Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 1

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

Saukar Littafi daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 2

إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ

Lalle Mu Muka saukar maka Littafi da gaskiya, to ka bauta wa Allah kana mai tsantsanta addini a gare Shi



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 3

أَلَا لِلَّهِ ٱلدِّينُ ٱلۡخَالِصُۚ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ

Ku saurara! Tsantsan addini na Allah ne[1]. Waxanda kuwa suka riqi wasu majivinta al’amari ba Shi ba (suna cewa): “Ba ma bauta musu sai kawai don su kusanta mu ga Allah.” Lalle Allah zai yi hukunci a tsakaninsu game da abin da suke sassavawa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake maqaryaci, mai yawan kafirci


1- Watau addinin kaxaita Allah da guje wa shirka.


Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 4

لَّوۡ أَرَادَ ٱللَّهُ أَن يَتَّخِذَ وَلَدٗا لَّٱصۡطَفَىٰ مِمَّا يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ سُبۡحَٰنَهُۥۖ هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّارُ

Da Allah Ya yi nufin Ya riqi xa, da sai Ya zavi wanda Ya ga dama daga abubuwan da Yake halitta. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shi ne Xaya, Mai rinjaye



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 5

خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۖ يُكَوِّرُ ٱلَّيۡلَ عَلَى ٱلنَّهَارِ وَيُكَوِّرُ ٱلنَّهَارَ عَلَى ٱلَّيۡلِۖ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِي لِأَجَلٖ مُّسَمًّىۗ أَلَا هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفَّـٰرُ

Ya halicci sammai da qasa da gaskiya; Yana naxa dare a kan yini, Ya kuma naxa yini a kan dare; kuma Ya hore rana da wata; kowane yana tafiya zuwa wani lokaci qayyadajje. Ku saurara! Shi ne Mabuwayi, Mai yawan gafara



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 6

خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ ثُمَّ جَعَلَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ ثَمَٰنِيَةَ أَزۡوَٰجٖۚ يَخۡلُقُكُمۡ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡ خَلۡقٗا مِّنۢ بَعۡدِ خَلۡقٖ فِي ظُلُمَٰتٖ ثَلَٰثٖۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ لَهُ ٱلۡمُلۡكُۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُصۡرَفُونَ

Ya halicce ku daga rai guda (shi ne Adamu), sannan Ya halicci matarsa daga gare shi, Ya kuma halitta muku dangogi guda takwas na dabbobin ni’ima. Yana (shirya) halittarku a cikin cikkunan iyayenku mata, matakin halitta bayan wani matakin, cikin duffai guda uku[1]. Wannan kuwa Shi ne Allah Ubangijinku; Wanda mulki nasa ne; babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi. To ta ina ne ake juyar da ku?


1- Watau duhun ciki da duhun mahaifa da kuma duhun mabiyiya.


Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 7

إِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنكُمۡۖ وَلَا يَرۡضَىٰ لِعِبَادِهِ ٱلۡكُفۡرَۖ وَإِن تَشۡكُرُواْ يَرۡضَهُ لَكُمۡۗ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرۡجِعُكُمۡ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Idan kun kafirce, to lalle Allah Mawadaci ne ga barin ku, ba Ya kuma yarda da kafirci daga bayinsa. Idan kuwa kuka gode Zai yarda da godiyar taku. Kuma wani rai ba ya xaukar laifin wani. Sannan zuwa ga Ubangijinku ne makomarku take, sannan Ya ba ku labarin irin abubuwan da kuka kasance kuna aikatawa. Lalle Shi Masanin abubuwan da suke cikin qiraza ne



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 8

۞وَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَا رَبَّهُۥ مُنِيبًا إِلَيۡهِ ثُمَّ إِذَا خَوَّلَهُۥ نِعۡمَةٗ مِّنۡهُ نَسِيَ مَا كَانَ يَدۡعُوٓاْ إِلَيۡهِ مِن قَبۡلُ وَجَعَلَ لِلَّهِ أَندَادٗا لِّيُضِلَّ عَن سَبِيلِهِۦۚ قُلۡ تَمَتَّعۡ بِكُفۡرِكَ قَلِيلًا إِنَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِ

Idan kuma wata cuta ta sami mutum sai ya roqi Ubangijinsa yana mai komawa gare Shi, sannan idan Ya ba shi wata ni’ima daga gare Shi, sai ya manta abin da ya kasance yana roqon Sa a da, ya kuma sanya abokan tarayya ga Allah don ya vatar (da mutane) daga hanyarsa (Allah). Ka ce: “Ka ji daxi xan kaxan da kafircinka; lalle kai kam kana daga cikin ‘yan wuta.”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 9

أَمَّنۡ هُوَ قَٰنِتٌ ءَانَآءَ ٱلَّيۡلِ سَاجِدٗا وَقَآئِمٗا يَحۡذَرُ ٱلۡأٓخِرَةَ وَيَرۡجُواْ رَحۡمَةَ رَبِّهِۦۗ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلَّذِينَ يَعۡلَمُونَ وَٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Shin yanzu wanda yake shi mai ibada ne a cikin sa’o’in dare, yana sujjada yana kuma tsayawa, yana tsoron ranar lahira yana kuma qaunar rahamar Ubangijinsa (zai yi daidai da wanda ba haka yake ba?) Ka ce: “Yanzu waxanda suke da sani za su yi daidai da waxanda ba su da sani? Ma’abota hankula ne kawai suke wa’azantuwa



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 10

قُلۡ يَٰعِبَادِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ لِلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٞۗ وَأَرۡضُ ٱللَّهِ وَٰسِعَةٌۗ إِنَّمَا يُوَفَّى ٱلصَّـٰبِرُونَ أَجۡرَهُم بِغَيۡرِ حِسَابٖ

Ka ce[1]: “Ya ku bayina waxanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Ubangijinku. Waxanda suka kyautata a wannan duniyar suna da kyakkyawan (sakamako). Qasar Allah kuma yalwatacciya ce. Lalle masu haquri ne kawai ake cika wa ladansu ba da lissafi ba.”


1- Allah () ya umarci Manzonsa () ya faxa wa bayinsa muminai a madadinsa.


Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 11

قُلۡ إِنِّيٓ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ

Ka ce: “Lalle ni an umarce ni da in bauta wa Allah ina mai tsantsanta addini gare Shi



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 12

وَأُمِرۡتُ لِأَنۡ أَكُونَ أَوَّلَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

“An kuma umarce ni da in kasance farkon Musulmi.”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 13

قُلۡ إِنِّيٓ أَخَافُ إِنۡ عَصَيۡتُ رَبِّي عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

Ka ce: “Lalle ni ina jin tsoron azabar wani yini mai girma idan na savi Ubangijina”



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 14

قُلِ ٱللَّهَ أَعۡبُدُ مُخۡلِصٗا لَّهُۥ دِينِي

Ka ce: “Allah kawai nake bauta wa, ina mai tsantsanta addinina gare Shi



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 15

فَٱعۡبُدُواْ مَا شِئۡتُم مِّن دُونِهِۦۗ قُلۡ إِنَّ ٱلۡخَٰسِرِينَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَأَهۡلِيهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ أَلَا ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡخُسۡرَانُ ٱلۡمُبِينُ

“Sai ku bauta wa abin da kuka ga dama ba Shi ba.” Ka ce: “Lalle asararru (su ne) waxanda suka yi asarar rayuwarsu da ta iyalinsu ranar alqiyama. Ku saurara! Wannan ita ce asara bayyananniya



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 16

لَهُم مِّن فَوۡقِهِمۡ ظُلَلٞ مِّنَ ٱلنَّارِ وَمِن تَحۡتِهِمۡ ظُلَلٞۚ ذَٰلِكَ يُخَوِّفُ ٱللَّهُ بِهِۦ عِبَادَهُۥۚ يَٰعِبَادِ فَٱتَّقُونِ

Suna da inuwoyi na wuta a samansu, a qarqashinsu kuma akwai wasu inuwoyin. Wannan ne fa Allah Yake tsoratar da bayinsa da shi. Ya ku bayina, sai ku kiyaye dokokina



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 17

وَٱلَّذِينَ ٱجۡتَنَبُواْ ٱلطَّـٰغُوتَ أَن يَعۡبُدُوهَا وَأَنَابُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ لَهُمُ ٱلۡبُشۡرَىٰۚ فَبَشِّرۡ عِبَادِ

Waxanda kuwa suka nisanci bautar xagutu[1], suka kuma koma ga Allah, suna da albishir (na Aljanna). To ka yi wa bayina aibishir


1- Xagutu, shi ne duk wani abu da bawa ya qetare iyakar Allah ta hanyansa.


Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 18

ٱلَّذِينَ يَسۡتَمِعُونَ ٱلۡقَوۡلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحۡسَنَهُۥٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ هَدَىٰهُمُ ٱللَّهُۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمۡ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Waxanda suke sauraron magana sai su bi mafi kyawunta, waxannan su ne waxanda Allah Ya shiriya, kuma waxannan su ne ma’abota hankula



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 19

أَفَمَنۡ حَقَّ عَلَيۡهِ كَلِمَةُ ٱلۡعَذَابِ أَفَأَنتَ تُنقِذُ مَن فِي ٱلنَّارِ

Yanzu wanda kalmar azaba ta tabbata a kansa (kai ne za ka iya shiyar da shi)? Yanzu kai za ka iya kuvutar da wanda yake cikin wuta?



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 20

لَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ رَبَّهُمۡ لَهُمۡ غُرَفٞ مِّن فَوۡقِهَا غُرَفٞ مَّبۡنِيَّةٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ لَا يُخۡلِفُ ٱللَّهُ ٱلۡمِيعَادَ

Sai dai waxanda suka kiyaye dokokin Ubangijinsu suna da xakunan benaye, a sama da su kuma akwai wasu xakunan benaye ginannu, qoramu suna gudana ta qarqashinsu; (wannan) alqawarin Allah ne; Allah ko ba Ya sava alqawari



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 21

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَسَلَكَهُۥ يَنَٰبِيعَ فِي ٱلۡأَرۡضِ ثُمَّ يُخۡرِجُ بِهِۦ زَرۡعٗا مُّخۡتَلِفًا أَلۡوَٰنُهُۥ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَىٰهُ مُصۡفَرّٗا ثُمَّ يَجۡعَلُهُۥ حُطَٰمًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَذِكۡرَىٰ لِأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Yanzu ba ka gani cewa Allah ne Ya saukar da ruwa daga sama, sannan Ya shigar da shi cikin idanuwan ruwa a qasa, sannan Yana fitar da shukoki masu launi iri-iri da shi, sannan ya bushe sai ka gan shi fatsi-fatsi, sannan Ya mayar da shi dudduga? Lalle a game da wannan tabbas akwai wa’azi ga ma’abota hankula



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 22

أَفَمَن شَرَحَ ٱللَّهُ صَدۡرَهُۥ لِلۡإِسۡلَٰمِ فَهُوَ عَلَىٰ نُورٖ مِّن رَّبِّهِۦۚ فَوَيۡلٞ لِّلۡقَٰسِيَةِ قُلُوبُهُم مِّن ذِكۡرِ ٱللَّهِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

Yanzu wanda Allah Ya buxa masa qirjinsa da Musulunci don haka ya zama cikin haske daga Ubangijinsa (zai yi kamar wanda zuciyarsa ta qeqashe?) To tsananin azaba ya tabbata ga masu qeqasassun zukata da ba sa ambaton Allah. Waxannan suna cikin vata mabayyani



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 23

ٱللَّهُ نَزَّلَ أَحۡسَنَ ٱلۡحَدِيثِ كِتَٰبٗا مُّتَشَٰبِهٗا مَّثَانِيَ تَقۡشَعِرُّ مِنۡهُ جُلُودُ ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ ثُمَّ تَلِينُ جُلُودُهُمۡ وَقُلُوبُهُمۡ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ هُدَى ٱللَّهِ يَهۡدِي بِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٍ

Allah Ya saukar da mafi kyan zance: Alqur’ani mai kama da juna, mai biyunta (saqo), tsikar fatun waxanda suke tsoron Ubangijinsu suna tashi, sannan fatunsu su yi taushi, zukatansu kuwa su koma zuwa ambaton Allah. Wannan ita ce shiriyar Allah, Yana shiyar da wanda Ya ga dama da ita. Wanda kuma Allah Ya vatar to ba shi da mai shiryar da shi



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 24

أَفَمَن يَتَّقِي بِوَجۡهِهِۦ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَقِيلَ لِلظَّـٰلِمِينَ ذُوقُواْ مَا كُنتُمۡ تَكۡسِبُونَ

Yanzu wanda yake kare mummunar azaba da fuskarsa[1] a ranar alqiyama (zai yi kama da wanda ba ya yi?) Aka kuma ce da azzalumai: “Ku xanxani abin da kuka kasance kuna aikatawa.”


1- Watau kafirin da aka xaure masa hannayensa aka kuma jefa shi wuta, don haka yake kare wuta da fuskarsa.


Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 25

كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَأَتَىٰهُمُ ٱلۡعَذَابُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَشۡعُرُونَ

Waxanda suke gabaninsu sun qaryata, sai azaba ta zo musu daga inda ba sa tsammani



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 26

فَأَذَاقَهُمُ ٱللَّهُ ٱلۡخِزۡيَ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَكۡبَرُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ

Sannan Allah Ya xanxana musu azabar wulaqanci a rayuwar duniya, kuma lalle azabar lahira ta fi girma. Da sun kasance sun san (hakan)



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 27

وَلَقَدۡ ضَرَبۡنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٖ لَّعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ

Kuma haqiqa Mun ba wa mutane kowane nau’i na misali a cikin wannan Alqur’ani don su wa’azantu



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 28

قُرۡءَانًا عَرَبِيًّا غَيۡرَ ذِي عِوَجٖ لَّعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ

Alqur’ani Balarabe marar karkata don su sami taqawa



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 29

ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا رَّجُلٗا فِيهِ شُرَكَآءُ مُتَشَٰكِسُونَ وَرَجُلٗا سَلَمٗا لِّرَجُلٍ هَلۡ يَسۡتَوِيَانِ مَثَلًاۚ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Allah Ya ba da misali na wani namiji (bawa) wanda yake da iyayen giji masu tarayya a kansa masu jayayya (a kan ba shi umarni) da kuma wani namiiji (bawa) da ya kevanta ga wani namiji guda, shin misalinsu za su yi daidai? Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. A’a, yawancinsu dai ba su sani ba ne



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 30

إِنَّكَ مَيِّتٞ وَإِنَّهُم مَّيِّتُونَ

Lalle kai mai mutuwa ne, su ma kuma lalle masu mutuwa ne