥۚ كَذَٰلِكَ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلظَّـٰلِمِينَ

A’a, ba haka ba ne, sun dai qaryata abin da ba su da iliminsa ne, kuma har yanzu haqiqanin fassararsa ba ta zo musu ba. Kamar haka ne waxanda suka gabace su suka qaryata. To duba ka ga yadda qarshen azzalumai ya zama



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 40

وَمِنۡهُم مَّن يُؤۡمِنُ بِهِۦ وَمِنۡهُم مَّن لَّا يُؤۡمِنُ بِهِۦۚ وَرَبُّكَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُفۡسِدِينَ

Daga cikinsu kuma akwai wanda yake yin imani da shi (Alqur’ani), akwai kuma wanda ba ya yin imani da shi. Ubangijinka kuma Shi ne Mafi sanin mavarnata



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 41

وَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل لِّي عَمَلِي وَلَكُمۡ عَمَلُكُمۡۖ أَنتُم بَرِيٓـُٔونَ مِمَّآ أَعۡمَلُ وَأَنَا۠ بَرِيٓءٞ مِّمَّا تَعۡمَلُونَ

Idan kuwa suka qaryata ka, to ka ce: “Aikina nawa ne ku ma aikinku naku ne. Ku babu ruwanku da abin da nake aikatawa, ni ma kuma babu ruwana da abin da kuke aikatawa.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 42

وَمِنۡهُم مَّن يَسۡتَمِعُونَ إِلَيۡكَۚ أَفَأَنتَ تُسۡمِعُ ٱلصُّمَّ وَلَوۡ كَانُواْ لَا يَعۡقِلُونَ

Daga cikinsu akwai waxanda suke sauraron ka. Yanzu kai za ka iya jiyar da kurame ko da ba su da hankali?



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 43

وَمِنۡهُم مَّن يَنظُرُ إِلَيۡكَۚ أَفَأَنتَ تَهۡدِي ٱلۡعُمۡيَ وَلَوۡ كَانُواْ لَا يُبۡصِرُونَ

Daga cikinsu kuma akwai wanda yake qura maka ido. Yanzu kai za ka iya shiryar da makafi ko da ba sa gani?



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 44

إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَظۡلِمُ ٱلنَّاسَ شَيۡـٔٗا وَلَٰكِنَّ ٱلنَّاسَ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

Lalle Allah ba Ya zaluntar mutane da komai, sai dai mutane kawunansu kawai suke zalunta



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 45

وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ كَأَن لَّمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا سَاعَةٗ مِّنَ ٱلنَّهَارِ يَتَعَارَفُونَ بَيۡنَهُمۡۚ قَدۡ خَسِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِلِقَآءِ ٱللَّهِ وَمَا كَانُواْ مُهۡتَدِينَ

Ranar da zai tattara su kuwa (za su ga) kamar ba su zauna ba sai wani xan lokaci na rana da suke gane junansu (a cikinsa). Haqiqa waxanda suka qaryata gamuwa da Allah sun tave, ba su kuma zamanto shiryayyu ba



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 46

وَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيۡنَا مَرۡجِعُهُمۡ ثُمَّ ٱللَّهُ شَهِيدٌ عَلَىٰ مَا يَفۡعَلُونَ

Ko dai Mu nuna maka sashin abin da Muke musu alkawarinsa ko kuma Mu karvi ranka, to makomarsu dai gare Mu take, sannan Allah Yana sane da abin da suke aikatawa



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 47

وَلِكُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولٞۖ فَإِذَا جَآءَ رَسُولُهُمۡ قُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Kowacce al’umma kuma tana da manzo. To idan manzonsu ya zo (suka qaryata shi) to sai a yi hukunci a tsakaninsu da adalci, su kuma ba za a zalunce su ba



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 48

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Suna kuma cewa: “To yaushe ne wannan alqawari (zai zo) idan kun kasance masu gaskiya?”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 49

قُل لَّآ أَمۡلِكُ لِنَفۡسِي ضَرّٗا وَلَا نَفۡعًا إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۗ لِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌۚ إِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ فَلَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ

Ka ce: “Ba na mallakar wata cuta, ko wani amfani ga kaina sai dai abin da Allah Ya ga dama. Kowacce al’umma tana da lokacin (da aka iyakance mata). Idan lokacin nasu ya yi, to ba za su yi jinkiri na sa’a guda ba, kuma ba za su gaggauto ba.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 50

قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِنۡ أَتَىٰكُمۡ عَذَابُهُۥ بَيَٰتًا أَوۡ نَهَارٗا مَّاذَا يَسۡتَعۡجِلُ مِنۡهُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

Ka ce: “Yanzu ku ba ni labari (yadda za ku yi) idan azabar Allah ta zo muku da daddare ko da rana; mene ne masu laifi suke yi wa gaggawar zuwansa?



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 51

أَثُمَّ إِذَا مَا وَقَعَ ءَامَنتُم بِهِۦٓۚ ءَآلۡـَٰٔنَ وَقَدۡ كُنتُم بِهِۦ تَسۡتَعۡجِلُونَ

“Shin sai idan (azabar) ta afka (muku) ne za ku yi imani da Shi (Allah)? Sai yanzu ne, alhali kuwa da can kun kasance kuna neman gaggautowarta?”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 52

ثُمَّ قِيلَ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡخُلۡدِ هَلۡ تُجۡزَوۡنَ إِلَّا بِمَا كُنتُمۡ تَكۡسِبُونَ

Sannan aka ce da waxanda suka yi zalunci: “Ku xanxani azaba mai dawwama; shin za a saka muku (da wani abu ne) in ban da abin da kuka kasance kuna aikatawa?.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 53

۞وَيَسۡتَنۢبِـُٔونَكَ أَحَقٌّ هُوَۖ قُلۡ إِي وَرَبِّيٓ إِنَّهُۥ لَحَقّٞۖ وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ

Suna kuma tambayar ka cewa: “Yanzu (batun azabar nan) gaskiya ne kuwa?” Ka ce: “I mana, na ko ranste da Allah lalle shi gaskiya ne; ba kuma za ku kuvuce ba.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 54

وَلَوۡ أَنَّ لِكُلِّ نَفۡسٖ ظَلَمَتۡ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لَٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۖ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Da a ce kowane rai da ya yi zalunci ya mallaki duk abin da yake bayan qasa, to lalle da ya fanshi kansa da shi. Suka kuwa voye nadama a lokacin da suka ga azaba; an kuma yi hukunci tsakaninsu na adalci; ba kuma za a zalunce su ba



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 55

أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

A saurara, lalle duk abin da yake sammai da qasa na Allah ne. A saurara, lalle alqwarin Allah gaskiya ne, sai dai kuma yawancin mutane ba su sani ba



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 56

هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Shi ne Yake rayawa Yake kuma kashewa, kuma wurinsa za a mai da ku



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 57

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَتۡكُم مَّوۡعِظَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَشِفَآءٞ لِّمَا فِي ٱلصُّدُورِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ

Ya ku mutane, haqiqa gargaxi ya zo muku daga Ubangijinku da kuma waraka ga abin da yake cikin zukatanku, kuma shiriya ne da rahama ga muminai



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 58

قُلۡ بِفَضۡلِ ٱللَّهِ وَبِرَحۡمَتِهِۦ فَبِذَٰلِكَ فَلۡيَفۡرَحُواْ هُوَ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ

Ka ce: “Da falalar Allah da rahamarsa, sai su yi farin ciki da wannan; shi ya fi alheri daga abin da suke tarawa (na dukiya).”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 59

قُلۡ أَرَءَيۡتُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ لَكُم مِّن رِّزۡقٖ فَجَعَلۡتُم مِّنۡهُ حَرَامٗا وَحَلَٰلٗا قُلۡ ءَآللَّهُ أَذِنَ لَكُمۡۖ أَمۡ عَلَى ٱللَّهِ تَفۡتَرُونَ

Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin abin da Allah Ya saukar muku na arziki, sannan kuka mayar da wani haram wani kuma halal”. Ka ce: “Yanzu Allah ne Ya yi muku izinin (yin haka), ko kuwa Allah kuke yi wa qage ne?”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 60

وَمَا ظَنُّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَشۡكُرُونَ

Mene ne kuma tsammanin waxanda suke yi wa Allah qagen qarya a ranar alqiyama? Lalle Allah Ma’abocin falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa