Sourate: Suratut Tauba

Verset : 91

لَّيۡسَ عَلَى ٱلضُّعَفَآءِ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرۡضَىٰ وَلَا عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ مَا يُنفِقُونَ حَرَجٌ إِذَا نَصَحُواْ لِلَّهِ وَرَسُولِهِۦۚ مَا عَلَى ٱلۡمُحۡسِنِينَ مِن سَبِيلٖۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Babu wani laifi a kan raunana ko marasa lafiya ko kuma waxanda ba su samu abin da za su ciyar ba (don talauci), matuqar dai sun tsarkake zuciyarsu ga Allah da Manzonsa. Babu wata hanya (ta xora laifi) ga masu kyautatawa. Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 92

وَلَا عَلَى ٱلَّذِينَ إِذَا مَآ أَتَوۡكَ لِتَحۡمِلَهُمۡ قُلۡتَ لَآ أَجِدُ مَآ أَحۡمِلُكُمۡ عَلَيۡهِ تَوَلَّواْ وَّأَعۡيُنُهُمۡ تَفِيضُ مِنَ ٱلدَّمۡعِ حَزَنًا أَلَّا يَجِدُواْ مَا يُنفِقُونَ

Haka kuma babu (laifi) a kan waxanda idan sun zo maka don ka ba su abin hawa sai ka ce: “Ba ni da abin hawan da zan ba ku,” sai suka juya idanuwansu suna kwararar da hawaye don baqin cikin ba su sami abin da za su ciyar ba



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 93

۞إِنَّمَا ٱلسَّبِيلُ عَلَى ٱلَّذِينَ يَسۡتَـٔۡذِنُونَكَ وَهُمۡ أَغۡنِيَآءُۚ رَضُواْ بِأَن يَكُونُواْ مَعَ ٱلۡخَوَالِفِ وَطَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Zargi kawai yana kan waxanda suke neman izininka alhali kuwa suna mawadata. Sun yarda da su kasance tare da masu zaman gida (mata da yara). Allah kuma Ya doxe zukatansu, saboda haka ba sa sanin (gaskiya)



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 94

يَعۡتَذِرُونَ إِلَيۡكُمۡ إِذَا رَجَعۡتُمۡ إِلَيۡهِمۡۚ قُل لَّا تَعۡتَذِرُواْ لَن نُّؤۡمِنَ لَكُمۡ قَدۡ نَبَّأَنَا ٱللَّهُ مِنۡ أَخۡبَارِكُمۡۚ وَسَيَرَى ٱللَّهُ عَمَلَكُمۡ وَرَسُولُهُۥ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Za su kawo muku uzurinsu idan kuka dawo musu. Ka ce: “Kada ku kawo wani uziri, mu ba za mu gaskata ku ba har abada, haqiqa Allah Ya faxa mana labarinku. Allah kuwa zai ga ayyukanku Shi da Manzonsa, sannan a komar da ku zuwa ga Masanin abin da yake voye da na sarari, sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.”



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 95

سَيَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ لَكُمۡ إِذَا ٱنقَلَبۡتُمۡ إِلَيۡهِمۡ لِتُعۡرِضُواْ عَنۡهُمۡۖ فَأَعۡرِضُواْ عَنۡهُمۡۖ إِنَّهُمۡ رِجۡسٞۖ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُ جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Za su rantse muku da Allah idan kuka dawo wurinsu don ku qyale su. To ku qyale su xin. Lalle su najasa ne; makomarsu kuma wutar Jahannama ce sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 96

يَحۡلِفُونَ لَكُمۡ لِتَرۡضَوۡاْ عَنۡهُمۡۖ فَإِن تَرۡضَوۡاْ عَنۡهُمۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يَرۡضَىٰ عَنِ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Suna rantse muku don ku yarda da su; to idan ma kun yarda da su xin, lalle (Shi) Allah ba zai yarda da mutane fasiqai ba



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 97

ٱلۡأَعۡرَابُ أَشَدُّ كُفۡرٗا وَنِفَاقٗا وَأَجۡدَرُ أَلَّا يَعۡلَمُواْ حُدُودَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Mutanen qauye sun fi tsananin kafirci da munafunci, kuma su suka fi dacewa da rashin sanin dokokin da Allah Ya saukar wa Manzonsa. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 98

وَمِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مَن يَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ مَغۡرَمٗا وَيَتَرَبَّصُ بِكُمُ ٱلدَّوَآئِرَۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Daga mutanen qauye kuma akwai waxanda suke xaukar abin da suke ciyarwa tara ne, suke kuma jiran faruwar masifu gare ku. To mummunar musiba ta tabbata a kansu. Allah kuma Mai ji ne, Masani



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 99

وَمِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مَن يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَيَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ قُرُبَٰتٍ عِندَ ٱللَّهِ وَصَلَوَٰتِ ٱلرَّسُولِۚ أَلَآ إِنَّهَا قُرۡبَةٞ لَّهُمۡۚ سَيُدۡخِلُهُمُ ٱللَّهُ فِي رَحۡمَتِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Daga mutanen qauye xin kuma akwai waxanda suke yin imani da Allah da ranar lahira, suke kuma xaukar abin da suke ciyarwa (hanyoyi ne) na samun kusanci ga Allah da kuma addu’o’in Manzo. Lalle wannan ibada ce gare su. Allah zai shigar da su cikin rahamarsa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 117

لَّقَد تَّابَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلنَّبِيِّ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ وَٱلۡأَنصَارِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ ٱلۡعُسۡرَةِ مِنۢ بَعۡدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٖ مِّنۡهُمۡ ثُمَّ تَابَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّهُۥ بِهِمۡ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ

Tabbas haqiqa Allah Ya yafe wa Annabi da masu hijira da kuma Ansaru waxanda suka bi shi a lokacin tsanani bayan har zukatan wasu qungiyoyi daga cikinsu sun kusa su karkace, sannan (Allah) Ya karvi tubansu. Lalle Shi Mai tausasawa ne, Mai jin qai a gare su



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 118

وَعَلَى ٱلثَّلَٰثَةِ ٱلَّذِينَ خُلِّفُواْ حَتَّىٰٓ إِذَا ضَاقَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَرۡضُ بِمَا رَحُبَتۡ وَضَاقَتۡ عَلَيۡهِمۡ أَنفُسُهُمۡ وَظَنُّوٓاْ أَن لَّا مَلۡجَأَ مِنَ ٱللَّهِ إِلَّآ إِلَيۡهِ ثُمَّ تَابَ عَلَيۡهِمۡ لِيَتُوبُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma (Ya yafe wa) mutanen nan guda uku waxanda aka dakatar da karvar tubansu[1], har sai yayin da duniya ta yi musu qunci duk da yalwarta, kuma zukatansu suka quntata, suka tabbatar da cewa dai babu wata mafaka daga Allah sai dai a wajensa. Sannan sai Ya yi musu muwafaqar tuba don su tuba. Lalle Allah Shi ne Mai yawan karvar tuba, Mai jin qai


1- Su ne sahabban nan uku, watau Ka’abu xan Maliku da Muraratu xan Rabi’atu da Hilal xan Umayyatu Al-Waqifi. Sun qi fita yaqin Tabuka tare da Annabi () ba tare da wani uzuri ba.


Sourate: Suratut Tauba

Verset : 120

مَا كَانَ لِأَهۡلِ ٱلۡمَدِينَةِ وَمَنۡ حَوۡلَهُم مِّنَ ٱلۡأَعۡرَابِ أَن يَتَخَلَّفُواْ عَن رَّسُولِ ٱللَّهِ وَلَا يَرۡغَبُواْ بِأَنفُسِهِمۡ عَن نَّفۡسِهِۦۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ لَا يُصِيبُهُمۡ ظَمَأٞ وَلَا نَصَبٞ وَلَا مَخۡمَصَةٞ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا يَطَـُٔونَ مَوۡطِئٗا يَغِيظُ ٱلۡكُفَّارَ وَلَا يَنَالُونَ مِنۡ عَدُوّٖ نَّيۡلًا إِلَّا كُتِبَ لَهُم بِهِۦ عَمَلٞ صَٰلِحٌۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Bai kamata ba ga mutanen Madina da waxanda suke kewaye da su daga mazauna qauye su noqe su qi bin Manzon Allah, ko kuma su zavi kansu fiye da shi. Wannan kuwa saboda ba wata qishirwa ko wahala ko yunwa da za ta same su a kan hanyar Allah, kuma ba za su taka wani wuri ba da zai vata wa kafirai rai, kuma ba za su tafka wa abokan gaba wata hasara ba sai an rubuta musu lada saboda shi (wato kowane xaya daga abubuwan da aka zana). Lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 121

وَلَا يُنفِقُونَ نَفَقَةٗ صَغِيرَةٗ وَلَا كَبِيرَةٗ وَلَا يَقۡطَعُونَ وَادِيًا إِلَّا كُتِبَ لَهُمۡ لِيَجۡزِيَهُمُ ٱللَّهُ أَحۡسَنَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Ba kuma za su bayar da wata sadaka ba, qarama ko kuma babba, kuma ba wani kwazazzabo da za su keta sai an rubuta musu ladansu don Allah Ya saka musu da mafi kyawun abin da suka zamanto suna aikatawa



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 122

۞وَمَا كَانَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لِيَنفِرُواْ كَآفَّةٗۚ فَلَوۡلَا نَفَرَ مِن كُلِّ فِرۡقَةٖ مِّنۡهُمۡ طَآئِفَةٞ لِّيَتَفَقَّهُواْ فِي ٱلدِّينِ وَلِيُنذِرُواْ قَوۡمَهُمۡ إِذَا رَجَعُوٓاْ إِلَيۡهِمۡ لَعَلَّهُمۡ يَحۡذَرُونَ

Bai kamata muminai su fita yaqi gaba xaya ba. Me zai hana wasu jama’a daga kowace qabila (su zauna) don su koyi ilimin addini, su kuma yi wa mutanensu gargaxi idan sun dawo musu don su kiyaye (dokokin Allah)?