Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 1

الٓمٓ

ALIF LAM MIM[1]


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 2

أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتۡرَكُوٓاْ أَن يَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا وَهُمۡ لَا يُفۡتَنُونَ

Yanzu mutane suna tsammanin za a qyale su ne saboda suna cewa: “Mun yi imani,” kuma ba za a fitine su ba?



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 3

وَلَقَدۡ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Haqiqa kuwa Mun fitini waxanda suke gabaninsu; to tabbas kuwa Allah zai bayyana waxanda suka yi gaskiya, lalle kuma zai bayyana maqaryata



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 4

أَمۡ حَسِبَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن يَسۡبِقُونَاۚ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ

Ko kuma waxanda suke aikata munanan ayyuka suna tsammanin za su gagare Mu ne? Abin da suke hukuntawa ya munana



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 5

مَن كَانَ يَرۡجُواْ لِقَآءَ ٱللَّهِ فَإِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ لَأٓتٖۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Wanda ya zama yana fatan haxuwa da Allah, to lalle lokacin (haxuwa da) Allah tabbas mai zuwa ne. Kuma Shi ne Mai ji, Masani



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 6

وَمَن جَٰهَدَ فَإِنَّمَا يُجَٰهِدُ لِنَفۡسِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَغَنِيٌّ عَنِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Duk wanda kuwa ya yi jihadi, to yana jihadin ne don kansa. Lalle Allah tabbas Mawadaci ne daga talikai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 7

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَنُكَفِّرَنَّ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَحۡسَنَ ٱلَّذِي كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waxanda kuma suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, tabbas za Mu kankare musu munanan ayyukansu, kuma tabbas za Mu saka musu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 8

وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ حُسۡنٗاۖ وَإِن جَٰهَدَاكَ لِتُشۡرِكَ بِي مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٞ فَلَا تُطِعۡهُمَآۚ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Kuma Mun yi wa mutum wasiyya da kyautata wa iyayensa; idan kuma suka yaqe ka kan ka yi shirka da Ni game da abin da ba ka da sani a kansa, to kada ka bi su. Wurina ne makomarku take kawai, sannan zan ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 9

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَنُدۡخِلَنَّهُمۡ فِي ٱلصَّـٰلِحِينَ

Waxanda kuma suka yi imani suka yi ayyuka nagari tabbas za Mu shigar da su cikin salihai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 10

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ فَإِذَآ أُوذِيَ فِي ٱللَّهِ جَعَلَ فِتۡنَةَ ٱلنَّاسِ كَعَذَابِ ٱللَّهِۖ وَلَئِن جَآءَ نَصۡرٞ مِّن رَّبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمۡۚ أَوَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَعۡلَمَ بِمَا فِي صُدُورِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma cikin mutane akwai mai cewa: “Mun yi imani da Allah,” to idan aka cuce shi a kan hanyar Allah sai yakan xauki fitinar mutane kamar azabar Allah, lalle kuwa idan wata nasara ta zo daga Ubangijinka, tabbas zai riqa cewa: “Lalle mu mun kasance tare da ku.” Yanzu Allah ba Shi Ya fi kowa sanin abin da ke cikin zukatan talikai ba?



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 11

وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ

Tabbas kuma Allah zai bayyana waxanda suka yi imani, kuma tabbas zai bayyana munafukai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 12

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّبِعُواْ سَبِيلَنَا وَلۡنَحۡمِلۡ خَطَٰيَٰكُمۡ وَمَا هُم بِحَٰمِلِينَ مِنۡ خَطَٰيَٰهُم مِّن شَيۡءٍۖ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

Kuma waxanda suka kafirta suka ce da waxanda suka yi imani: “Ku bi tafarkinmu, (mu) lalle za mu xauke muku laifuffukanku,” alhali kuwa su ba za su iya xauke wani abu na laifuffukansu ba; lalle su dai tabbas maqaryata ne



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 13

وَلَيَحۡمِلُنَّ أَثۡقَالَهُمۡ وَأَثۡقَالٗا مَّعَ أَثۡقَالِهِمۡۖ وَلَيُسۡـَٔلُنَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَمَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

Tabbas kuma za su xauki zunubansu da kuma wasu zunuban tare da zunubansu[1]; kuma tabbas za a tambaye su a ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna qirqira


1- Watau tare da zunuban waxanda suka yaudara suka vatar da su, ba kuma tare da an rage zunuban mabiyansu ba.


Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 14

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَلَبِثَ فِيهِمۡ أَلۡفَ سَنَةٍ إِلَّا خَمۡسِينَ عَامٗا فَأَخَذَهُمُ ٱلطُّوفَانُ وَهُمۡ ظَٰلِمُونَ

Kuma haqiqa Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya zauna cikinsu shekara dubu ba hamsin, sai (ruwan) Xufana ya ci su, alhalin suna azzalumai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 15

فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَصۡحَٰبَ ٱلسَّفِينَةِ وَجَعَلۡنَٰهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

Sai Muka tserar da shi tare da mutanen jirgin ruwa, Muka kuma sanya shi (jirgin) aya ga talikai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 16

وَإِبۡرَٰهِيمَ إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُۖ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Kuma (ka tuna) Ibrahimu lokacin da ya ce da mutanensa: “Ku bauta wa Allah, kuma ku kiyaye dokokinsa, wannan shi ya fi muku alheri in kun kasance kun san (haka)



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 17

إِنَّمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا وَتَخۡلُقُونَ إِفۡكًاۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ لَكُمۡ رِزۡقٗا فَٱبۡتَغُواْ عِندَ ٱللَّهِ ٱلرِّزۡقَ وَٱعۡبُدُوهُ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥٓۖ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Lalle abin da kuke bauta wa ba Allah ba gumaka ne kawai, kuna kuma qirqirar qarya ne[1]. Lalle waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba su mallaki wani arziki ba gare ku, sai ku nemi arziki a wurin Allah, kuma ku bauta masa, ku kuma gode masa; gare Shi ne kawai za a mayar da ku


1- Domin su ne suke sassaqa su da hannayensu suke kuma sanya musu sunaye sannan su bauta musu.


Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 18

وَإِن تُكَذِّبُواْ فَقَدۡ كَذَّبَ أُمَمٞ مِّن قَبۡلِكُمۡۖ وَمَا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

Idan kuma kuka qaryata, to haqiqa da ma wasu al’ummun da suke gabaninku sun qaryata; ba abin da yake kan Manzo sai isar da saqo mabayyani



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 19

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ كَيۡفَ يُبۡدِئُ ٱللَّهُ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥٓۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ

Yanzu ba su ga yadda Allah Yake farar halitta ba, sannan Shi ne kuma zai mayar da ita? Lalle wannan mai sauqi ne a wurin Allah



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 20

قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ بَدَأَ ٱلۡخَلۡقَۚ ثُمَّ ٱللَّهُ يُنشِئُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأٓخِرَةَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Ka ce: “Ku yi tafiya a bayan qasa sai ku duba ku ga yadda Allah Ya fari halittu. Sannan Allah ne zai sake samar da su samarwar qarshe. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 21

يُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ وَيَرۡحَمُ مَن يَشَآءُۖ وَإِلَيۡهِ تُقۡلَبُونَ

“Yana azabtar da wanda Ya ga dama, Yana kuma jin qan wanda Ya ga dama; kuma wurinsa kawai za a mayar da ku



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 22

وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ

“Kuma ku ba za ku gagara ba a qasa ko kuma a sama; kuma ba ku da wani majivinci ko mataimaki in ba Allah ba.”



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 23

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَلِقَآئِهِۦٓ أُوْلَـٰٓئِكَ يَئِسُواْ مِن رَّحۡمَتِي وَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Waxanda kuma suka kafirce wa ayoyin Allah da kuma gamuwa da Shi, waxannan sun xebe qauna daga rahamata, kuma waxannan suna da azaba mai raxaxi



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 24

فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوۡمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُواْ ٱقۡتُلُوهُ أَوۡ حَرِّقُوهُ فَأَنجَىٰهُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلنَّارِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

To ba wani jawabi da ya fito daga bakin mutanensa sai cewa da suka yi: “Ku kashe shi ko kuma ku qone shi!” Sai Allah Ya tserar da shi daga wutar. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suka yi imani



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 25

وَقَالَ إِنَّمَا ٱتَّخَذۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا مَّوَدَّةَ بَيۡنِكُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ ثُمَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَكۡفُرُ بَعۡضُكُم بِبَعۡضٖ وَيَلۡعَنُ بَعۡضُكُم بَعۡضٗا وَمَأۡوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Kuma ya ce (da su): “Lalle ba abin da kuka riqa wanin Allah sai gumaka kawai don qauna da take tsakaninku a rayuwar duniya; sannan ranar alqiyama wasunku za su kafirce wa wasu, kuma wasunku za su la’anci wasu, makomarku kuma wuta ce, ba ku da kuwa wasu mataimaka.”



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 26

۞فَـَٔامَنَ لَهُۥ لُوطٞۘ وَقَالَ إِنِّي مُهَاجِرٌ إِلَىٰ رَبِّيٓۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Sai Luxu ya yi imani da shi. (Sai Ibrahimu) kuma ya ce: “Lalle ni mai yin hijira ne zuwa ga Ubangijina; lalle Shi Mabuwayi ne, Mai hikima.”



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 27

وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَجَعَلۡنَا فِي ذُرِّيَّتِهِ ٱلنُّبُوَّةَ وَٱلۡكِتَٰبَ وَءَاتَيۡنَٰهُ أَجۡرَهُۥ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَإِنَّهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Muka kuma yi masa baiwa da (xansa) Is’haqa da kuma (jikansa) Ya’aqubu, Muka kuma sanya annabta da littafi a cikin zuriyarsa, Muka kuma ba shi ladansa a duniya; kuma lalle shi a lahira tabbas yana cikin salihai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 28

وَلُوطًا إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ إِنَّكُمۡ لَتَأۡتُونَ ٱلۡفَٰحِشَةَ مَا سَبَقَكُم بِهَا مِنۡ أَحَدٖ مِّنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma (ka tuna) Luxu lokacin da ya ce da mutanensa: “Lalle ku kuna zaike wa mummunan aiki wanda ba wani mutum guda daga talikai da ya rigaye ku (aikata) shi



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 29

أَئِنَّكُمۡ لَتَأۡتُونَ ٱلرِّجَالَ وَتَقۡطَعُونَ ٱلسَّبِيلَ وَتَأۡتُونَ فِي نَادِيكُمُ ٱلۡمُنكَرَۖ فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوۡمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُواْ ٱئۡتِنَا بِعَذَابِ ٱللَّهِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

“Yanzu kwa riqa zaike wa maza, ku kuma riqa tsare hanya (kuna yin fashi), kuma kuna aikata abin qi a cikin majalisarku[1]?” Ba wani jawabi da ya fito daga bakin mutanensa sai cewa suka yi: “To ka zo mana da azabar Allah idan ka kasance cikin masu gaskiya.”


1- Watau kamar nuna tsiraici da cutar da masu wucewa a hanya da maganganunsu da ayyukansu.


Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 30

قَالَ رَبِّ ٱنصُرۡنِي عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

(Sai Luxu) ya ce: “Ya Ubangijina, Ka taimake ni kan mutanen nan mavarnata.”