Sourate: Suratul Jasiya

Verset : 29

هَٰذَا كِتَٰبُنَا يَنطِقُ عَلَيۡكُم بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّا كُنَّا نَسۡتَنسِخُ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

(Za a ce da su): “Wannan Littafinmu ne da yake yi muku furuci da gaskiya[1]. Lalle Mu mun kasance Muna rubuta abin da kuka kasance kuna aikatawa[2].”


1- Watau littafin da mala’iku suka rubuta na ayyukansu yana ba da shaida a kansu da tsantsar gaskiya.


2- Domin Allah ne da kansa ya umarci waxannan mala’ikun su riqa rubuta ayyukan mutane a duniya.


Sourate: Suratul Ahqaf 

Verset : 19

وَلِكُلّٖ دَرَجَٰتٞ مِّمَّا عَمِلُواْۖ وَلِيُوَفِّيَهُمۡ أَعۡمَٰلَهُمۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Kuma kowane yana da darajoji (na sakamakon) abin da suka aikata; don kuma tabbas zai cika musu sakamakon ayyukansu, ba kuma za a zalunce su ba



Sourate: Suratu Muhammad

Verset : 1

ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ أَضَلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ

Waxanda suka kafirta suka kuma toshe hanyar Allah, to (Allah) Ya lalata ayyukansu[1]


1- Watau ba za su sami lada ba a kan ayyuka na qwarai da suka yi. Hakanan ayyukansu da suke yi na qoqarin rushe Musulunci haqansu ba zai cimma ruwa ba.


Sourate: Suratu Muhammad

Verset : 2

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَءَامَنُواْ بِمَا نُزِّلَ عَلَىٰ مُحَمَّدٖ وَهُوَ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّهِمۡ كَفَّرَ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَأَصۡلَحَ بَالَهُمۡ

Waxanda kuwa suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, kuma suka gaskata abin da aka saukar wa Muhammadu alhali kuwa shi ne gaskiya daga Ubangijinsu, sai (Allah) Ya kankare musu munanan ayyukansu, Ya kuma gyara musu halayensu



Sourate: Suratun Najm

Verset : 39

وَأَن لَّيۡسَ لِلۡإِنسَٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ

“Kuma mutum bai mallaki wani sakamako ba sai na abin da ya aikata



Sourate: Suratun Najm

Verset : 40

وَأَنَّ سَعۡيَهُۥ سَوۡفَ يُرَىٰ

“Kuma lalle aikin nasa ba da daxewa ba za a gan shi



Sourate: Suratus Saff 

Verset : 2

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفۡعَلُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, don me kuke faxar abin da ba kwa aikatawa?



Sourate: Suratus Saff 

Verset : 3

كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ أَن تَقُولُواْ مَا لَا تَفۡعَلُونَ

Ya isa babban abin qi a wurin Allah, ku riqa faxin abin da ba kwa aikatawa



Sourate: Suratut Taghabun

Verset : 7

زَعَمَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَن لَّن يُبۡعَثُواْۚ قُلۡ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتُبۡعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلۡتُمۡۚ وَذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ

Waxanda suka kafirta sun riya cewa ba za a tashe su ba har abada. Ka ce: “A’a, na rantse da Ubangijina tabbas za a tashe ku, sannan kuma tabbas za a ba ku labarin abin da kuka aikata. Wannan kuwa mai sauqi ne a wurin Allah



Sourate: Suratul Mulk

Verset : 2

ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡمَوۡتَ وَٱلۡحَيَوٰةَ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفُورُ

Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku (Ya bayyana) wane ne a cikinku ya fi kyakkyawan aiki? Shi kuma Mabuwayi ne, Mai gafara



Sourate: Suratul Lail

Verset : 4

إِنَّ سَعۡيَكُمۡ لَشَتَّىٰ

Lalle aikinku ya sha bamban



Sourate: Suratuz Zalzala

Verset : 7

فَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَيۡرٗا يَرَهُۥ

To duk wanda ya yi aikin alheri daidai da zarra zai gan shi



Sourate: Suratuz Zalzala

Verset : 8

وَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ شَرّٗا يَرَهُۥ

Wanda kuma duk ya yi aikin sharri daidai da zarra zai gan shi