Sourate: Suratu Maryam

Verset : 48

وَأَعۡتَزِلُكُمۡ وَمَا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَأَدۡعُواْ رَبِّي عَسَىٰٓ أَلَّآ أَكُونَ بِدُعَآءِ رَبِّي شَقِيّٗا

“Zan kuwa qaurace muku ku da abin da kuke bauta wa wanda ba Allah ba, in kuma roqi Ubangijina, na kuma sa tsammanin cewa ba zan zama tavavve ba game da roqon Ubangijina.”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 49

فَلَمَّا ٱعۡتَزَلَهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۖ وَكُلّٗا جَعَلۡنَا نَبِيّٗا

To lokacin da ya qaurace musu tare da abin da suke bauta wa wanda ba Allah ba, sai Muka yi masa baiwa da Is’haqa da Ya’aqubu; kowannensu kuma Muka ba shi annabta



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 50

وَوَهَبۡنَا لَهُم مِّن رَّحۡمَتِنَا وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ لِسَانَ صِدۡقٍ عَلِيّٗا

Muka kuma yi musu baiwa da rahamarmu, kuma Muka sanya musu kyakkyawan ambato maxaukaki[1]


1- Watau ya sa suka zamanto ababen yabo mai xorewa a gun kowa.


Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 51

۞وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَآ إِبۡرَٰهِيمَ رُشۡدَهُۥ مِن قَبۡلُ وَكُنَّا بِهِۦ عَٰلِمِينَ

Haqiqa kuma Mun bai wa Ibrahimu shiriyarsa tun da farko, Mun kuma zamanto Muna sane da shi



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 52

إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَا هَٰذِهِ ٱلتَّمَاثِيلُ ٱلَّتِيٓ أَنتُمۡ لَهَا عَٰكِفُونَ

(Ka tuna) lokacin da ya ce da babansa da kuma jama’arsa: “Mene ne (amfanin) waxannan gumakan da kuka duqufa a bautar su?”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 53

قَالُواْ وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا لَهَا عَٰبِدِينَ

Suka ce: “Mun sami iyayenmu suna bauta musu ne.”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 54

قَالَ لَقَدۡ كُنتُمۡ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُمۡ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

(Ibrahimu) ya ce: “Haqiqa ku da iyayen naku kun tabbata a kan vata bayyananne.”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 55

قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا بِٱلۡحَقِّ أَمۡ أَنتَ مِنَ ٱللَّـٰعِبِينَ

Suka ce: “Yanzu ka zo mana da gaskiya ne ko kuwa kai ma kana cikin masu wasa (da mu) ne?”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 56

قَالَ بَل رَّبُّكُمۡ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ ٱلَّذِي فَطَرَهُنَّ وَأَنَا۠ عَلَىٰ ذَٰلِكُم مِّنَ ٱلشَّـٰهِدِينَ

(Ibrahimu) ya ce: “A’a, Ubangijinku dai (Shi ne) Ubangijin sammai da qasa, Wanda Ya halicce su, kuma ni ina daga masu shaida a kan wannan



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 57

وَتَٱللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصۡنَٰمَكُم بَعۡدَ أَن تُوَلُّواْ مُدۡبِرِينَ

“Na rantse da Allah tabbas zan shirya wa gumakanku kaidi bayan kun tafi kun ba da baya!



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 58

فَجَعَلَهُمۡ جُذَٰذًا إِلَّا كَبِيرٗا لَّهُمۡ لَعَلَّهُمۡ إِلَيۡهِ يَرۡجِعُونَ

Sai ya mayar da su guntu-guntu in ban da babbansu (da ya bari) don ko sa dawo masa (su tambaye shi)



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 59

قَالُواْ مَن فَعَلَ هَٰذَا بِـَٔالِهَتِنَآ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Suke ce: “Wane ne ya yi wa ababen bautarmu wannan (aika-aika)? Lallai shi yana daga azzalumai!”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 60

قَالُواْ سَمِعۡنَا فَتٗى يَذۡكُرُهُمۡ يُقَالُ لَهُۥٓ إِبۡرَٰهِيمُ

(Wasu daga cikinsu) suka ce: “Mun ji wani saurayi yana ambaton su, ana ce da shi Ibrahimu.”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 61

قَالُواْ فَأۡتُواْ بِهِۦ عَلَىٰٓ أَعۡيُنِ ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَشۡهَدُونَ

Suka ce: “(Ku je) ku zo da shi kan idon mutane don su shaidi (abin da ya aikata).”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 62

قَالُوٓاْ ءَأَنتَ فَعَلۡتَ هَٰذَا بِـَٔالِهَتِنَا يَـٰٓإِبۡرَٰهِيمُ

(Da aka kawo shi sai) suka ce: “Yanzu kai ka aikata wannan (irin aiki) ga ababen bautarmu, ya Ibrahimu?”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 63

قَالَ بَلۡ فَعَلَهُۥ كَبِيرُهُمۡ هَٰذَا فَسۡـَٔلُوهُمۡ إِن كَانُواْ يَنطِقُونَ

(Ibrahimu) ya ce: “A’a, wannan babban nasu (shi) ya aikata shi, sai ku tambaye su idan ya zamana suna magana.”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 64

فَرَجَعُوٓاْ إِلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ فَقَالُوٓاْ إِنَّكُمۡ أَنتُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Sai suka koma ga (zargin) kawunansu sannan suka ce: “Lallai ku dai ne azzalumai.”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 65

ثُمَّ نُكِسُواْ عَلَىٰ رُءُوسِهِمۡ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَا هَـٰٓؤُلَآءِ يَنطِقُونَ

Sannan aka juyo da kawunansu (zuwa kafirci) suka ce (da Ibrahimu): “Mun rantse haqiqa ka san cewa su waxannan ba sa magana.”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 66

قَالَ أَفَتَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا يَضُرُّكُمۡ

Ya ce: “To yanzu kwa riqa bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amfana muku komai ba kuma ba zai cuce ku ba?



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 67

أُفّٖ لَّكُمۡ وَلِمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

“Tir da ku, da kuma abin da kuke bauta wa wanda ba Allah ba. To yanzu ba kwa hankalta ba?”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 68

قَالُواْ حَرِّقُوهُ وَٱنصُرُوٓاْ ءَالِهَتَكُمۡ إِن كُنتُمۡ فَٰعِلِينَ

Sai suka ce: “Ku qone shi ku kuma taimaki allolinku in kun kasance masu aikata hakan.”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 69

قُلۡنَا يَٰنَارُ كُونِي بَرۡدٗا وَسَلَٰمًا عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ

(Da suka jefa shi cikin wutar sai) Muka ce: “Ke wuta, ki zama sassanya da kuma aminci ga Ibrahimu!”



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 70

وَأَرَادُواْ بِهِۦ كَيۡدٗا فَجَعَلۡنَٰهُمُ ٱلۡأَخۡسَرِينَ

Suka yi nufin shirya masa makirci sai Muka mayar da su tavavvu



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 71

وَنَجَّيۡنَٰهُ وَلُوطًا إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَا لِلۡعَٰلَمِينَ

Muka kuma tserar da shi, shi da Luxu zuwa ga qasar da Muka yi albarka a cikinta ga talikai (watau Sham)



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 72

وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ نَافِلَةٗۖ وَكُلّٗا جَعَلۡنَا صَٰلِحِينَ

Muka kuma ba shi Is’haqa da kuma Ya’aqubu qari (wato jika). Dukkanninsu kuma Mun sanya su salihai



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 73

وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَئِمَّةٗ يَهۡدُونَ بِأَمۡرِنَا وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِمۡ فِعۡلَ ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَإِقَامَ ٱلصَّلَوٰةِ وَإِيتَآءَ ٱلزَّكَوٰةِۖ وَكَانُواْ لَنَا عَٰبِدِينَ

Muka kuma sanya su shugabanni masu shiryarwa da umarninmu, Muka kuma yi musu wahayi na aikata alheri da tsai da salla da ba da zakka, sun kuwa zamanto masu bauta mana ne



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 26

وَإِذۡ بَوَّأۡنَا لِإِبۡرَٰهِيمَ مَكَانَ ٱلۡبَيۡتِ أَن لَّا تُشۡرِكۡ بِي شَيۡـٔٗا وَطَهِّرۡ بَيۡتِيَ لِلطَّآئِفِينَ وَٱلۡقَآئِمِينَ وَٱلرُّكَّعِ ٱلسُّجُودِ

Kuma (ka tuna) lokacin da Muka nuna wa Ibrahimu gurbin Xakin (Ka’aba, Muka ce da shi): “Kada ka haxa komai da Ni (wajen bauta), kuma ka tsarkake Xakina ga masu xawafi da masu zama a cikinsa da kuma masu ruku’i masu sujjada



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 27

وَأَذِّن فِي ٱلنَّاسِ بِٱلۡحَجِّ يَأۡتُوكَ رِجَالٗا وَعَلَىٰ كُلِّ ضَامِرٖ يَأۡتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٖ

Kuma ka yi shela cikin mutane saboda yin Hajji, za su zo maka matafiya a qasa da kuma kan kowanne raqumi mai xamammen ciki, za su zo maka daga kowane wuri mai nisa



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 78

وَجَٰهِدُواْ فِي ٱللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِۦۚ هُوَ ٱجۡتَبَىٰكُمۡ وَمَا جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلدِّينِ مِنۡ حَرَجٖۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمۡ إِبۡرَٰهِيمَۚ هُوَ سَمَّىٰكُمُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ مِن قَبۡلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ ٱلرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيۡكُمۡ وَتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِۚ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱعۡتَصِمُواْ بِٱللَّهِ هُوَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ فَنِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ

Kuma ku yi jihadi wajen (xaukaka addinin) Allah iyakar iyawarku. Shi ne Ya zave ku, bai kuma sanya muku wani qunci ba cikin addini. Addinin Babanku ne Ibrahimu. (Allah) Shi ne Ya kira ku Musulmi tuntuni, da kuma cikin wannan (Alqur’ani) don Manzo ya zama shaida a gare ku, ku kuma ku zama shaida ga (sauran) mutane. To sai ku tsai da salla kuma ku ba da zakka, ku kuma yi riqo da (addinin) Allah, Shi ne Majivincin al’amarinku; to madalla da Majivinci, kuma madalla da Mataimaki



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 69

وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ إِبۡرَٰهِيمَ

Kuma ka karanta musu labarin Ibrahimu?