Sourate: Suratul Ma’ida

Verset : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَوۡفُواْ بِٱلۡعُقُودِۚ أُحِلَّتۡ لَكُم بَهِيمَةُ ٱلۡأَنۡعَٰمِ إِلَّا مَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ غَيۡرَ مُحِلِّي ٱلصَّيۡدِ وَأَنتُمۡ حُرُمٌۗ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ مَا يُرِيدُ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku cika alqawura. An halatta muku dabbobin ni’ima, sai dai abin da ake karanta muku (haramcinsa), ba kuna masu halatta farauta ba alhalin kuna cikin Harami, lalle Allah Yana hukunta abin da Yake nufi



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 34

وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ بِٱلۡعَهۡدِۖ إِنَّ ٱلۡعَهۡدَ كَانَ مَسۡـُٔولٗا

Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai dai ta (hanya) wadda take mafi kyau[1], har sai ya kawo qarfi. Kuma ku cika alqawari; lalle alqawari ya kasance abin tambaya ne (a lahira)


1- Watau ta hanyar yi masa kasuwanci da ita.


Sourate: Suratu Maryam

Verset : 52

وَنَٰدَيۡنَٰهُ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ ٱلۡأَيۡمَنِ وَقَرَّبۡنَٰهُ نَجِيّٗا

Muka kuma kira shi a gefen dutsen Xuri na dama, Muka kuma kusanto shi yana mai ganawa (da Mu)



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 8

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ

Kuma waxanda suke masu kiyaye amanarsu da kuma alqawarinsu



Sourate: Suratul Ahzab

Verset : 23

مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ رِجَالٞ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيۡهِۖ فَمِنۡهُم مَّن قَضَىٰ نَحۡبَهُۥ وَمِنۡهُم مَّن يَنتَظِرُۖ وَمَا بَدَّلُواْ تَبۡدِيلٗا

Akwai wasu mazaje daga muminai da suka cika abin da suka yi wa Allah alqawari da shi; akwai daga cikinsu wanda ya haxu da ajalinsa, akwai kuma daga cikinsu wanda yake sauraron (ajalin); kuma ba su yi kowace irin savawa ba (game da alqawarin)



Sourate: Suratul Ahzab

Verset : 24

لِّيَجۡزِيَ ٱللَّهُ ٱلصَّـٰدِقِينَ بِصِدۡقِهِمۡ وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ إِن شَآءَ أَوۡ يَتُوبَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Don Allah Ya saka wa masu gaskiya a kan gaskiyarsu, Ya kuma azabtar da munafukai idan Ya ga dama, ko kuma Ya karvi tubarsu. Lalle Allah Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai



Sourate: Suratul Fat’h

Verset : 10

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُبَايِعُونَكَ إِنَّمَا يُبَايِعُونَ ٱللَّهَ يَدُ ٱللَّهِ فَوۡقَ أَيۡدِيهِمۡۚ فَمَن نَّكَثَ فَإِنَّمَا يَنكُثُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَوۡفَىٰ بِمَا عَٰهَدَ عَلَيۡهُ ٱللَّهَ فَسَيُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا

Lalle waxanda suka yi maka mubaya’a[1] Allah kawai suke yi wa mubaya’a, Hannun Allah yana saman hannayensu. To duk wanda ya warware, to kansa kawai ya warware wa, wanda kuwa ya cika abin da ya yi wa Allah alqawarinsa, to ba da daxewa ba za Mu ba shi lada mai girma


1- Su ne sahabbai dubu da xari huxu da suka yi wa Annabi () mubaya’ar yaqi a Hudaibiyya, watau Bai’atur Ridhwan.


Sourate: Suratul Mumtahana

Verset : 10

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا جَآءَكُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ مُهَٰجِرَٰتٖ فَٱمۡتَحِنُوهُنَّۖ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِإِيمَٰنِهِنَّۖ فَإِنۡ عَلِمۡتُمُوهُنَّ مُؤۡمِنَٰتٖ فَلَا تَرۡجِعُوهُنَّ إِلَى ٱلۡكُفَّارِۖ لَا هُنَّ حِلّٞ لَّهُمۡ وَلَا هُمۡ يَحِلُّونَ لَهُنَّۖ وَءَاتُوهُم مَّآ أَنفَقُواْۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ أَن تَنكِحُوهُنَّ إِذَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّۚ وَلَا تُمۡسِكُواْ بِعِصَمِ ٱلۡكَوَافِرِ وَسۡـَٔلُواْ مَآ أَنفَقۡتُمۡ وَلۡيَسۡـَٔلُواْ مَآ أَنفَقُواْۚ ذَٰلِكُمۡ حُكۡمُ ٱللَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡۖ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan muminai mata sun zo muku suna masu yin hijira, sai ku jarraba su; Allah ne Ya fi sanin imaninsu; to idan kuka san cewa su muminai ne, to kada ku mayar da su wurin kafirai; su ba halal ba ne gare su (kafirai), su ma (kafiran) ba halal ba ne a gare su; kuma ku ba su abin da suka kashe. Kuma babu laifi a kanku ku aure su idan kun ba su sadakinsu. Kada kuma ku riqe igiyar auren mata kafirai, ku tambayi abin da kuka kashe, su ma su tambayi abin da suka kashe[1]. Wannan shi ne hukuncin Allah da Yake hukuntawa a tsakaninku. Allah kuma Masani ne, Mai hikima


1- Watau duk matan da suka yi ridda suka gudu zuwa wajen kafirai, to Musulmi su nemi kafiran su biya su abin da suka kashe wajen auren su. Su ma kafiran su nemi Musulmi su biya su sadakin matansu da suka musulunta suka gudo wajen Musulmi.


Sourate: Suratul Ma’arij

Verset : 32

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ

Waxanda kuma suke kiyaye amanoninsu da alqawuransu