Sourate: Suratul Baqara

Verset : 25

وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ كُلَّمَا رُزِقُواْ مِنۡهَا مِن ثَمَرَةٖ رِّزۡقٗا قَالُواْ هَٰذَا ٱلَّذِي رُزِقۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَأُتُواْ بِهِۦ مُتَشَٰبِهٗاۖ وَلَهُمۡ فِيهَآ أَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞۖ وَهُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Kuma ka yi albishir ga waxanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na qwarai cewa suna da wasu gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Duk sa’adda aka arzuta su da ’ya’yan itatuwa daga gare su sai su ce: “Wannan shi ne irin abin da aka arzuta mu da shi xazu.” An kawo musu shi yana mai kama da juna, kuma suna da wasu mata tsarkaka a cikinsu, kuma su masu zama ne a cikinsu dindindin



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 134

تِلۡكَ أُمَّةٞ قَدۡ خَلَتۡۖ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَلَكُم مَّا كَسَبۡتُمۡۖ وَلَا تُسۡـَٔلُونَ عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waccan al’umma ce da ta riga ta wuce; abin da ta aikata mallakarta ne, ku ma abin da kuka aikata naku ne, kuma ba za a tambaye ku ba game da abin da suka kasance suna aikatawa.”



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 141

تِلۡكَ أُمَّةٞ قَدۡ خَلَتۡۖ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَلَكُم مَّا كَسَبۡتُمۡۖ وَلَا تُسۡـَٔلُونَ عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waccan al’umma ce da ta riga ta wuce, abin da ta aikata mallakarta ne, ku ma abin da kuka aikata naku ne, kuma ba za a tambaye ku game da abin da suka kasance suna aikatawa ba.”



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 167

وَقَالَ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُواْ لَوۡ أَنَّ لَنَا كَرَّةٗ فَنَتَبَرَّأَ مِنۡهُمۡ كَمَا تَبَرَّءُواْ مِنَّاۗ كَذَٰلِكَ يُرِيهِمُ ٱللَّهُ أَعۡمَٰلَهُمۡ حَسَرَٰتٍ عَلَيۡهِمۡۖ وَمَا هُم بِخَٰرِجِينَ مِنَ ٱلنَّارِ

Kuma waxanda suka yi biyayya suka ce: “Ina ma dai muna da wata dama ta komawa (duniya) don mu ma mu nisantar da kanmu daga gare su, kamar yadda suka nisanta kansu daga gare mu?” Kamar haka ne Allah Yake nuna musu ayyukansu suka zama nadama a gare su, kuma su ba masu samun fita ne daga wuta ba



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 123

لَّيۡسَ بِأَمَانِيِّكُمۡ وَلَآ أَمَانِيِّ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِۗ مَن يَعۡمَلۡ سُوٓءٗا يُجۡزَ بِهِۦ وَلَا يَجِدۡ لَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا

(Al’amarin) ba wai ya dangaci burace-buracenku ba ne, ba kuma burace-buracen Ma’abota Littafi ba ne. Duk wanda ya aikata mummunan aiki, to za a saka masa da shi, kuma ba zai sami wani masoyi ko mai taimako ba Allah ba



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 124

وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ مِن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ نَقِيرٗا

Kuma wanda ya yi wani aiki nagari, namiji ne ko mace, alhali yana mumini, to waxannan za su shiga Aljanna, kuma ba za a zalunce su gwargwadon xigon bayan qwallon dabino ba



Sourate: Suratul Ma’ida

Verset : 9

وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٌ عَظِيمٞ

Allah Ya yi alqawari ga waxanda suka yi imani, kuma suka yi aiki nagari, suna da gafara da kuma lada mai girma



Sourate: Suratul Ma’ida

Verset : 33

إِنَّمَا جَزَـٰٓؤُاْ ٱلَّذِينَ يُحَارِبُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَسۡعَوۡنَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوٓاْ أَوۡ يُصَلَّبُوٓاْ أَوۡ تُقَطَّعَ أَيۡدِيهِمۡ وَأَرۡجُلُهُم مِّنۡ خِلَٰفٍ أَوۡ يُنفَوۡاْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِۚ ذَٰلِكَ لَهُمۡ خِزۡيٞ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ

Lalle sakamakon waxanda suke yaqar Allah da Manzonsa, kuma suke varna a bayan qasa[1], shi ne kawai a karkashe su ko kuma a giggicciye su ko kuma a yayyanke hannayensu da qafafuwansu a tarnaqe ko kuma a kore su daga qasa. Wannan qasqanci ne a gare su a nan duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma


1- Ana nufin duk wasu masu ta’addanci da aikata fashi da makami, wannan shi ne hukuncinsu.


Sourate: Suratul An’am

Verset : 132

وَلِكُلّٖ دَرَجَٰتٞ مِّمَّا عَمِلُواْۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَٰفِلٍ عَمَّا يَعۡمَلُونَ

Kuma kowanne yana da nasa matsayi game da abin da suka aikata, kuma Ubangijinka bai zama Mai rafkana ba dangane da abin da suke aikatawa



Sourate: Suratul An’am

Verset : 160

مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ عَشۡرُ أَمۡثَالِهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَىٰٓ إِلَّا مِثۡلَهَا وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Wanda ya zo da kyakkyawan aiki xaya, to yana da ninkin ladansa goma; wanda kuwa ya zo da mummuna xaya, to ba za a saka masa ba sai daidai da shi, ba kuma za a zalunce su ba



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 43

وَنَزَعۡنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنۡ غِلّٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَقَالُواْ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي هَدَىٰنَا لِهَٰذَا وَمَا كُنَّا لِنَهۡتَدِيَ لَوۡلَآ أَنۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُۖ لَقَدۡ جَآءَتۡ رُسُلُ رَبِّنَا بِٱلۡحَقِّۖ وَنُودُوٓاْ أَن تِلۡكُمُ ٱلۡجَنَّةُ أُورِثۡتُمُوهَا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Muka kuma cire abin da yake cikin qirazansu na qullata, qoramu suna gudana ta qarqashinsu; kuma za su ce: “Yabo ya tabbata ga Allah da Ya shiryar da mu ga wannan, kuma da ba za mu tava shiryuwa ba ba don Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle haqiqa manzannin Ubangijinmu sun zo da gaskiya.” Sai a kira su da cewa: “Waccan Aljannar an gadar muku da ita saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.”



Sourate: Suratu Hud

Verset : 15

مَن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيۡهِمۡ أَعۡمَٰلَهُمۡ فِيهَا وَهُمۡ فِيهَا لَا يُبۡخَسُونَ

Waxanda suke nufin rayuwar duniya da qawace-qawacenta, to za Mu ba su cikakken sakamakon ayyukansu a cikinta, kuma ba za a tauye musu (komai ba)



Sourate: Suratu Hud

Verset : 16

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَيۡسَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا ٱلنَّارُۖ وَحَبِطَ مَا صَنَعُواْ فِيهَا وَبَٰطِلٞ مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waxannan su ne waxanda ba su da komai a lahira sai wuta; kuma abin da suka aikata a cikinta (duniyar) ya rushe, kuma abin da suke aikatawa ya lalace



Sourate: Suratu Hud

Verset : 111

وَإِنَّ كُلّٗا لَّمَّا لَيُوَفِّيَنَّهُمۡ رَبُّكَ أَعۡمَٰلَهُمۡۚ إِنَّهُۥ بِمَا يَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Kuma lalle kowannensu tabbas sai Ubangijinka Ya cika musu sakamakon ayyukansu. Lalle Shi Masanin abin da suke aikatawa ne



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 93

وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَلَتُسۡـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Da kuwa Allah Ya ga dama da Ya sanya ku al’umma xaya (masu addini xaya), sai dai kuma Yana vatar da wanda Ya ga dama Yana kuma shiryar da wanda Ya ga dama. Kuma tabbas za a tambaye ku game da abin da kuka kasance kuna aikatawa



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 97

مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Wanda ya yi kyakkyawan aiki namiji ko mace alhali shi yana mumini, to lalle za Mu raya shi rayuwa mai daxi, kuma za Mu saka musu ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 19

وَمَنۡ أَرَادَ ٱلۡأٓخِرَةَ وَسَعَىٰ لَهَا سَعۡيَهَا وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَـٰٓئِكَ كَانَ سَعۡيُهُم مَّشۡكُورٗا

Wanda kuma ya nufi lahira ya kuma yi aiki irin nata dominta alhalin yana mumini, to waxannan aikinsu ya zamanto abin godewa ne (a wurin Allah)



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 30

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجۡرَ مَنۡ أَحۡسَنَ عَمَلًا

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari tabbas Mu ba ma tozarta ladan wanda ya kyautata aiki



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 31

أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَيَلۡبَسُونَ ثِيَابًا خُضۡرٗا مِّن سُندُسٖ وَإِسۡتَبۡرَقٖ مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِۚ نِعۡمَ ٱلثَّوَابُ وَحَسُنَتۡ مُرۡتَفَقٗا

Waxannan suna da gidajen Aljanna na dawwama waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, ana yi musu ado a cikinsu (watau gidajen) da awarwaro na zinare, suna kuma sanya tufafi koraye na alharini mai shara-shara da mai kauri, suna kwance a kan gadaje. Madalla (da wannan) lada, wurin hutu kuma ya kyautata



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 49

وَوُضِعَ ٱلۡكِتَٰبُ فَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُشۡفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَٰوَيۡلَتَنَا مَالِ هَٰذَا ٱلۡكِتَٰبِ لَا يُغَادِرُ صَغِيرَةٗ وَلَا كَبِيرَةً إِلَّآ أَحۡصَىٰهَاۚ وَوَجَدُواْ مَا عَمِلُواْ حَاضِرٗاۗ وَلَا يَظۡلِمُ رَبُّكَ أَحَدٗا

Aka kuma ajiye littafin (ayyukansu), sannan sai ka ga masu laifi suna cike da tsoron abin da yake cikinsa, suna kuma cewa: “Kaiconmu, me ya sami wannan littafin, ba ya barin (aiki) qarami balle babba sai ya qididdige su. Suka kuma sami (duk) abubuwan da suka aikata an zo da su. Ubangijinka kuwa ba zai zalunci kowa ba



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 103

قُلۡ هَلۡ نُنَبِّئُكُم بِٱلۡأَخۡسَرِينَ أَعۡمَٰلًا

Ka ce (da su): “Ba na ba ku labarin waxanda suka fi asarar ayyukansu ba?



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 104

ٱلَّذِينَ ضَلَّ سَعۡيُهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّهُمۡ يُحۡسِنُونَ صُنۡعًا

“(Su ne) waxanda aikinsu ya vace a rayuwarsu ta duniya alhali kuwa su suna tsammanin suna kyautata aiki ne.”



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 105

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ وَلِقَآئِهِۦ فَحَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فَلَا نُقِيمُ لَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَزۡنٗا

Waxannan (su ne) waxanda suka kafirce wa ayoyin Ubangijinsu da kuma gamuwa da shi, sai ayyukansu suka lalace, ba za Mu sanya musu wani ma’auni ba a ranar alqiyama



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 106

ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُمۡ جَهَنَّمُ بِمَا كَفَرُواْ وَٱتَّخَذُوٓاْ ءَايَٰتِي وَرُسُلِي هُزُوًا

Wannan shi ne sakamakonsu, Jahannama, saboda kafircewa da suka yi suka kuma riqi ayoyina da manzannina abin yi wa izgili



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 107

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ كَانَتۡ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ ٱلۡفِرۡدَوۡسِ نُزُلًا

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari to Aljannar Firdausi[1] ita ce ta kasance masaukinsu


1- Aljannar Firdausi ita ce qololuwar Aljanna mafi daraja.


Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 108

خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يَبۡغُونَ عَنۡهَا حِوَلٗا

Suna masu dawwama a cikinta, ba sa neman wani musaya da ita



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 15

إِنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٌ أَكَادُ أُخۡفِيهَا لِتُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا تَسۡعَىٰ

“Lalle alqiyama za ta zo, ina nufin voye ta ne don a saka wa kowanne rai da irin abin da yake aikatawa



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 74

إِنَّهُۥ مَن يَأۡتِ رَبَّهُۥ مُجۡرِمٗا فَإِنَّ لَهُۥ جَهَنَّمَ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحۡيَىٰ

Lalle duk wanda ya zo wa Ubangijinsa yana mai babban laifi[1] to lalle yana da (sakamakon) Jahannama, ba zai mutu a cikinta ba, ba kuma zai rayu ba (rayuwa mai daxi)


1- Watau kafirce wa Allah da haxa wani da shi a wajen bauta.


Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 75

وَمَن يَأۡتِهِۦ مُؤۡمِنٗا قَدۡ عَمِلَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلدَّرَجَٰتُ ٱلۡعُلَىٰ

Wanda kuwa ya zo masa yana mumini ya zamana ya yi aiki na gari, to waxannan suna da (sakamakon samun) darajoji maxaukaka



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 94

فَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا كُفۡرَانَ لِسَعۡيِهِۦ وَإِنَّا لَهُۥ كَٰتِبُونَ

To duk wanda ya aikata kyawawan ayyuka alhali kuwa shi mumini ne, to babu musantawa ga aikinsa[1], lallai kuma Mu Masu rubuta masa shi ne


1- Watau ba za a yi masa runton aikinsa mai kyau ba, za a yi masa kyakkyawar sakayya ne a kai.