Sourate: Suratu Maryam

Verset : 1

كٓهيعٓصٓ

KAF HA YA AIN SAD[1]


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Sourate: Suratu Maryam

Verset : 2

ذِكۡرُ رَحۡمَتِ رَبِّكَ عَبۡدَهُۥ زَكَرِيَّآ

(Wannan) ambaton rahamar Ubangijinka ne (da Ya yi wa) Bawansa Zakariyya



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 3

إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ نِدَآءً خَفِيّٗا

Lokacin da ya kira Ubangijinsa (ya roqe Shi) cikin asiri



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 4

قَالَ رَبِّ إِنِّي وَهَنَ ٱلۡعَظۡمُ مِنِّي وَٱشۡتَعَلَ ٱلرَّأۡسُ شَيۡبٗا وَلَمۡ أَكُنۢ بِدُعَآئِكَ رَبِّ شَقِيّٗا

Ya ce: “Ya Ubangiji lalle qasusuwana sun yi rauni, kaina kuma ya yi fari fat da furfura, Ubangijina ban kuma zama mai tavewa ba game da roqon Ka



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 5

وَإِنِّي خِفۡتُ ٱلۡمَوَٰلِيَ مِن وَرَآءِي وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا فَهَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيّٗا

“Kuma lalle ni na ji tsoron dangina a bayana[1], matata kuma ga ta bakarara ce, saboda haka Ka yi mini baiwa daga gare Ka ta (xa) majivinci


1- Watau kada su watsar da kulawa da addini, su shagala da neman abincinsu.


Sourate: Suratu Maryam

Verset : 6

يَرِثُنِي وَيَرِثُ مِنۡ ءَالِ يَعۡقُوبَۖ وَٱجۡعَلۡهُ رَبِّ رَضِيّٗا

“(Wanda) zai gaje ni[1] ya kuma gaji iyalan Ya’aqub; Ubangijina kuma Ka sanya shi yardajje (a wurinka).”


1- Watau ya gaji ilimi da annabta da shugabantar gudanar da harkokin addini.


Sourate: Suratu Maryam

Verset : 7

يَٰزَكَرِيَّآ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ ٱسۡمُهُۥ يَحۡيَىٰ لَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ مِن قَبۡلُ سَمِيّٗا

(Aka ce): Ya Zakariyya, lalle Muna yi maka albishir da samun xa, sunansa Yahya, ba Mu kuwa sanya wa wani sunan ba gabaninsa



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 8

قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا وَقَدۡ بَلَغۡتُ مِنَ ٱلۡكِبَرِ عِتِيّٗا

Ya ce: “Ubangijina ta qaqa zan samu xa, alhali kuwa matata ta zamanto bakarara ce, ni kuma ga shi na tsufa tukuf”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 9

قَالَ كَذَٰلِكَ قَالَ رَبُّكَ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞ وَقَدۡ خَلَقۡتُكَ مِن قَبۡلُ وَلَمۡ تَكُ شَيۡـٔٗا

Ya ce: “Kamar haka Ubangijinka Ya faxa (cewa): ‘Shi (wannan) mai sauqi ne a wurina, don kuwa haqiqa Na halicce ka alhalin ba ka zama komai ba.’”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 10

قَالَ رَبِّ ٱجۡعَل لِّيٓ ءَايَةٗۖ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَٰثَ لَيَالٖ سَوِيّٗا

Ya ce: “Ubangijina Ka sanya mini wata alama.” Sai (Allah) Ya ce: “Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana (tsawon) kwana uku daidai.”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 11

فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ مِنَ ٱلۡمِحۡرَابِ فَأَوۡحَىٰٓ إِلَيۡهِمۡ أَن سَبِّحُواْ بُكۡرَةٗ وَعَشِيّٗا

Sannan (Zakariyya) ya fito wa mutanensa daga wurin ibada ya yi musu ishara cewa: “Ku yi tasbihi safe da maraice.”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 12

يَٰيَحۡيَىٰ خُذِ ٱلۡكِتَٰبَ بِقُوَّةٖۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡحُكۡمَ صَبِيّٗا

(Allah ya ce): “Ya Yahaya, ka riqi littafin (Attaura) da qarfi”; Muka kuma ba shi annabci tun yana qarami



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 13

وَحَنَانٗا مِّن لَّدُنَّا وَزَكَوٰةٗۖ وَكَانَ تَقِيّٗا

Kuma (Muka hore masa) tausayi daga gare Mu da tsarkin (zuciya), ya kuma kasance mai kiyaye dokokin Allah ne



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 14

وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَيۡهِ وَلَمۡ يَكُن جَبَّارًا عَصِيّٗا

Kuma mai biyayya ga mahaifansa, bai kuma zamanto mai taurin kai mai sava wa (umarnin Allah) ba



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 15

وَسَلَٰمٌ عَلَيۡهِ يَوۡمَ وُلِدَ وَيَوۡمَ يَمُوتُ وَيَوۡمَ يُبۡعَثُ حَيّٗا

Kuma aminci ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi da kuma ranar da zai mutu da kuma ranar da za a tashe shi rayayye



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 16

وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَرۡيَمَ إِذِ ٱنتَبَذَتۡ مِنۡ أَهۡلِهَا مَكَانٗا شَرۡقِيّٗا

Kuma ka ambaci (labarin) Maryamu a cikin (wannan) Littafi lokacin da ta qaurace wa mutanenta zuwa wani wuri a nahiyar gabas



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 17

فَٱتَّخَذَتۡ مِن دُونِهِمۡ حِجَابٗا فَأَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرٗا سَوِيّٗا

Sai ta saka shamaki tsakaninta da su (mutanen nata), to sai Muka aiko mata da Ruhinmu (shi ne Jibrilu) ya bayyana gare ta da surar daidaitaccen mutum



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 18

قَالَتۡ إِنِّيٓ أَعُوذُ بِٱلرَّحۡمَٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيّٗا

Ta ce: “Lalle ina neman Allah ya tsare ni daga gare ka idan ka zamanto mai taqawa ne.”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 19

قَالَ إِنَّمَآ أَنَا۠ رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَٰمٗا زَكِيّٗا

Ya ce: “Ni manzo ne kawai na Ubangijinki na zo don in yi miki baiwar xa tsarkakakke.”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 20

قَالَتۡ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞ وَلَمۡ أَكُ بَغِيّٗا

Ta ce: “Ta qaqa zan samu xa, alhalin kuwa wani namiji bai tava shafa ta ba, kuma ni ban zamanto mazinaciya ba?”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 21

قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞۖ وَلِنَجۡعَلَهُۥٓ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِ وَرَحۡمَةٗ مِّنَّاۚ وَكَانَ أَمۡرٗا مَّقۡضِيّٗا

(Mala’ika) ya ce: “Kamar haka ne Ubangijinki Ya faxa (cewa): “Shi (wannan) mai sauqi ne a wurina, kuma don Mu mayar da shi aya ga mutane da kuma rahama daga gare Mu, kuma (yin haka) ya zamanto al’amari ne tabbatacce (rubuce a Lauhul-Mahafuzu).”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 22

۞فَحَمَلَتۡهُ فَٱنتَبَذَتۡ بِهِۦ مَكَانٗا قَصِيّٗا

Sai ta xauki cikinsa sannan ta (tafi) da shi wani wuri mai nisa



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 23

فَأَجَآءَهَا ٱلۡمَخَاضُ إِلَىٰ جِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ قَالَتۡ يَٰلَيۡتَنِي مِتُّ قَبۡلَ هَٰذَا وَكُنتُ نَسۡيٗا مَّنسِيّٗا

Sai ciwon naquda ya tilasta mata zuwa ga kututturen dabino, ta ce: “Ina ma na mutu tun kafin wannan (abu ya faru), na kuma kasance yasasshiya, mantacciya!”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 24

فَنَادَىٰهَا مِن تَحۡتِهَآ أَلَّا تَحۡزَنِي قَدۡ جَعَلَ رَبُّكِ تَحۡتَكِ سَرِيّٗا

Sai ya kira ta daga qarqashinta[1] cewa: “Kada ki yi baqin ciki, haqiqa Ubangijinki Ya sanya qorama a qarqashinki


1- Watau Annabi Isa ().


Sourate: Suratu Maryam

Verset : 25

وَهُزِّيٓ إِلَيۡكِ بِجِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ تُسَٰقِطۡ عَلَيۡكِ رُطَبٗا جَنِيّٗا

“Ki kuma girgiza kututturen dabinon nan zai zubo miki da lubiyar dabino nunanniya



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 26

فَكُلِي وَٱشۡرَبِي وَقَرِّي عَيۡنٗاۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ ٱلۡبَشَرِ أَحَدٗا فَقُولِيٓ إِنِّي نَذَرۡتُ لِلرَّحۡمَٰنِ صَوۡمٗا فَلَنۡ أُكَلِّمَ ٱلۡيَوۡمَ إِنسِيّٗا

“Don haka ki ci, ki sha, kuma ki kwantar da hankalinki; kuma duk mutumin da kika gani (ya yi magana da ke), sai ki yi nuni da cewa: “Na xauki alqawari ga Allah na kame bakina, ba zan yi magana da wani mutum ba yau.”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 27

فَأَتَتۡ بِهِۦ قَوۡمَهَا تَحۡمِلُهُۥۖ قَالُواْ يَٰمَرۡيَمُ لَقَدۡ جِئۡتِ شَيۡـٔٗا فَرِيّٗا

Sai ta zo wa mutanenta da shi tana xauke da shi; suka ce: “Ya Maryamu, haqiqa kin zo da babban abu!



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 28

يَـٰٓأُخۡتَ هَٰرُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ ٱمۡرَأَ سَوۡءٖ وَمَا كَانَتۡ أُمُّكِ بَغِيّٗا

“Ya ke ‘yar’uwar Haruna[1], mahaifinki bai kasance lalataccen mutum ba, mahaifiyarki ma ba mazinaciya ba.”


1- Wani mutum ne mai ibada da kamun kai, ana ce masa Haruna. Wasu malaman sun ce xan’uwanta ne.


Sourate: Suratu Maryam

Verset : 29

فَأَشَارَتۡ إِلَيۡهِۖ قَالُواْ كَيۡفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِي ٱلۡمَهۡدِ صَبِيّٗا

Sai ta nuna shi; (sai) suka ce: “Ta qaqa za mu yi magana da wanda yake xan jariri cikin shimfixar jego?”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 30

قَالَ إِنِّي عَبۡدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِيَ ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلَنِي نَبِيّٗا

(Isa) ya ce (da su): “Lalle ni bawan Allah ne, Ya ba ni littafi Ya kuma sanya ni Annabi