Sourate: Suratul Baqara

Verset : 235

وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا عَرَّضۡتُم بِهِۦ مِنۡ خِطۡبَةِ ٱلنِّسَآءِ أَوۡ أَكۡنَنتُمۡ فِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ سَتَذۡكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِن لَّا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّآ أَن تَقُولُواْ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗاۚ وَلَا تَعۡزِمُواْ عُقۡدَةَ ٱلنِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡكِتَٰبُ أَجَلَهُۥۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Kuma babu laifi a kanku game da abin da kuka yi wa mata jirwaye da shi na neman aurensu ko kuma kuka voye a cikin zukatanku, Allah Ya san cewa ku za ku riqa maganarsu, sai dai kar ku yi alqawari da su (na aure) a asirce, sai dai in za ku faxi zance wanda yake sananne a (shari’a). Kuma kada ku qulla igiyar aure (da mata masu takaba) har sai faralin idda ya cika wa’adinsa. Kuma ku sani lalle Allah Ya san abin da yake cikin zukatanku, don haka ku kiyaye Shi. Kuma ku sani lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai haquri



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 263

۞قَوۡلٞ مَّعۡرُوفٞ وَمَغۡفِرَةٌ خَيۡرٞ مِّن صَدَقَةٖ يَتۡبَعُهَآ أَذٗىۗ وَٱللَّهُ غَنِيٌّ حَلِيمٞ

Kyakkyawar magana da yafiya sun fi sadakar da cutarwa za ta biyo bayanta alheri. Kuma Allah Shi ne Wadatacce, Mai haquri



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 155

إِنَّ ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ مِنكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِ إِنَّمَا ٱسۡتَزَلَّهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِبَعۡضِ مَا كَسَبُواْۖ وَلَقَدۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Lalle waxanda suka gudu daga cikinku yayin da runduna biyu suka haxu, Shaixan ne ya nemi ya zamar da su saboda wani laifi da suka yi; kuma tabbas haqiqa Allah Ya yi musu afuwa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai haquri



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 12

۞وَلَكُمۡ نِصۡفُ مَا تَرَكَ أَزۡوَٰجُكُمۡ إِن لَّمۡ يَكُن لَّهُنَّ وَلَدٞۚ فَإِن كَانَ لَهُنَّ وَلَدٞ فَلَكُمُ ٱلرُّبُعُ مِمَّا تَرَكۡنَۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصِينَ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٖۚ وَلَهُنَّ ٱلرُّبُعُ مِمَّا تَرَكۡتُمۡ إِن لَّمۡ يَكُن لَّكُمۡ وَلَدٞۚ فَإِن كَانَ لَكُمۡ وَلَدٞ فَلَهُنَّ ٱلثُّمُنُ مِمَّا تَرَكۡتُمۚ مِّنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ تُوصُونَ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٖۗ وَإِن كَانَ رَجُلٞ يُورَثُ كَلَٰلَةً أَوِ ٱمۡرَأَةٞ وَلَهُۥٓ أَخٌ أَوۡ أُخۡتٞ فَلِكُلِّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا ٱلسُّدُسُۚ فَإِن كَانُوٓاْ أَكۡثَرَ مِن ذَٰلِكَ فَهُمۡ شُرَكَآءُ فِي ٱلثُّلُثِۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصَىٰ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٍ غَيۡرَ مُضَآرّٖۚ وَصِيَّةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَلِيمٞ

Kuma kuna da rabin abin da matanku suka bari in ya kasance ba su da xa ko ‘ya, amma idan sun kasance suna da xa ko ‘ya, to kuna da kaso xaya bisa huxu na abin da suka bari, bayan zartar da wasiyyar da suka yi ko kuma bashi. Kuma suna da kaso xaya bisa huxu[1] na abin da kuka bari, in ya kasance ba ku da xa ko ‘ya. Amma idan ya kasance kuna da xa ko ‘ya to (matanku) suna da kaso xaya cikin takwas na abin da kuka bari, bayan zartar da wasiyyar da kuka yi ko kuma bashi. Amma idan namiji ne za a gaje shi a matsayin kalala[2] ko mace, kuma yana da xan’uwa guda xaya ko ‘yar’uwa guda xaya, to kowanne xaya yana da kaso xaya bisa shida. Amma idan sun fi haka yawa, to za su yi tarayya cikin kaso xaya bisa uku, bayan zartar da wasiyyar da aka yi ko kuma bashi, ba wanda zai cutar da (magadansa) ba. Allah Yana yi muku wasiyya matuqar wasiyya. Allah kuma Mai cikakken sani ne, Mai haquri


1- Idan sama da mace xaya ce, to za su yi tarayya ne a cikin wannan kason.


2- Kalala shi ne mamaci; namiji ko mace da bai bar ‘ya’ya ko iyaye ba, sai ‘yan’uwa.


Sourate: Suratul Ma’ida

Verset : 101

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَسۡـَٔلُواْ عَنۡ أَشۡيَآءَ إِن تُبۡدَ لَكُمۡ تَسُؤۡكُمۡ وَإِن تَسۡـَٔلُواْ عَنۡهَا حِينَ يُنَزَّلُ ٱلۡقُرۡءَانُ تُبۡدَ لَكُمۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهَاۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku yi tambaya game da waxansu al’amurra, waxanda idan aka bayyana muku su za su dame ku, idan kuwa kuka riqa tambaya game da su yayin da Alqur’ani yake sauka, za a bayyana muku su; Allah Ya yi rangwame game da su. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai haquri



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 11

۞وَلَوۡ يُعَجِّلُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ ٱلشَّرَّ ٱسۡتِعۡجَالَهُم بِٱلۡخَيۡرِ لَقُضِيَ إِلَيۡهِمۡ أَجَلُهُمۡۖ فَنَذَرُ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ

Da dai Allah zai gaggauta (karvar addu’ar) mutane ta sharri kamar yadda yake gaggauta ta alheri to da qarshen rayuwarsu ya zo. Sai dai Mukan bar waxanda ba sa tsammanin haxuwa da Mu cikin shisshiginsu su yi ta ximuwa



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 61

وَلَوۡ يُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِظُلۡمِهِم مَّا تَرَكَ عَلَيۡهَا مِن دَآبَّةٖ وَلَٰكِن يُؤَخِّرُهُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗىۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ لَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ

Da kuwa Allah Yana kama mutane da laifukansu ne to da bai bar wata dabba (mai tafiya) a bayanta ba (wato qasa), sai dai kuma Yana saurara musu ne har zuwa wani lokaci qayyadajje. To idan ajalinsu ya zo ba za su jinkirta daidai da sa’a guda ba, kuma ba za su gabata ba



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 44

تُسَبِّحُ لَهُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ ٱلسَّبۡعُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهِنَّۚ وَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمۡدِهِۦ وَلَٰكِن لَّا تَفۡقَهُونَ تَسۡبِيحَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورٗا

Sammai bakwai da qasa da abin da yake cikinsu (duka) suna tsarkake Shi. Ba wani abu wanda ba ya tasbihi tare da gode masa, sai dai ba kwa fahimtar tasbihinsu. Lalle Shi Ya kasance Mai yawan haquri ne, Mai yawan gafara



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 58

وَرَبُّكَ ٱلۡغَفُورُ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۖ لَوۡ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُواْ لَعَجَّلَ لَهُمُ ٱلۡعَذَابَۚ بَل لَّهُم مَّوۡعِدٞ لَّن يَجِدُواْ مِن دُونِهِۦ مَوۡئِلٗا

Ubangijinka kuwa Mai yawan gafara ne Ma’abocin rahama; da Yana kama su da abin da suka aikata, to da Ya gaggauta musu azaba. A’a, (ba Ya yin haka), sai dai suna da qayyadajjen lokaci wanda ba za su sami wata makauta ba daga gare shi



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 59

لَيُدۡخِلَنَّهُم مُّدۡخَلٗا يَرۡضَوۡنَهُۥۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٞ

Lalle tabbas Zai shigar da su wata mashiga da za su yarda da ita. Kuma lalle Allah tabbas Masani ne, Mai hakuri



Sourate: Suratul Ahzab

Verset : 51

۞تُرۡجِي مَن تَشَآءُ مِنۡهُنَّ وَتُـٔۡوِيٓ إِلَيۡكَ مَن تَشَآءُۖ وَمَنِ ٱبۡتَغَيۡتَ مِمَّنۡ عَزَلۡتَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكَۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَن تَقَرَّ أَعۡيُنُهُنَّ وَلَا يَحۡزَنَّ وَيَرۡضَيۡنَ بِمَآ ءَاتَيۡتَهُنَّ كُلُّهُنَّۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا فِي قُلُوبِكُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَلِيمٗا

Ka dakatar da duk wadda ka ga dama daga cikinsu, ka kuma jawo duk wadda ka ga dama[1]; (duk) wadda kuwa ka nema daga waxanda ka dakatar, to babu wani laifi a kanka. (Yin) wannan kuwa shi ya fi kusantar da kwanciyar ransu da kuma rashin yin baqin ciki, su kuma yarda da duk abin da ka ba su dukkansu[2]. Allah kuwa Yana sane da abin da yake cikin zukatanku. Allah kuwa Ya kasance Masani ne, Mai haquri


1- Watau Allah () bai wajabta masa rabon kwana a tsakanin matansa ba, yana iya dakatar da kwanan wadda ya ga dama ko ya jawo da kwananta.


2- Domin sun tabbatar ba zai hana musu haqqoqinsu ba ko ya qi yi musu adalci.


Sourate: Suratu Faxir

Verset : 41

۞إِنَّ ٱللَّهَ يُمۡسِكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ أَن تَزُولَاۚ وَلَئِن زَالَتَآ إِنۡ أَمۡسَكَهُمَا مِنۡ أَحَدٖ مِّنۢ بَعۡدِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورٗا

Lalle Allah ne Yake riqe da sammai da qasa don kada su ruguje. Lallai kuwa idan da za su ruguje, to ba wani mai riqe su in ba Shi ba. Lalle Shi (Allah) Ya kasance Mai haquri ne, Mai gafara



Sourate: Suratu Faxir

Verset : 45

وَلَوۡ يُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِمَا كَسَبُواْ مَا تَرَكَ عَلَىٰ ظَهۡرِهَا مِن دَآبَّةٖ وَلَٰكِن يُؤَخِّرُهُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗىۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِعِبَادِهِۦ بَصِيرَۢا

Idan da Allah Yana (saurin) damqar mutane saboda laifin da suka aikata, to da bai bar kowane mai rai ba a bayan qasa, sai dai kuma Yana saurara musu ne zuwa wani lokaci qayyadajje; to idan lokacin nasu ya zo, to lalle Allah Ya kasance Mai ganin bayinsa ne, (zai kuwa saka musu)



Sourate: Suratut Taghabun

Verset : 17

إِن تُقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا يُضَٰعِفۡهُ لَكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ شَكُورٌ حَلِيمٌ

Idan kuka ranta wa Allah kyakkyawan rance, to zai ninninka muku shi[1], Ya kuma gafarta muku. Allah kuma Mai godewa ne, Mai haquri


1- Watau duk wani kyakkyawan aiki xaya zai ninka musu shi gida goma, har zuwa ninki xari bakwai, har zuwa ninkin ba ninkin mai yawa.