Sourate: Suratul Furqan

Verset : 4

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ إِفۡكٌ ٱفۡتَرَىٰهُ وَأَعَانَهُۥ عَلَيۡهِ قَوۡمٌ ءَاخَرُونَۖ فَقَدۡ جَآءُو ظُلۡمٗا وَزُورٗا

Waxanda kuma suka kafirta suka ce: “Wannan (Alqur’ani) ba komai ba ne sai qarya da ya qage ta kuma wasu mutane daban suka taimake shi a kansa.” To haqiqa sun zo da zalunci da kuma qarya



Sourate: Suratul Furqan

Verset : 5

وَقَالُوٓاْ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ٱكۡتَتَبَهَا فَهِيَ تُمۡلَىٰ عَلَيۡهِ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلٗا

Suka kuma ce: “Tatsuniyoyin mutanen farko ne da ya rubuta su, waxanda ake masa shiftar su safe da yamma.”



Sourate: Suratul Furqan

Verset : 6

قُلۡ أَنزَلَهُ ٱلَّذِي يَعۡلَمُ ٱلسِّرَّ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Ka ce (da su): “Wanda Yake sane da asirin sammai da qasa Shi Ya saukar da shi. Lalle Shi Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai.”



Sourate: Suratul Furqan

Verset : 30

وَقَالَ ٱلرَّسُولُ يَٰرَبِّ إِنَّ قَوۡمِي ٱتَّخَذُواْ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ مَهۡجُورٗا

Manzo kuma ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riqi wannan Alqur’ani abin qaurace wa[1].”


1- Watau ta hanyar guje wa sauraron sa da rashin karanta shi da aiki da koyarwarsa.


Sourate: Suratul Furqan

Verset : 32

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَا نُزِّلَ عَلَيۡهِ ٱلۡقُرۡءَانُ جُمۡلَةٗ وَٰحِدَةٗۚ كَذَٰلِكَ لِنُثَبِّتَ بِهِۦ فُؤَادَكَۖ وَرَتَّلۡنَٰهُ تَرۡتِيلٗا

Waxanda kuma suka kafirta suka ce: “Me ya hana a saukar masa da Alqur’ani gaba xaya, a lokaci guda[1]?” Kamar haka ne (Muke saukar da shi kaxan-kaxan) don Mu tabbatar da zuciyarka da shi, Muka kuma karantar (da kai) shi daki-daki


1- Watau kamar yadda aka saukar da littafin Attaura ko Linjila.


Sourate: Suratul Furqan

Verset : 73

وَٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ لَمۡ يَخِرُّواْ عَلَيۡهَا صُمّٗا وَعُمۡيَانٗا

(Su ne) kuma waxanda idan aka yi musu wa’azi da ayoyin Ubangijinsu ba sa fuskantar su suna kurame kuma makafi



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 192

وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma lalle shi (Alqur’ani) saukarwa ce ta Ubangijin talikai



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 193

نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلۡأَمِينُ

Ruhi amintacce (watau Jibrilu) ne ya sauko da shi



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 194

عَلَىٰ قَلۡبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُنذِرِينَ

A bisa zuciyarka don ka zamanto daga masu gargaxi



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 195

بِلِسَانٍ عَرَبِيّٖ مُّبِينٖ

(Ya saukar da shi) da harshen Larabci mabayyani



Sourate: Suratun Namli

Verset : 1

طسٓۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡقُرۡءَانِ وَكِتَابٖ مُّبِينٍ

XA SIN[1]. Waxannan ayoyin Alqur’ani ne kuma Littafi mabayyani


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Sourate: Suratun Namli

Verset : 2

هُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ

(Kuma) shiriya da albishir ne ga muminai



Sourate: Suratun Namli

Verset : 76

إِنَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ يَقُصُّ عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ أَكۡثَرَ ٱلَّذِي هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Lalle wannan Alqur’anin yana labarta wa Banu-Isra’ila mafi yawan abin da suke savani a kansa



Sourate: Suratun Namli

Verset : 77

وَإِنَّهُۥ لَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ

Lalle kuma shi (Alqur’ani) tabbas shiriya ne kuma rahama ce ga muminai



Sourate: Suratun Namli

Verset : 92

وَأَنۡ أَتۡلُوَاْ ٱلۡقُرۡءَانَۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَقُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُنذِرِينَ

“An kuma (umarce ni) da in karanta Alqur’ani; don haka duk wanda ya shiriya, to ya shiriya ne don amfanin kansa; wanda kuwa ya vace sai ka ce (da shi): ‘Da ma ni ina cikin masu gargaxi ne kawai’”



Sourate: Suratul Qasas

Verset : 52

ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِهِۦ هُم بِهِۦ يُؤۡمِنُونَ

Waxanda Muka bai wa littafi a gabaninsa (Alqur’ani) (suka tsaya a kansa) su suna yin imani da shi (Alqur’ani)



Sourate: Suratul Qasas

Verset : 53

وَإِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِهِۦٓ إِنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّنَآ إِنَّا كُنَّا مِن قَبۡلِهِۦ مُسۡلِمِينَ

Idan kuma ana karanta musu (Alqur’anin) sai su ce: “Mun yi imani da shi, lalle shi gaskiya ne daga Ubangijinmu, lalle mu mun kasance Musulmi tun gabaninsa.”



Sourate: Suratul Qasas

Verset : 86

وَمَا كُنتَ تَرۡجُوٓاْ أَن يُلۡقَىٰٓ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبُ إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۖ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرٗا لِّلۡكَٰفِرِينَ

Kuma ba ka kasance kana fatan a saukar maka da littafi ba, sai dai (an yi haka ne) don rahama daga Ubangijinka; to don haka kada ka zamanto mai taimakon kafirai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 45

ٱتۡلُ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَۖ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ تَنۡهَىٰ عَنِ ٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِۗ وَلَذِكۡرُ ٱللَّهِ أَكۡبَرُۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تَصۡنَعُونَ

Ka karanta abin da ake yi maka wahayinsa na Alqur’ani, ka kuma tsai da salla; lalle salla tana hana alfasha da kuma abin qi. Kuma tabbas ambaton Allah shi ne mafi girma. Kuma Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 47

وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَۚ فَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۖ وَمِنۡ هَـٰٓؤُلَآءِ مَن يُؤۡمِنُ بِهِۦۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا ٱلۡكَٰفِرُونَ

Kamar haka kuma Muka saukar maka da Alqur’ani. To waxanda Muka bai wa littafi (a gabaninka) suna imani da shi; daga waxannan kuma (wato mutanen Makka) akwai wanda yake imani da shi. Ba kuwa mai musun ayoyinmu sai kafirai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 48

وَمَا كُنتَ تَتۡلُواْ مِن قَبۡلِهِۦ مِن كِتَٰبٖ وَلَا تَخُطُّهُۥ بِيَمِينِكَۖ إِذٗا لَّٱرۡتَابَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ

Ba ka zamanto kuma kana karanta wani littafi kafinsa ba (wato Alkur’ani), kuma ba ka rubuta shi da hannun damanka; da kuwa haka ya faru, to da sai masu qaryatawa su shiga kokwanto



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 49

بَلۡ هُوَ ءَايَٰتُۢ بَيِّنَٰتٞ فِي صُدُورِ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا ٱلظَّـٰلِمُونَ

A’a, shi dai (Alqur’ani) ayoyi ne bayyanannu (da suke) cikin zukatan waxanda aka bai wa ilimi. Ba kuwa mai yin musun ayoyinmu sai azzalumai



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 51

أَوَلَمۡ يَكۡفِهِمۡ أَنَّآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَرَحۡمَةٗ وَذِكۡرَىٰ لِقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu bai ishe su ba cewa, Mun saukar maka da Littafi da ake karanta musu shi? Lalle a game da wannan tabbas akwai rahama da kuma tunatarwa ga mutanen da suke yin imani



Sourate: Suratur Rum

Verset : 53

وَمَآ أَنتَ بِهَٰدِ ٱلۡعُمۡيِ عَن ضَلَٰلَتِهِمۡۖ إِن تُسۡمِعُ إِلَّا مَن يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا فَهُم مُّسۡلِمُونَ

Kuma kai ba mai iya shiryar da makafi (wato vatattu) ba ne daga vatansu; ba waxanda kake iya jiyarwa sai waxanda suka yi imani da ayoyinmu don haka suna masu miqa wuya



Sourate: Suratu Luqman

Verset : 2

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡحَكِيمِ

Waxannan ayoyin littafi ne mai hikima



Sourate: Suratu Luqman

Verset : 3

هُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّلۡمُحۡسِنِينَ

Shiriya ne da rahama ga masu kyautatawa



Sourate: Suratu Luqman

Verset : 7

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا وَلَّىٰ مُسۡتَكۡبِرٗا كَأَن لَّمۡ يَسۡمَعۡهَا كَأَنَّ فِيٓ أُذُنَيۡهِ وَقۡرٗاۖ فَبَشِّرۡهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Idan kuma ana karanta masa ayoyinmu sai ya juya yana mai girman kai kamar bai ji su ba, kamar a ce akwai wani nauyi a cikin kunnuwansa; to ka yi masa albishir da azaba mai raxaxi



Sourate: Suratu Luqman

Verset : 21

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ بَلۡ نَتَّبِعُ مَا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَآۚ أَوَلَوۡ كَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ يَدۡعُوهُمۡ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

Idan kuma aka ce da su: “Ku bi abin da Allah Ya saukar”, sai su ce: “A’a, mu muna bin abin da muka sami iyayenmu ne a kansa.” Yanzu (sa yi haka) ko da Shaixan ya zamanto yana kiran su zuwa ga azaba ta (wuta) mai ruruwa?



Sourate: Suratus Sajda

Verset : 2

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ لَا رَيۡبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Saukar da Littafin da babu kokwanto a cikinsa daga Ubangijin talikai ne



Sourate: Suratus Sajda

Verset : 15

إِنَّمَا يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِهَا خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَسَبَّحُواْ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ۩

Lalle kawai masu imani da ayoyinmu su ne waxanda idan aka yi musu wa’azi da su za su faxi suna masu sujjada su kuma yi tasbihi tare da yabon Ubangijinsu, kuma su ba sa yin girman kai