Sourate: Suratun Nur

Verset : 1

سُورَةٌ أَنزَلۡنَٰهَا وَفَرَضۡنَٰهَا وَأَنزَلۡنَا فِيهَآ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖ لَّعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ

Wannan Sura ce da Muka saukar da ita Muka kuma wajabta (hukunce-hukuncen da suke cikinta), Muka kuma saukar da ayoyi bayyanannu a cikinta don ku wa’azantu



Sourate: Suratun Nur

Verset : 2

ٱلزَّانِيَةُ وَٱلزَّانِي فَٱجۡلِدُواْ كُلَّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا مِاْئَةَ جَلۡدَةٖۖ وَلَا تَأۡخُذۡكُم بِهِمَا رَأۡفَةٞ فِي دِينِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۖ وَلۡيَشۡهَدۡ عَذَابَهُمَا طَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Mazinaciya da mazinaci (idan suka yi zina) sai ku yi wa kowanne xaya daga cikinsu bulala xari[1], kada kuwa wani tausayi ya kama ku game da (tabbatar da hukuncin) addinin Allah idan kun kasance kuna imani da Allah da ranar lahira; kuma lalle ne wata qungiya daga cikin muminai su halarci (wurin) yi musu haddin


1- Ga waxanda ba su yi aure ba, bayan an samu shaidun gani da ido maza huxu; ko sun yi iqirari; ko ta zo da ciki ba tare da aure ba kuma ba sa-xaka ba.


Sourate: Suratun Nur

Verset : 3

ٱلزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوۡ مُشۡرِكَةٗ وَٱلزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَآ إِلَّا زَانٍ أَوۡ مُشۡرِكٞۚ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Mazinaci ba ya aure sai da karuwa ko mushirika, karuwa kuma ba ta aure sai da mazinaci ko mushiriki. An kuma haramta wannan ga muminai



Sourate: Suratun Nur

Verset : 4

وَٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَأۡتُواْ بِأَرۡبَعَةِ شُهَدَآءَ فَٱجۡلِدُوهُمۡ ثَمَٰنِينَ جَلۡدَةٗ وَلَا تَقۡبَلُواْ لَهُمۡ شَهَٰدَةً أَبَدٗاۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Waxanda kuwa suke jifan mata masu kamun kai sannan ba su kawo shaidu huxu ba, sai ku yi musu bulala tamanin, kuma kada ku karvi shaidarsu har abada. Waxannan kuma su ne fasiqai



Sourate: Suratun Nur

Verset : 5

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sai dai waxanda suka tuba bayan wannan suka kuma gyara, to haqiqa Allah Mai gafara ne, Mai jin qai ne



Sourate: Suratun Nur

Verset : 6

وَٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ أَزۡوَٰجَهُمۡ وَلَمۡ يَكُن لَّهُمۡ شُهَدَآءُ إِلَّآ أَنفُسُهُمۡ فَشَهَٰدَةُ أَحَدِهِمۡ أَرۡبَعُ شَهَٰدَٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Waxanda kuma suke jifan matayensu (da zina) kuma ba su da wasu shaidu sai su kansu, to shaidar xayansu ita ce ya rantsuwa da Allah sau huxu a kan cewa shi lalle yana daga masu gaskiya



Sourate: Suratun Nur

Verset : 7

وَٱلۡخَٰمِسَةُ أَنَّ لَعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

(Rantsuwa) ta biyar kuwa kan cewa tsinuwar Allah ta hau kansa in ya kasance daga cikin maqaryata



Sourate: Suratun Nur

Verset : 8

وَيَدۡرَؤُاْ عَنۡهَا ٱلۡعَذَابَ أَن تَشۡهَدَ أَرۡبَعَ شَهَٰدَٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Kuma (abin da) zai kawar mata da azabar haddi shi ne ta yi rantsuwa da Allah sau huxu kan cewa shi lalle yana daga cikin maqaryata



Sourate: Suratun Nur

Verset : 9

وَٱلۡخَٰمِسَةَ أَنَّ غَضَبَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَآ إِن كَانَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

(Rantsuwa) ta biyar kuwa kan cewa lalle fushin Allah ya hau kanta idan ya kasance daga masu gaskiya



Sourate: Suratun Nur

Verset : 10

وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ وَأَنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٌ حَكِيمٌ

Ba don falalar Allah gare ku ba da rahamarsa, da kuma cewa Allah Mai karvar tuba ne, Mai hikima (to da ya kunyata maqaryaci)



Sourate: Suratun Nur

Verset : 11

إِنَّ ٱلَّذِينَ جَآءُو بِٱلۡإِفۡكِ عُصۡبَةٞ مِّنكُمۡۚ لَا تَحۡسَبُوهُ شَرّٗا لَّكُمۖ بَلۡ هُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۚ لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُم مَّا ٱكۡتَسَبَ مِنَ ٱلۡإِثۡمِۚ وَٱلَّذِي تَوَلَّىٰ كِبۡرَهُۥ مِنۡهُمۡ لَهُۥ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Lalle waxanda suka zo da qagaggiyar qarya wasu jama’a ne daga cikinku[1]. Kada ku zace shi sharri ne a gare ku; a’a, shi alheri ne a gare ku. Kowanne mutum daga cikinsu yana da sakamakon abin da ya aikata na zunubi. Wanda kuwa ya jivinci fara kwaza shi daga cikinsu[2] yana da azaba mai girma


1- Daga nan zuwa aya ta 26 suna magana ne a kan qazafin zina da munafukai suka yi wa Nana A’isha ().


2- Shi ne shugaban munafukan Madina Abdullahi xan Ubayyu xan Salul.


Sourate: Suratun Nur

Verset : 12

لَّوۡلَآ إِذۡ سَمِعۡتُمُوهُ ظَنَّ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ بِأَنفُسِهِمۡ خَيۡرٗا وَقَالُواْ هَٰذَآ إِفۡكٞ مُّبِينٞ

Me ya hana lokacin da kuka ji shi (wato qyagen) muminai maza da muminai mata ba su yi wa kawunansu zaton alheri ba suka kuma ce, wannan ai qage ne bayyananne?



Sourate: Suratun Nur

Verset : 13

لَّوۡلَا جَآءُو عَلَيۡهِ بِأَرۡبَعَةِ شُهَدَآءَۚ فَإِذۡ لَمۡ يَأۡتُواْ بِٱلشُّهَدَآءِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ عِندَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ

Me ya hana su kawo shaidu huxu game da shi (qagen)? To tun da yake ba su kawo shaidun ba, to waxannan a wurin Allah su ne maqaryata



Sourate: Suratun Nur

Verset : 14

وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ لَمَسَّكُمۡ فِي مَآ أَفَضۡتُمۡ فِيهِ عَذَابٌ عَظِيمٌ

Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba a duniya da lahira, to tabbas da azaba mai girma ta shafe ku game da abin da kuka kutsa cikinsa



Sourate: Suratun Nur

Verset : 15

إِذۡ تَلَقَّوۡنَهُۥ بِأَلۡسِنَتِكُمۡ وَتَقُولُونَ بِأَفۡوَاهِكُم مَّا لَيۡسَ لَكُم بِهِۦ عِلۡمٞ وَتَحۡسَبُونَهُۥ هَيِّنٗا وَهُوَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمٞ

Yayin da kuke bayeyeniyarsa (qagen) da harsunanku, kuke faxar abin da ba ku sani ba da bakunanku, kuke kuma tsammaninsa abu ne mai sauqi, alhali kuwa shi mai girma ne a wurin Allah



Sourate: Suratun Nur

Verset : 16

وَلَوۡلَآ إِذۡ سَمِعۡتُمُوهُ قُلۡتُم مَّا يَكُونُ لَنَآ أَن نَّتَكَلَّمَ بِهَٰذَا سُبۡحَٰنَكَ هَٰذَا بُهۡتَٰنٌ عَظِيمٞ

Me ya hana yayin da kuka ji shi ku ce: “Bai dace da mu mu yi irin wannan magana ba,” (kuma ku ce:) “Subhanallahi! Ai wannan qage ne babba!”



Sourate: Suratun Nur

Verset : 17

يَعِظُكُمُ ٱللَّهُ أَن تَعُودُواْ لِمِثۡلِهِۦٓ أَبَدًا إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Allah Yana gargaxin ku kada ku koma yin irinsa har abada idan kun zamanto muminai



Sourate: Suratun Nur

Verset : 18

وَيُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِۚ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ

Allah kuma yana bayyana muku ayoyinsa ne, Allah kuwa Masani ne, Mai hikima



Sourate: Suratun Nur

Verset : 19

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحِبُّونَ أَن تَشِيعَ ٱلۡفَٰحِشَةُ فِي ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

Lalle waxanda suke son yaxuwar mummunan abu a cikin waxanda suka yi imani suna da (sakamakon) azaba mai raxaxi a duniya da lahira, kuma Allah (Shi) ne Yake sane, ku ba ba ku san komai ba



Sourate: Suratun Nur

Verset : 20

وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ وَأَنَّ ٱللَّهَ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ

Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba, da kuma cewa lalle Allah Mai tausayi ne, Mai rahama (da kun faxa cikin hallaka)



Sourate: Suratun Nur

Verset : 21

۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ وَمَن يَتَّبِعۡ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَإِنَّهُۥ يَأۡمُرُ بِٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِۚ وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ مَا زَكَىٰ مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ أَبَدٗا وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُزَكِّي مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin Shaixan, wanda kuwa duk ya bi hanyoyin Shaixan, to lalle shi (Shaixan) umarni yake yi da aikata alfasha da abin qyama. Ba don kuma falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba, da babu xaya daga cikinku da zai tsarkaka har abada, sai dai kuma Allah (Shi) Yake tsarkake wanda Ya ga dama, Allah kuwa Mai ji ne, Masani



Sourate: Suratun Nur

Verset : 22

وَلَا يَأۡتَلِ أُوْلُواْ ٱلۡفَضۡلِ مِنكُمۡ وَٱلسَّعَةِ أَن يُؤۡتُوٓاْ أُوْلِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينَ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ وَلۡيَعۡفُواْ وَلۡيَصۡفَحُوٓاْۗ أَلَا تُحِبُّونَ أَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

Kuma kada masu hali da wadata daga cikinku su rantse a kan qin ba da (abin hannunsu) ga makusanta da miskinai da masu hijira saboda Allah. Su kuma yi afuwa su yafe. Shin ku ba kwa so ne Allah Ya gafarta muku? Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai[1]


1- Ayar tana magana ne a kan Abubakar () lokacin da ya yi rantsuwa ba zai ci gaba da taimaka wa xan innarsa Misxahu xan Usasa ba domin ya zama cikin masu kwaza qagen da aka yi wa Nana A’isha (RAH)..


Sourate: Suratun Nur

Verset : 23

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ٱلۡغَٰفِلَٰتِ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ لُعِنُواْ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Lalle waxanda suke jifan kamammun mata waxanda ba su san me yake faruwa ba, muminai, (suke jifan su da zina), to an la’ance su duniya da lahira, kuma suna da (sakamakon) azaba mai girma



Sourate: Suratun Nur

Verset : 24

يَوۡمَ تَشۡهَدُ عَلَيۡهِمۡ أَلۡسِنَتُهُمۡ وَأَيۡدِيهِمۡ وَأَرۡجُلُهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

A ranar da harsunansu da hannayensu da kuma qafafunsu za su ba da shaida a kansu game da abin da suka kasance suna aikatawa



Sourate: Suratun Nur

Verset : 25

يَوۡمَئِذٖ يُوَفِّيهِمُ ٱللَّهُ دِينَهُمُ ٱلۡحَقَّ وَيَعۡلَمُونَ أَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ ٱلۡمُبِينُ

A wannan ranar Allah zai ba su cikakken sakamakonsu na gaskiya kuma za su san cewa lalle Allah Shi ne gaskiya bayyananniya



Sourate: Suratun Nur

Verset : 26

ٱلۡخَبِيثَٰتُ لِلۡخَبِيثِينَ وَٱلۡخَبِيثُونَ لِلۡخَبِيثَٰتِۖ وَٱلطَّيِّبَٰتُ لِلطَّيِّبِينَ وَٱلطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَٰتِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ مُبَرَّءُونَ مِمَّا يَقُولُونَۖ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ

Miyagun mata da miyagun maganganu sun dace da miyagun maza. Kuma miyagun maza da miyagun maganganu sun dace ne da miyagun mata. Tsarkakan mata da tsarkakan maganganu sun dace da tsarkakan maza. Kuma tsarkakan maza da tsakakan maganganu sun dace da tsarkakan mata. Su waxannan (tsarkaka) kuwa wankakakku ne daga abin da suke faxa (na qage a kansu), suna da (sakamakon) gafara da arziki mai girma



Sourate: Suratun Nur

Verset : 27

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَدۡخُلُواْ بُيُوتًا غَيۡرَ بُيُوتِكُمۡ حَتَّىٰ تَسۡتَأۡنِسُواْ وَتُسَلِّمُواْ عَلَىٰٓ أَهۡلِهَاۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini, kuma kun yi sallama ga masu su. Wannan kuwa shi ya fi alheri a gare ku don ku wa’azantu



Sourate: Suratun Nur

Verset : 28

فَإِن لَّمۡ تَجِدُواْ فِيهَآ أَحَدٗا فَلَا تَدۡخُلُوهَا حَتَّىٰ يُؤۡذَنَ لَكُمۡۖ وَإِن قِيلَ لَكُمُ ٱرۡجِعُواْ فَٱرۡجِعُواْۖ هُوَ أَزۡكَىٰ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ

To idan ba ku sami kowa a cikinsu ba to kada ku shige su har sai an yi muku izini; idan kuwa aka ce da ku ku koma sai ku koma; wannan shi ya fi tsarki a gare ku. Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne



Sourate: Suratun Nur

Verset : 29

لَّيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَدۡخُلُواْ بُيُوتًا غَيۡرَ مَسۡكُونَةٖ فِيهَا مَتَٰعٞ لَّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُبۡدُونَ وَمَا تَكۡتُمُونَ

Babu wani laifi a kanku ku shiga gidaje waxanda ba wani zaune a cikinsu, kuma akwai kayanku a cikinsu[1], kuma Allah Yana sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuke voyewa


1- Watau wuraren da aka tanada domin amfanin kowa da kowa, kamar xakunan karatu ko shaguna a kasuwanni.


Sourate: Suratun Nur

Verset : 30

قُل لِّلۡمُؤۡمِنِينَ يَغُضُّواْ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِمۡ وَيَحۡفَظُواْ فُرُوجَهُمۡۚ ذَٰلِكَ أَزۡكَىٰ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا يَصۡنَعُونَ

Ka ce da muminai maza su kame idanuwansu[1] kuma su kiyaye farjinsu. Wannan shi ya fi tsarki a gare su. Lalle Allah Masanin abin da suke aikatawa ne


1- Watau su kawar da idanuwansu daga kallon matan da bai halatta su kalle su ba, hakanan da kallon al’aurarsu.