Sourate: Suratul Baqara

Verset : 169

إِنَّمَا يَأۡمُرُكُم بِٱلسُّوٓءِ وَٱلۡفَحۡشَآءِ وَأَن تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

Yana umartar ku ne kawai da savo da ayyukan assha da kuma faxin abin da ba ku da ilimi game da shi ku jingina wa Allah



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 30

يَوۡمَ تَجِدُ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ مِنۡ خَيۡرٖ مُّحۡضَرٗا وَمَا عَمِلَتۡ مِن سُوٓءٖ تَوَدُّ لَوۡ أَنَّ بَيۡنَهَا وَبَيۡنَهُۥٓ أَمَدَۢا بَعِيدٗاۗ وَيُحَذِّرُكُمُ ٱللَّهُ نَفۡسَهُۥۗ وَٱللَّهُ رَءُوفُۢ بِٱلۡعِبَادِ

Ranar da kowane rai zai sami abin da ya aikata na alheri an halarto da shi, abin da kuwa ya aikata na mummunan aiki, zai so ina ma da a ce tsakaninsa da shi akwai wata tazara mai nisa. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kansa, kuma Allah Mai tausayi ne ga bayi



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 22

وَلَا تَنكِحُواْ مَا نَكَحَ ءَابَآؤُكُم مِّنَ ٱلنِّسَآءِ إِلَّا مَا قَدۡ سَلَفَۚ إِنَّهُۥ كَانَ فَٰحِشَةٗ وَمَقۡتٗا وَسَآءَ سَبِيلًا

Kuma kada ku auri wadda iyayenku maza suka aure ta cikin mata, sai fa abin da ya riga ya shuxe. Lalle yin hakan ya kasance alfasha ce kuma abu ne da zai jawo fushin Allah, kuma tafarki ne wanda ya yi muni



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 79

مَّآ أَصَابَكَ مِنۡ حَسَنَةٖ فَمِنَ ٱللَّهِۖ وَمَآ أَصَابَكَ مِن سَيِّئَةٖ فَمِن نَّفۡسِكَۚ وَأَرۡسَلۡنَٰكَ لِلنَّاسِ رَسُولٗاۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدٗا

Duk wani kyakkyawan abu da ya same ka, to daga Allah ne; duk kuma wani mummunan abu da ya same ka, to daga wajen ka ne[1]. Kuma Mun aiko ka Manzo ga mutane. Kuma Allah Ya isa Mai shaida (a kan haka)


1- Watau saboda laifukansa ne da zunubansa.


Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 84

فَقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا تُكَلَّفُ إِلَّا نَفۡسَكَۚ وَحَرِّضِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَكُفَّ بَأۡسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ وَٱللَّهُ أَشَدُّ بَأۡسٗا وَأَشَدُّ تَنكِيلٗا

To ka yi yaqi domin xaukaka kalmar Allah, ba a xora maka nauyin tilasta kowa ba sai kanka. Kuma ka zaburar da muminai; Allah zai dankwafe qarfin waxanda suka kafirta; kuma Allah Shi ne Mafi tsananin qarfi, kuma Mafi tsananin uquba



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 148

۞لَّا يُحِبُّ ٱللَّهُ ٱلۡجَهۡرَ بِٱلسُّوٓءِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ إِلَّا مَن ظُلِمَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعًا عَلِيمًا

Allah ba Ya son bayyana mummunan zance, sai dai wanda aka zalunce shi. Kuma Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai yawan sani



Sourate: Suratul An’am

Verset : 31

قَدۡ خَسِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِلِقَآءِ ٱللَّهِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَتۡهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةٗ قَالُواْ يَٰحَسۡرَتَنَا عَلَىٰ مَا فَرَّطۡنَا فِيهَا وَهُمۡ يَحۡمِلُونَ أَوۡزَارَهُمۡ عَلَىٰ ظُهُورِهِمۡۚ أَلَا سَآءَ مَا يَزِرُونَ

Haqiqa waxanda suka qaryata haxuwa da Allah sun yi hasara; har sai lokacin da alqiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, sai su ce: “Kaiconmu kan irin sakacin da muka yi a cikinta (duniya),” alhalin kuwa suna xauke da kayan laifukansu a bayansu. Ku saurara, abin da suka xauka na laifi ya munana matuqa



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 9

ٱشۡتَرَوۡاْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلٗا فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِهِۦٓۚ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Sun musanya ayoyin Allah da xan kuxi qanqani, sannan suka toshe hanyarsa. Lalle su dai abin da suke aikatawa ya munana



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 98

وَمِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مَن يَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ مَغۡرَمٗا وَيَتَرَبَّصُ بِكُمُ ٱلدَّوَآئِرَۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Daga mutanen qauye kuma akwai waxanda suke xaukar abin da suke ciyarwa tara ne, suke kuma jiran faruwar masifu gare ku. To mummunar musiba ta tabbata a kansu. Allah kuma Mai ji ne, Masani



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 11

۞وَلَوۡ يُعَجِّلُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ ٱلشَّرَّ ٱسۡتِعۡجَالَهُم بِٱلۡخَيۡرِ لَقُضِيَ إِلَيۡهِمۡ أَجَلُهُمۡۖ فَنَذَرُ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ

Da dai Allah zai gaggauta (karvar addu’ar) mutane ta sharri kamar yadda yake gaggauta ta alheri to da qarshen rayuwarsu ya zo. Sai dai Mukan bar waxanda ba sa tsammanin haxuwa da Mu cikin shisshiginsu su yi ta ximuwa



Sourate: Suratu Hud

Verset : 114

وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَيِ ٱلنَّهَارِ وَزُلَفٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَٰتِ يُذۡهِبۡنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ ذَٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّـٰكِرِينَ

Ka kuma tsai da salla farkon rana da qarshenta da kuma farkon dare. Lalle kyawawan (ayyuka) suna shafe munana. Wannan tunasarwa ne ga masu tunawa



Sourate: Suratu Yusuf 

Verset : 53

۞وَمَآ أُبَرِّئُ نَفۡسِيٓۚ إِنَّ ٱلنَّفۡسَ لَأَمَّارَةُۢ بِٱلسُّوٓءِ إِلَّا مَا رَحِمَ رَبِّيٓۚ إِنَّ رَبِّي غَفُورٞ رَّحِيمٞ

“Ba kuma wai ina wanke kaina ba ne. Babu shakka xabi’ar rai ce ta umarci mutum da yin mummunan abu, sai fa wanda Ubangijina Ya yi wa jin qai. Lalle Ubangijina Mai gafara ne Mai jin qai.”



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 26

وَمَثَلُ كَلِمَةٍ خَبِيثَةٖ كَشَجَرَةٍ خَبِيثَةٍ ٱجۡتُثَّتۡ مِن فَوۡقِ ٱلۡأَرۡضِ مَا لَهَا مِن قَرَارٖ

Misalin kuma mummunar kalma kamar mummunar bishiya ce da aka tumvuke daga kan qasa, ba ta da wata matabbata



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 25

لِيَحۡمِلُوٓاْ أَوۡزَارَهُمۡ كَامِلَةٗ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَمِنۡ أَوۡزَارِ ٱلَّذِينَ يُضِلُّونَهُم بِغَيۡرِ عِلۡمٍۗ أَلَا سَآءَ مَا يَزِرُونَ

(Wannan kuwa) don su xauki laifukansu cikakku ranar alqiyama, da kuma laifukan waxanda suke vatarwa ba da ilimi ba. Ku saurara, abin da suke xauka ya munana!



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 10

وَأَنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ أَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا

Waxanda kuwa ba su yi imani da ranar lahira ba lalle Mun tanadar musu azaba mai raxaxi



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 32

وَلَا تَقۡرَبُواْ ٱلزِّنَىٰٓۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَٰحِشَةٗ وَسَآءَ سَبِيلٗا

Kuma kada ku kusanci zina; lalle ita (zina) ta kasance mugun aiki ne, kuma hanya ce wadda ta munana



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 38

كُلُّ ذَٰلِكَ كَانَ سَيِّئُهُۥ عِندَ رَبِّكَ مَكۡرُوهٗا

Duk waxancan abubuwa mummunansu a wurin Ubangijinka abin qi ne



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 83

وَإِذَآ أَنۡعَمۡنَا عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ أَعۡرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ كَانَ يَـُٔوسٗا

Kuma idan Muka yi wa mutum ni’ima sai ya bijire ya kuma juya kwivinsa; idan kuwa sharri ne ya same shi sai ya zama mai yawan yanke qauna



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 35

كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَنَبۡلُوكُم بِٱلشَّرِّ وَٱلۡخَيۡرِ فِتۡنَةٗۖ وَإِلَيۡنَا تُرۡجَعُونَ

Kowanne rai zai xanxani mutuwa. Muna kuwa jarrabar ku da fitinar sharri da ta alheri, kuma gare Mu ne za a dawo da ku



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 96

ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ ٱلسَّيِّئَةَۚ نَحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَصِفُونَ

Ka ingije mummunan abu da wanda ya fi kyau. Mu ne Muka fi sanin abin da suke siffata (ka da shi)



Sourate: Suratur Rum

Verset : 36

وَإِذَآ أَذَقۡنَا ٱلنَّاسَ رَحۡمَةٗ فَرِحُواْ بِهَاۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ إِذَا هُمۡ يَقۡنَطُونَ

Idan kuma Muka xanxana wa mutane rahama sai su yi farin ciki da ita; idan kuwa wata masifa ta same su saboda abin da hannayensu suka gabatar sai ka gan su suna xebe qauna



Sourate: Suratu Faxir

Verset : 43

ٱسۡتِكۡبَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَكۡرَ ٱلسَّيِّيِٕۚ وَلَا يَحِيقُ ٱلۡمَكۡرُ ٱلسَّيِّئُ إِلَّا بِأَهۡلِهِۦۚ فَهَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا سُنَّتَ ٱلۡأَوَّلِينَۚ فَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ ٱللَّهِ تَبۡدِيلٗاۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ ٱللَّهِ تَحۡوِيلًا

Don girman kai a bayan qasa da kuma makirci mummuna. (Sakamakon) makirci mummuna kuwa ba ya sauka sai a kan masu shi. Ba abin da suke saurare in ban da sunnar da ta sami mutanen farko. Sannan ba za ka tava samun wani canji ba game da sunnar Allah; kuma ba za ka sami wani sauyi ba game da sunnar Allah



Sourate: Suratu Fussilat

Verset : 34

وَلَا تَسۡتَوِي ٱلۡحَسَنَةُ وَلَا ٱلسَّيِّئَةُۚ ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ فَإِذَا ٱلَّذِي بَيۡنَكَ وَبَيۡنَهُۥ عَدَٰوَةٞ كَأَنَّهُۥ وَلِيٌّ حَمِيمٞ

Kyakkyawan (abu) da mummuna ba za su zama xaya ba. To ka ture mummuna da abin da ya fi kyau, to sai ka ga wanda yake tsakaninsa da kai gaba ce, ya zamanto kamar wani masoyi ne na qut da qut



Sourate: Suratuz Zalzala

Verset : 8

وَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ شَرّٗا يَرَهُۥ

Wanda kuma duk ya yi aikin sharri daidai da zarra zai gan shi



Sourate: Suratul Falaq

Verset : 1

قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ

Ka ce: “Ina neman tsari da Ubangijin asuba



Sourate: Suratul Falaq

Verset : 2

مِن شَرِّ مَا خَلَقَ

“Daga sharrin abin da Ya halitta[1]


1- Watau duk wani mahluqi mai cutarwa, mutum ne ko aljani ko dabba.


Sourate: Suratul Falaq

Verset : 3

وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ

“Da kuma sharrin dare idan ya lulluve da duhu



Sourate: Suratul Falaq

Verset : 4

وَمِن شَرِّ ٱلنَّفَّـٰثَٰتِ فِي ٱلۡعُقَدِ

“Da kuma sharrin mata masu tofi a cikin qulle-qulle



Sourate: Suratul Falaq

Verset : 5

وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ

“Da kuma sharrin mai hassada yayin da ya yi hassadar.”



Sourate: Suratun Nas

Verset : 1

قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ

Ka ce: “Ina neman tsari da Ubangijin mutane