Sourate: Suratul Hajji

Verset : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ إِنَّ زَلۡزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَيۡءٌ عَظِيمٞ

Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku. Lalle girgizar (ranar) alqiyama abu ne mai girma



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 2

يَوۡمَ تَرَوۡنَهَا تَذۡهَلُ كُلُّ مُرۡضِعَةٍ عَمَّآ أَرۡضَعَتۡ وَتَضَعُ كُلُّ ذَاتِ حَمۡلٍ حَمۡلَهَا وَتَرَى ٱلنَّاسَ سُكَٰرَىٰ وَمَا هُم بِسُكَٰرَىٰ وَلَٰكِنَّ عَذَابَ ٱللَّهِ شَدِيدٞ

Ranar da za ku gan ta, (don tsananin firgita) kowacce mai shayarwa za ta manta da abin da ta shayar, kuma kowacce mai ciki ta zubar da cikinta, ka ga kuma mutane suna tangaxi, alhali kuwa ba bugaggu ba ne, sai dai azabar Allah ce mai tsanani



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 3

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيۡطَٰنٖ مَّرِيدٖ

Daga mutane kuma akwai wanda yake jayayya game da Allah ba tare da wani ilimi ba, kuma yake bin kowanne shaixani mai tsaurin kai



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 4

كُتِبَ عَلَيۡهِ أَنَّهُۥ مَن تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُۥ يُضِلُّهُۥ وَيَهۡدِيهِ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

An qaddara masa (wato Shaixan) cewa duk wanda ya rungume shi to haqiqa zai vatar da shi kuma ya ja shi zuwa ga azaba ta (wutar) Sa’ira



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 5

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّنَ ٱلۡبَعۡثِ فَإِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ مِن مُّضۡغَةٖ مُّخَلَّقَةٖ وَغَيۡرِ مُخَلَّقَةٖ لِّنُبَيِّنَ لَكُمۡۚ وَنُقِرُّ فِي ٱلۡأَرۡحَامِ مَا نَشَآءُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ نُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡۖ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرۡذَلِ ٱلۡعُمُرِ لِكَيۡلَا يَعۡلَمَ مِنۢ بَعۡدِ عِلۡمٖ شَيۡـٔٗاۚ وَتَرَى ٱلۡأَرۡضَ هَامِدَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡ وَأَنۢبَتَتۡ مِن كُلِّ زَوۡجِۭ بَهِيجٖ

Ya ku mutane, idan kun zamanto cikin kokwanton tashi (bayan mutuwa), to lalle Mu Muka halicce ku daga qasa, sannan daga maniyyi, sannan daga gudan jini, sannan daga tsoka, mai cikakkiyar halitta da kuma wadda ba cikakkiya ba[1], don Mu bayyana muku (Ikonmu). Kuma Muna tabbatar da abin da Muka ga dama a cikin mahaifa har zuwa wani lokaci qayyadajje, sannan kuma Mu fito da ku kuna jarirai, sannan kuma don ku kai cikar qarfinku; daga cikinku akwai wanda za a karvi ransa, akwai kuma wanda za a bari har zuwa mafi qasqantar rayuwa don ya kai ga halin da ba zai san komai ba bayan kuwa da can ya sani. Za ka kuma ga qasa a qeqashe, sannan idan Muka saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura kuma ta fitar da kowanne irin tsiro mai qayatarwa


1- Watau tsokar ta zama wata halitta wadda ba cikakken mutum ba, daga bisani a yi varin ta.


Sourate: Suratul Hajji

Verset : 6

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّهُۥ يُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَأَنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Wannan (kuwa) saboda lalle Allah Shi ne gaskiya, kuma lalle Shi ne Yake raya matattu, kuma lalle Mai iko ne a kan komai



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 7

وَأَنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٞ لَّا رَيۡبَ فِيهَا وَأَنَّ ٱللَّهَ يَبۡعَثُ مَن فِي ٱلۡقُبُورِ

Kuma lalle Alqiyama za ta zo babu kokwanto game da ita, kuma lalle Allah zai tashi waxanda suke cikin qaburbura



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 8

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَلَا هُدٗى وَلَا كِتَٰبٖ مُّنِيرٖ

Daga mutane kuma akwai wanda yake jayayya game da (al’amarin) Allah ba tare da ilimi ba ko shiriya ko kuma wani littafi mai haske



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 9

ثَانِيَ عِطۡفِهِۦ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۖ لَهُۥ فِي ٱلدُّنۡيَا خِزۡيٞۖ وَنُذِيقُهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

Yana juyar da kansa don ya vatar da (mutane) daga hanyar Allah; yana da wulaqanci a duniya; kuma ranar alqiyama Mu xanxana masa azabar quna



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 10

ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتۡ يَدَاكَ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيۡسَ بِظَلَّـٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ

(Za a ce da shi): “Wannan (kuwa) saboda abin da hannayenka suka aikata ne, kuma lalle Allah ba Mai zaluntar bayi ba ne.”



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 11

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَعۡبُدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ حَرۡفٖۖ فَإِنۡ أَصَابَهُۥ خَيۡرٌ ٱطۡمَأَنَّ بِهِۦۖ وَإِنۡ أَصَابَتۡهُ فِتۡنَةٌ ٱنقَلَبَ عَلَىٰ وَجۡهِهِۦ خَسِرَ ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةَۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡخُسۡرَانُ ٱلۡمُبِينُ

Daga mutane kuma akwai wanda yake bauta wa Allah a kan gava[1]; to idan alheri ya same shi sai ya nutsu da shi, idan kuwa wata masifa ta same shi sai ya juya a kan fuskarsa; to ya yi hasarar duniya da lahira. Wannan (kuwa) ita ce hasara bayyananniya


1- Watau yana bautar Allah cikin shakku, shi ne munafuki.


Sourate: Suratul Hajji

Verset : 12

يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُۥ وَمَا لَا يَنفَعُهُۥۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَٰلُ ٱلۡبَعِيدُ

Yana bauta wa wanin Allah, abin da ba zai cuce shi ba kuma ba zai amfane shi ba. Wannan kuwa shi ne vata mai nisa



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 13

يَدۡعُواْ لَمَن ضَرُّهُۥٓ أَقۡرَبُ مِن نَّفۡعِهِۦۚ لَبِئۡسَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَلَبِئۡسَ ٱلۡعَشِيرُ

Yana bauta wa abin da cutarsa ta fi kusa fiye da amfaninsa. Tabbas mataimaki ya munana, kuma tabbas aboki ya munana



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 14

إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يُرِيدُ

Lalle Allah Yana shigar da waxanda suka yi imani kuma suka yi aiki na gari gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Lalle Allah Yana aikata abin da Ya ga dama



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 15

مَن كَانَ يَظُنُّ أَن لَّن يَنصُرَهُ ٱللَّهُ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ فَلۡيَمۡدُدۡ بِسَبَبٍ إِلَى ٱلسَّمَآءِ ثُمَّ لۡيَقۡطَعۡ فَلۡيَنظُرۡ هَلۡ يُذۡهِبَنَّ كَيۡدُهُۥ مَا يَغِيظُ

Wanda ya zamanto yana tsammanin cewa Allah ba zai taimake shi ba, (wato Annabinsa) a duniya da lahira, to sai ya hau sama da igiya, sannan ya yanke ta[1], ya duba shin wannan mugun tanadi nasa zai kawar da abin da yake cike da haushinsa?


1- Watau ya faxo qasa; ko kuma ya shaqe kansa da ita.


Sourate: Suratul Hajji

Verset : 16

وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖ وَأَنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يُرِيدُ

Kamar haka kuwa Muka saukar da shi (Alqur’ani) ayoyi mabayyana, kuma lalle Allah Yana shiryar da wanda Yake nufin (shiryar da shi)



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 17

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلصَّـٰبِـِٔينَ وَٱلنَّصَٰرَىٰ وَٱلۡمَجُوسَ وَٱلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡصِلُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

Lalle waxanda suka yi imani da waxanda suka zama Yahudawa da Sabi’awa da waxanda suka zama Majusawa da kuma waxanda suka yi shirka, lalle Allah zai yi hukunci a tsakaninsu ranar alqiyama. Lalle Allah Mai ganin kowane abu ne



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 18

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يَسۡجُدُۤ لَهُۥۤ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ وَٱلنُّجُومُ وَٱلۡجِبَالُ وَٱلشَّجَرُ وَٱلدَّوَآبُّ وَكَثِيرٞ مِّنَ ٱلنَّاسِۖ وَكَثِيرٌ حَقَّ عَلَيۡهِ ٱلۡعَذَابُۗ وَمَن يُهِنِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن مُّكۡرِمٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يَشَآءُ۩

Shin ba ka san cewa duk abin da yake cikin sammai da qasa suna yin sujjada ne ga Allah ba, (haka ma) rana da wata da taurari da duwatsu da bishiyoyi da dabbobi da kuma mutane masu yawa; da yawa kuma azaba ta tabbata a kansu? Duk kuwa wanda Allah Ya wulaqanta, to ba shi da wani mai girmama shi. Lalle Allah Yana aikata abin da Ya ga dama



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 19

۞هَٰذَانِ خَصۡمَانِ ٱخۡتَصَمُواْ فِي رَبِّهِمۡۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ قُطِّعَتۡ لَهُمۡ ثِيَابٞ مِّن نَّارٖ يُصَبُّ مِن فَوۡقِ رُءُوسِهِمُ ٱلۡحَمِيمُ

Biyu xin nan (muminai da kafirai) masu jayayya ne da suka yi jayayya game da Ubangijinsu (wato addininsu); waxanda suka kafirce sai aka xinka musu tufafi na wuta, kuma ana zuba musu tafasasshen ruwa ta saman kawunansu



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 20

يُصۡهَرُ بِهِۦ مَا فِي بُطُونِهِمۡ وَٱلۡجُلُودُ

Ana narka abin da yake cikinsu da shi (tafasasshen ruwan) da kuma fatu



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 21

وَلَهُم مَّقَٰمِعُ مِنۡ حَدِيدٖ

Suna kuma (shan duka) da gudumomi na baqin qarfe



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 22

كُلَّمَآ أَرَادُوٓاْ أَن يَخۡرُجُواْ مِنۡهَا مِنۡ غَمٍّ أُعِيدُواْ فِيهَا وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

Duk sanda suka yi nufin fita daga cikinta (wutar) saboda baqin ciki sai a sake mayar da su cikinta, (a ce da su): “Ku xanxani azabar gobara.”



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 23

إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَلُؤۡلُؤٗاۖ وَلِبَاسُهُمۡ فِيهَا حَرِيرٞ

Lalle Allah Yana shigar da waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na gari gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, ana yi musu ado a cikinsu da awarwaro na zinare da kuma lu’ulu’u; tufafinsu kuwa a cikinsu alharini ne



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 24

وَهُدُوٓاْ إِلَى ٱلطَّيِّبِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ وَهُدُوٓاْ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡحَمِيدِ

Kuma an shiryar da su zuwa ga magana mai daxi (a duniya, wato Kalmar Shahada), an kuma shiryar da su zuwa ga tafarkin (Allah) Sha-yabo



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 25

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ ٱلَّذِي جَعَلۡنَٰهُ لِلنَّاسِ سَوَآءً ٱلۡعَٰكِفُ فِيهِ وَٱلۡبَادِۚ وَمَن يُرِدۡ فِيهِ بِإِلۡحَادِۭ بِظُلۡمٖ نُّذِقۡهُ مِنۡ عَذَابٍ أَلِيمٖ

Lalle waxanda suka kafirta suke kuma toshe hanyar Allah da kuma Masallacin Harami wanda Muka sanya shi bai-xaya ga mutane, mazaunin cikinsa da kuma mai zuwa (daga waje). Wanda kuwa ya nufe shi da wata fanxara da zalunci to za Mu xanxana masa azaba mai raxaxi[1]


1- Watau qudurce niyyar aikata laifi a cikin hurumin Makka kawai ya isa ya jawo wa mutum azabar Allah ko da kuwa bai aikata ba.


Sourate: Suratul Hajji

Verset : 26

وَإِذۡ بَوَّأۡنَا لِإِبۡرَٰهِيمَ مَكَانَ ٱلۡبَيۡتِ أَن لَّا تُشۡرِكۡ بِي شَيۡـٔٗا وَطَهِّرۡ بَيۡتِيَ لِلطَّآئِفِينَ وَٱلۡقَآئِمِينَ وَٱلرُّكَّعِ ٱلسُّجُودِ

Kuma (ka tuna) lokacin da Muka nuna wa Ibrahimu gurbin Xakin (Ka’aba, Muka ce da shi): “Kada ka haxa komai da Ni (wajen bauta), kuma ka tsarkake Xakina ga masu xawafi da masu zama a cikinsa da kuma masu ruku’i masu sujjada



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 27

وَأَذِّن فِي ٱلنَّاسِ بِٱلۡحَجِّ يَأۡتُوكَ رِجَالٗا وَعَلَىٰ كُلِّ ضَامِرٖ يَأۡتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٖ

Kuma ka yi shela cikin mutane saboda yin Hajji, za su zo maka matafiya a qasa da kuma kan kowanne raqumi mai xamammen ciki, za su zo maka daga kowane wuri mai nisa



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 28

لِّيَشۡهَدُواْ مَنَٰفِعَ لَهُمۡ وَيَذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ فِيٓ أَيَّامٖ مَّعۡلُومَٰتٍ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّنۢ بَهِيمَةِ ٱلۡأَنۡعَٰمِۖ فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡبَآئِسَ ٱلۡفَقِيرَ

Don su halarci amfanin da za su samu, kuma su ambaci sunan Allah cikin kwanaki sanannu a kan abin da Ya arzuta su da shi na dabbobin ni’ima (watau raquma da tumaki da awakai da shanu); sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da galavaitaccen matalauci



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 29

ثُمَّ لۡيَقۡضُواْ تَفَثَهُمۡ وَلۡيُوفُواْ نُذُورَهُمۡ وَلۡيَطَّوَّفُواْ بِٱلۡبَيۡتِ ٱلۡعَتِيقِ

Sannan su kammala ayyukan hajjinsu (kamar yin aski da yanke farce), kuma su cika alqawuransu (na yin hadaya da layya), kuma su yi xawafi a ‘yantaccen Xaki (na Ka’aba)



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 30

ذَٰلِكَۖ وَمَن يُعَظِّمۡ حُرُمَٰتِ ٱللَّهِ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّهُۥ عِندَ رَبِّهِۦۗ وَأُحِلَّتۡ لَكُمُ ٱلۡأَنۡعَٰمُ إِلَّا مَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡۖ فَٱجۡتَنِبُواْ ٱلرِّجۡسَ مِنَ ٱلۡأَوۡثَٰنِ وَٱجۡتَنِبُواْ قَوۡلَ ٱلزُّورِ

Wannan (umarni da aka yi muku) kuwa, duk wanda ya girmama abubuwan da Allah Ya hana (a Hajji) to shi ya fi masa alheri a wurin Ubangijinsa. An kuma halatta muku dabbobin ni’ima, in ban da waxanda aka karanta muku (haramcinsu)[1]. To sai ku nisanci qazanta ta bauta wa gumaka, kuma ku nisanci faxar shaidar zur


1- Watau kamar abubuwan da aka ambata muku a Suratul An’am aya ta 145; da kuma wanda aka ambata bayan saukar wannan ayar kamar na cikin Suratul Ma’ida aya ta 3.