Sourate: Suratul Fatiha

Verset : 4

مَٰلِكِ يَوۡمِ ٱلدِّينِ

Mamallakin ranar sakamako



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 48

وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا لَّا تَجۡزِي نَفۡسٌ عَن نَّفۡسٖ شَيۡـٔٗا وَلَا يُقۡبَلُ مِنۡهَا شَفَٰعَةٞ وَلَا يُؤۡخَذُ مِنۡهَا عَدۡلٞ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ

Kuma ku kiyayi wata rana da babu wani (mai) rai da zai isar wa da wani (mai) rai komai a cikinta; kuma ba za a karvi wani ceto daga gare shi ba, kuma ba za a karvi wata fansa daga gare shi ba, kuma ba za a taimaka musu ba



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 113

وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ لَيۡسَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَقَالَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ لَيۡسَتِ ٱلۡيَهُودُ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَهُمۡ يَتۡلُونَ ٱلۡكِتَٰبَۗ كَذَٰلِكَ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ مِثۡلَ قَوۡلِهِمۡۚ فَٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Yahudawa suka ce: “Nasara ba a kan komai suke ba”, su ma Nasara suka ce: “Yahudawa ba a kan komai suke ba”, alhalin dukkansu suna karanta Littafi. Kamar haka ne waxanda ba su da ilimi suka yi irin maganarsu. Kuma Allah zai yi hukunci a tsakaninsu ranar Alqiyama a kan abin da suka kasance suna savani a cikinsa



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 123

وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا لَّا تَجۡزِي نَفۡسٌ عَن نَّفۡسٖ شَيۡـٔٗا وَلَا يُقۡبَلُ مِنۡهَا عَدۡلٞ وَلَا تَنفَعُهَا شَفَٰعَةٞ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ

Kuma ku kiyayi wani yini da wani rai ba zai isar wa da wani rai komai ba, kuma ba za a karvi wata fansa daga gare shi ba, kuma ceto ba zai amfane shi ba, kuma su ba za a taimaka musu ba



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 281

وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا تُرۡجَعُونَ فِيهِ إِلَى ٱللَّهِۖ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Kuma ku kiyayi wani yini da za a mayar da ku zuwa ga Allah a cikinsa, sannan kowane rai za a cika masa abin da ya aiwatar na aiki, kuma su ba za a zalunce su ba



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 9

رَبَّنَآ إِنَّكَ جَامِعُ ٱلنَّاسِ لِيَوۡمٖ لَّا رَيۡبَ فِيهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ

“Ya Ubangijinmu, lalle Kai ne Mai tattara mutane a yinin da babu kokwanto a cikinsa. Lalle Allah ba Ya sava alqawari.”



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 30

يَوۡمَ تَجِدُ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ مِنۡ خَيۡرٖ مُّحۡضَرٗا وَمَا عَمِلَتۡ مِن سُوٓءٖ تَوَدُّ لَوۡ أَنَّ بَيۡنَهَا وَبَيۡنَهُۥٓ أَمَدَۢا بَعِيدٗاۗ وَيُحَذِّرُكُمُ ٱللَّهُ نَفۡسَهُۥۗ وَٱللَّهُ رَءُوفُۢ بِٱلۡعِبَادِ

Ranar da kowane rai zai sami abin da ya aikata na alheri an halarto da shi, abin da kuwa ya aikata na mummunan aiki, zai so ina ma da a ce tsakaninsa da shi akwai wata tazara mai nisa. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kansa, kuma Allah Mai tausayi ne ga bayi



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 185

كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوۡنَ أُجُورَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ فَمَن زُحۡزِحَ عَنِ ٱلنَّارِ وَأُدۡخِلَ ٱلۡجَنَّةَ فَقَدۡ فَازَۗ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ

Kowane rai zai xanxani mutuwa. Kuma a ranar alqiyama ne za a cika muku ladan ayyukanku; to duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to haqiqa ya rabauta. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daxi mai ruxarwa



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 87

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ لَيَجۡمَعَنَّكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِۗ وَمَنۡ أَصۡدَقُ مِنَ ٱللَّهِ حَدِيثٗا

Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Lalle zai tattara ku a ranar alqiyama, wadda babu kokwanto a cikinsa. Kuma wane ne ya fi Allah gaskiyar zance?



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 141

ٱلَّذِينَ يَتَرَبَّصُونَ بِكُمۡ فَإِن كَانَ لَكُمۡ فَتۡحٞ مِّنَ ٱللَّهِ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَكُن مَّعَكُمۡ وَإِن كَانَ لِلۡكَٰفِرِينَ نَصِيبٞ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَسۡتَحۡوِذۡ عَلَيۡكُمۡ وَنَمۡنَعۡكُم مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ فَٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَلَن يَجۡعَلَ ٱللَّهُ لِلۡكَٰفِرِينَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ سَبِيلًا

Su ne waxanda suke fakon ku, idan kun sami wata nasara daga Allah sai su ce: “Shin ashe ba tare da ku muke ba?” Kuma idan kafirai ne suka samu wata nasara, sai su ce: “Ashe ba mu muka sami dama a kanku ba (amma muka qyale ku), kuma muka kare ku daga muminai?” To lalle Allah zai yi hukunci a tsakaninku ranar alqiyama, kuma Allah ba zai tava ba wa kafirai wata dama ba a kan muminai[1]


1- Watau ba zai tava ba su nasara a kan muminai gaba xaya ba, sai dai ta wani wuri ban da wani wuri. Hakanan a lahira ba zai ba su hujjar da za su rinjayi muminai da ita ba.


Sourate: Suratu Yunus

Verset : 28

وَيَوۡمَ نَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ مَكَانَكُمۡ أَنتُمۡ وَشُرَكَآؤُكُمۡۚ فَزَيَّلۡنَا بَيۡنَهُمۡۖ وَقَالَ شُرَكَآؤُهُم مَّا كُنتُمۡ إِيَّانَا تَعۡبُدُونَ

(Ka tuna) ranar da za mu tara su ga baki xaya, sannan mu ce da waxanda suka yi shirka: “Ku tsaya cak a wurarenku ku da abokan tarayyarku”. Sai kuma mu raba tsakaninsu; sai abokan tarayyarsu kuma su ce: “Ba mu ne kuka kasance kuna bauta wa ba



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 29

فَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ إِن كُنَّا عَنۡ عِبَادَتِكُمۡ لَغَٰفِلِينَ

“To kuma Allah Ya isa shaida tsakaninmu da ku: mu kam lalle mun kasance ba mu ma san kuna bautar mu ba.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 30

هُنَالِكَ تَبۡلُواْ كُلُّ نَفۡسٖ مَّآ أَسۡلَفَتۡۚ وَرُدُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ مَوۡلَىٰهُمُ ٱلۡحَقِّۖ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

A can ne kowane rai zai samu sakamakon abin da ya gabatar (a duniya). An kuma mayar da su zuwa ga Allah Majivincinsu na gaskiya; abin da kuma suka kasance suna qirqira ya vace musu



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 93

وَلَقَدۡ بَوَّأۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ مُبَوَّأَ صِدۡقٖ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ فَمَا ٱخۡتَلَفُواْ حَتَّىٰ جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقۡضِي بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Haqiqa Mun sanya Banu Isra’ila a kyakkyawan matsayi na gaskiya, Muka kuma arzuta su da abubuwa daxaxa na halal, to kawunansu ba su tashi rabuwa ba har sai lokacin da ilimi ya zo musu. Lalle Ubangijinka zai yi hukunci tsakaninsu ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna savani a kansa



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 44

وَأَنذِرِ ٱلنَّاسَ يَوۡمَ يَأۡتِيهِمُ ٱلۡعَذَابُ فَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ رَبَّنَآ أَخِّرۡنَآ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖ نُّجِبۡ دَعۡوَتَكَ وَنَتَّبِعِ ٱلرُّسُلَۗ أَوَلَمۡ تَكُونُوٓاْ أَقۡسَمۡتُم مِّن قَبۡلُ مَا لَكُم مِّن زَوَالٖ

Kuma ka gargaxi mutane game da ranar da azaba za ta zo musu, sai waxanda suka yi kafirci su ce: “Ya Ubangijinmu, Ka saurara mana zuwa xan lokaci qanqani, za mu amsa kiranka kuma mu bi manzanni.” (Sai a ce da su): “A da ba ku ne kuka yi rantsuwa ba cewa ba za ku gushe ba?



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 47

فَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ مُخۡلِفَ وَعۡدِهِۦ رُسُلَهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٖ

To kada ka yi tsammanin Allah Mai sava wa manzanninsa alqawarinsa ne. Lalle Allah Mabuwayi ne Ma’abocin uquba



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 48

يَوۡمَ تُبَدَّلُ ٱلۡأَرۡضُ غَيۡرَ ٱلۡأَرۡضِ وَٱلسَّمَٰوَٰتُۖ وَبَرَزُواْ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ

(Ka tuna) ranar da za a sake qasa ba (wannan) qasar ba, da kuma sammai (ba waxannan samman ba. Halittu) kuma suka fito (daga cikin qasa) a gaban Allah Makaxaici, Mai rinjaye



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 49

وَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ يَوۡمَئِذٖ مُّقَرَّنِينَ فِي ٱلۡأَصۡفَادِ

Kuma za ka ga masu laifi a wannan ranar a ququmce cikin maruruwa



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 50

سَرَابِيلُهُم مِّن قَطِرَانٖ وَتَغۡشَىٰ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ

Rigunansu na (tafasasshen) man qaxiran ne[1], kuma wuta za ta lulluve fuskokinsu


1- Qaxiran, wani baqin mai ne kamar kwalta, mai saurin kamawa da wuta, mai kuma xan karen wari.


Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 51

لِيَجۡزِيَ ٱللَّهُ كُلَّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

(An yi musu haka ne) don Allah Ya saka wa kowanne rai da gwargwadon abin da ya aikata. Lalle Allah Mai saurin hisabi ne



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 111

۞يَوۡمَ تَأۡتِي كُلُّ نَفۡسٖ تُجَٰدِلُ عَن نَّفۡسِهَا وَتُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Ranar da kowanne rai zai zo yana kare kansa, kuma a cika wa kowanne rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 13

وَكُلَّ إِنسَٰنٍ أَلۡزَمۡنَٰهُ طَـٰٓئِرَهُۥ فِي عُنُقِهِۦۖ وَنُخۡرِجُ لَهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ كِتَٰبٗا يَلۡقَىٰهُ مَنشُورًا

Kuma kowane mutum Mun xaura masa littafin aikinsa a wuyansa, za kuma Mu fito masa da wani littafi a ranar alqiyama da zai same shi a buxe



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 14

ٱقۡرَأۡ كِتَٰبَكَ كَفَىٰ بِنَفۡسِكَ ٱلۡيَوۡمَ عَلَيۡكَ حَسِيبٗا

(A ce da shi): “Karanta littafinka; a yau ka isa ka yi wa kanka hukunci da kanka.”



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 37

فَٱخۡتَلَفَ ٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَيۡنِهِمۡۖ فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن مَّشۡهَدِ يَوۡمٍ عَظِيمٍ

Sai qungiyoyin suka sassava a tsakaninsu; to bone ya tabbata ga waxanda suka kafirta daga halartar rana mai girma (ita ce alqiyama)



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 38

أَسۡمِعۡ بِهِمۡ وَأَبۡصِرۡ يَوۡمَ يَأۡتُونَنَا لَٰكِنِ ٱلظَّـٰلِمُونَ ٱلۡيَوۡمَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

Ka yi mamakin jinsu da ganinsu a ranar da za su zo mana; sai dai azzalumai a wannan rana suna cikin vata mabayyani



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 39

وَأَنذِرۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡحَسۡرَةِ إِذۡ قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ وَهُمۡ فِي غَفۡلَةٖ وَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Ka kuma gargaxe su game da ranar nadama, lokacin da aka qare hisabi, alhali kuwa su (a duniya) suna cikin rafkana kuma su ba sa yin imani



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 40

إِنَّا نَحۡنُ نَرِثُ ٱلۡأَرۡضَ وَمَنۡ عَلَيۡهَا وَإِلَيۡنَا يُرۡجَعُونَ

Lalle Mu ne za Mu gaje qasa da wanda yake bayanta kuma gare Mu ne za a komar da su



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 85

يَوۡمَ نَحۡشُرُ ٱلۡمُتَّقِينَ إِلَى ٱلرَّحۡمَٰنِ وَفۡدٗا

Ranar da za Mu tayar da masu taqawa zuwa ga (Allah) Mai rahama a matsayin manyan baqi



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 86

وَنَسُوقُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ إِلَىٰ جَهَنَّمَ وِرۡدٗا

Mu kuma kora kafirai zuwa Jahannama cikin tsananin qishirwa



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 87

لَّا يَمۡلِكُونَ ٱلشَّفَٰعَةَ إِلَّا مَنِ ٱتَّخَذَ عِندَ ٱلرَّحۡمَٰنِ عَهۡدٗا

Ba wani mai ikon yin ceto sai wanda yake da alqawari a wurin (Allah) Mai rahama[1]


1- Watau ya riqe alqawarin da ya yi na imani da Allah da manzanninsa.