Sourate: Suratun Namli

Verset : 37

ٱرۡجِعۡ إِلَيۡهِمۡ فَلَنَأۡتِيَنَّهُم بِجُنُودٖ لَّا قِبَلَ لَهُم بِهَا وَلَنُخۡرِجَنَّهُم مِّنۡهَآ أَذِلَّةٗ وَهُمۡ صَٰغِرُونَ

“Koma musu (da kyautarsu) sannan (ka gaya musu) lalle za mu zo musu da runduna wadda ba za su iya tunkarar ta ba, kuma lalle za mu fitar da su daga cikinta (alqaryar) a wulaqance suna qasqantattu!”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 38

قَالَ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَؤُاْ أَيُّكُمۡ يَأۡتِينِي بِعَرۡشِهَا قَبۡلَ أَن يَأۡتُونِي مُسۡلِمِينَ

Sai (Sulaimanu) ya ce: “Ya ku manyan fada, wane ne daga cikinku zai zo min da gadon mulkinta tun kafin su zo min suna masu miqa wuya?”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 39

قَالَ عِفۡرِيتٞ مِّنَ ٱلۡجِنِّ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن تَقُومَ مِن مَّقَامِكَۖ وَإِنِّي عَلَيۡهِ لَقَوِيٌّ أَمِينٞ

Sai wani ifritu[1] daga cikin aljannu ya ce: “Ni zan zo maka da shi kafin ka tashi daga majalisarka; lalle ni kuma mai qarfi ne amintacce game da (kawo) shi.”


1- Watau wani qaqqarfan aljani.


Sourate: Suratun Namli

Verset : 40

قَالَ ٱلَّذِي عِندَهُۥ عِلۡمٞ مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن يَرۡتَدَّ إِلَيۡكَ طَرۡفُكَۚ فَلَمَّا رَءَاهُ مُسۡتَقِرًّا عِندَهُۥ قَالَ هَٰذَا مِن فَضۡلِ رَبِّي لِيَبۡلُوَنِيٓ ءَأَشۡكُرُ أَمۡ أَكۡفُرُۖ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيّٞ كَرِيمٞ

Sai wani (mutum) wanda yake da ilimin Littafi (na Attaura) ya ce: “Ni zan kawo maka shi kafin ka qifta idonka!” To lokacin da (Sulaimanu) ya gan shi ga shi nan a gabansa sai ya ce: “Wannan yana daga falalar Ubangijina don Ya jarraba ni (Ya gani) shin zan gode ne ko zan butulce; to duk wanda ya gode kansa ya yi wa; wanda kuwa ya butulce, to lalle Ubangijina Mawadaci ne, Mai karamci.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 41

قَالَ نَكِّرُواْ لَهَا عَرۡشَهَا نَنظُرۡ أَتَهۡتَدِيٓ أَمۡ تَكُونُ مِنَ ٱلَّذِينَ لَا يَهۡتَدُونَ

(Sai Sulaimanu) ya ce: “Ku sauya kamannin gadon nata mu gani za ta gane (shi) ko kuwa za ta zamanto cikin waxanda ba sa ganewa?”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 42

فَلَمَّا جَآءَتۡ قِيلَ أَهَٰكَذَا عَرۡشُكِۖ قَالَتۡ كَأَنَّهُۥ هُوَۚ وَأُوتِينَا ٱلۡعِلۡمَ مِن قَبۡلِهَا وَكُنَّا مُسۡلِمِينَ

To lokacin da ta zo, sai aka ce (da ita): “Shin haka kuwa gadonki yake?” Sai ta ce: “Sai ka ce shi.” (Sulaimanu ya ce): “An kuwa ba mu ilimi tun gabaninta, kuma mun kasance Musulmi



Sourate: Suratun Namli

Verset : 43

وَصَدَّهَا مَا كَانَت تَّعۡبُدُ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ إِنَّهَا كَانَتۡ مِن قَوۡمٖ كَٰفِرِينَ

“Kuma abin da ta kasance tana bauta wa ba Allah ba, shi ya hana ta (yin imani); lalle ita ta kasance cikin mutane kafurai.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 44

قِيلَ لَهَا ٱدۡخُلِي ٱلصَّرۡحَۖ فَلَمَّا رَأَتۡهُ حَسِبَتۡهُ لُجَّةٗ وَكَشَفَتۡ عَن سَاقَيۡهَاۚ قَالَ إِنَّهُۥ صَرۡحٞ مُّمَرَّدٞ مِّن قَوَارِيرَۗ قَالَتۡ رَبِّ إِنِّي ظَلَمۡتُ نَفۡسِي وَأَسۡلَمۡتُ مَعَ سُلَيۡمَٰنَ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Aka ce da ita: “Ki shiga fadar;” to lokacin da ta gan ta sai ta zace ta ruwa ne mai zurfi, sai kuwa ta yaye qwaurinta. Sai (Sulaimanu) ya ce: “Ai ita fada ce da aka gina da gogaggun kasaken qarau (ruwa yake gudana ta qarqashinsu).” Ta ce: “Ya Ubangijina, haqiqa na zalunci kaina, na kuma miqa wuya ga Allah Ubangijin talikai tare da Sulaimanu.”



Sourate: Suratu Saba’i

Verset : 12

وَلِسُلَيۡمَٰنَ ٱلرِّيحَ غُدُوُّهَا شَهۡرٞ وَرَوَاحُهَا شَهۡرٞۖ وَأَسَلۡنَا لَهُۥ عَيۡنَ ٱلۡقِطۡرِۖ وَمِنَ ٱلۡجِنِّ مَن يَعۡمَلُ بَيۡنَ يَدَيۡهِ بِإِذۡنِ رَبِّهِۦۖ وَمَن يَزِغۡ مِنۡهُمۡ عَنۡ أَمۡرِنَا نُذِقۡهُ مِنۡ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

Kuma (Muka hore wa) Sulaimanu iska, tafiyarta ta safe wata guda ce, ta yamma ma kuma wata guda ce; Muka kuma vuvvugo masa da narkakkiyar tagulla tana gudana. Daga aljannu kuma akwai masu aiki a wajensa da umarnin Ubangijinsa; wanda kuwa ya kauce wa umarninmu daga cikinsu, to za Mu xanxana masa azabar wutar Sa’ira



Sourate: Suratu Saba’i

Verset : 13

يَعۡمَلُونَ لَهُۥ مَا يَشَآءُ مِن مَّحَٰرِيبَ وَتَمَٰثِيلَ وَجِفَانٖ كَٱلۡجَوَابِ وَقُدُورٖ رَّاسِيَٰتٍۚ ٱعۡمَلُوٓاْ ءَالَ دَاوُۥدَ شُكۡرٗاۚ وَقَلِيلٞ مِّنۡ عِبَادِيَ ٱلشَّكُورُ

Suna aikata masa abubuwan da yake bukata na manya-manyan gine-gine[1] da mutum-mutumi[2] da akusa manya-manya kamar tafkuna da kafaffun tukwane. Ya ku iyalin Dawuda, ku yi aikin (xa’a) domin godiya. Masu godiya daga bayina kuwa kaxan ne


1- Watau wuraren ibada.


2- A wancan lokacin ba a haramta yin su ba. Sai bayan zuwan Annabi () ne ya haramta suranta su ko gina su.


Sourate: Suratu Saba’i

Verset : 14

فَلَمَّا قَضَيۡنَا عَلَيۡهِ ٱلۡمَوۡتَ مَا دَلَّهُمۡ عَلَىٰ مَوۡتِهِۦٓ إِلَّا دَآبَّةُ ٱلۡأَرۡضِ تَأۡكُلُ مِنسَأَتَهُۥۖ فَلَمَّا خَرَّ تَبَيَّنَتِ ٱلۡجِنُّ أَن لَّوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ ٱلۡغَيۡبَ مَا لَبِثُواْ فِي ٱلۡعَذَابِ ٱلۡمُهِينِ

Sannan lokacin da Muka qaddara masa mutuwa ba abin da ya nuna musu mutuwarsa sai gara da ta riqa cin sandarsa[1]; to lokacin da ya faxi sai aljannu suka gane cewa da sun san gaibu da ba su zauna cikin azabar wulaqanci ba


1- Sandarsa da yake tsaye a kanta.


Sourate: Suratu Sad

Verset : 30

وَوَهَبۡنَا لِدَاوُۥدَ سُلَيۡمَٰنَۚ نِعۡمَ ٱلۡعَبۡدُ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٌ

Muka kuma yi wa Dawuda baiwar (xa) Sulaimanu. Madalla da wannan bawan; lalle shi mai yawan komawa ne (ga Allah)



Sourate: Suratu Sad

Verset : 31

إِذۡ عُرِضَ عَلَيۡهِ بِٱلۡعَشِيِّ ٱلصَّـٰفِنَٰتُ ٱلۡجِيَادُ

(Ka tuna) lokacin da aka jera masa ingarmun dawakai masu tsayawa da qafa uku da yamma



Sourate: Suratu Sad

Verset : 32

فَقَالَ إِنِّيٓ أَحۡبَبۡتُ حُبَّ ٱلۡخَيۡرِ عَن ذِكۡرِ رَبِّي حَتَّىٰ تَوَارَتۡ بِٱلۡحِجَابِ

Sai ya ce: “Lalle ni na fifita son dukiya (watau dawakai) a kan ambaton Ubangijina (watau sallar La’asar) har sai da (rana) ta faxi.”



Sourate: Suratu Sad

Verset : 33

رُدُّوهَا عَلَيَّۖ فَطَفِقَ مَسۡحَۢا بِٱلسُّوقِ وَٱلۡأَعۡنَاقِ

(Ya ce): “Ku dawo min da su;” sai ya riqa saran su ta qafafu da wuyoyi



Sourate: Suratu Sad

Verset : 34

وَلَقَدۡ فَتَنَّا سُلَيۡمَٰنَ وَأَلۡقَيۡنَا عَلَىٰ كُرۡسِيِّهِۦ جَسَدٗا ثُمَّ أَنَابَ

Kuma haqiqa Mun jarrabi Sulaimanu Muka xora wani jiki a kan gadonsa na mulki[1], sannan ya koma (kan mulkinsa)


1- Wannan wata jarrrabawa ce da Allah ya yi wa Annabi Sulaimanu () game da mulkinsa, lokacin da ya xora wani jiki a kan kujerarsa ta mulki. Mafi yawan malamai sun ce wani shaixani ne Allah ya ba shi ikon hayewa kujerarsa.


Sourate: Suratu Sad

Verset : 35

قَالَ رَبِّ ٱغۡفِرۡ لِي وَهَبۡ لِي مُلۡكٗا لَّا يَنۢبَغِي لِأَحَدٖ مِّنۢ بَعۡدِيٓۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡوَهَّابُ

Ya ce: “Ya Ubangijina, Ka gafarta min, Ka kuma ba ni wani mulki wanda bai kamaci wani ba a bayana ya sami irinsa; lalle Kai Kai ne Mai yawan kyauta.”



Sourate: Suratu Sad

Verset : 36

فَسَخَّرۡنَا لَهُ ٱلرِّيحَ تَجۡرِي بِأَمۡرِهِۦ رُخَآءً حَيۡثُ أَصَابَ

Sai Muka hore masa iska tana tafiya da umarninsa a natse duk inda ya fuskanta



Sourate: Suratu Sad

Verset : 37

وَٱلشَّيَٰطِينَ كُلَّ بَنَّآءٖ وَغَوَّاصٖ

Da kuma shaixanu masu yin kowane irin gini da kuma masu yin nutso (a ruwa)



Sourate: Suratu Sad

Verset : 38

وَءَاخَرِينَ مُقَرَّنِينَ فِي ٱلۡأَصۡفَادِ

Wasu kuma an xaxxaure su cikin maruruwa



Sourate: Suratu Sad

Verset : 39

هَٰذَا عَطَآؤُنَا فَٱمۡنُنۡ أَوۡ أَمۡسِكۡ بِغَيۡرِ حِسَابٖ

Wannan kyautarmu ce, to ka yi kyauta ko ka hana ba da wani bincike ba



Sourate: Suratu Sad

Verset : 40

وَإِنَّ لَهُۥ عِندَنَا لَزُلۡفَىٰ وَحُسۡنَ مَـَٔابٖ

Lalle kuma shi tabbas yana da kusanci a wurinmu, da kuma kyakkyawar makoma