Sourate: Suratul Baqara

Verset : 247

وَقَالَ لَهُمۡ نَبِيُّهُمۡ إِنَّ ٱللَّهَ قَدۡ بَعَثَ لَكُمۡ طَالُوتَ مَلِكٗاۚ قَالُوٓاْ أَنَّىٰ يَكُونُ لَهُ ٱلۡمُلۡكُ عَلَيۡنَا وَنَحۡنُ أَحَقُّ بِٱلۡمُلۡكِ مِنۡهُ وَلَمۡ يُؤۡتَ سَعَةٗ مِّنَ ٱلۡمَالِۚ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰهُ عَلَيۡكُمۡ وَزَادَهُۥ بَسۡطَةٗ فِي ٱلۡعِلۡمِ وَٱلۡجِسۡمِۖ وَٱللَّهُ يُؤۡتِي مُلۡكَهُۥ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ

Kuma Annabinsu ya ce da su: “Lalle haqiqa Allah Ya naxa Xalutu ya zama Sarki gare ku.” Sai suka ce: “Ta yaya zai samu sarauta a kanmu, alhalin mun fi shi cancatar sarauta, kuma ba a ba shi yalwar dukiya ba?” Sai ya ce: “Lalle Allah Ya zave shi a kanku, kuma Ya qare shi da yalwar ilimi da ta girman jiki, kuma Allah Yana bayar da mulkinsa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai yalwa ne, Masani.”



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 248

وَقَالَ لَهُمۡ نَبِيُّهُمۡ إِنَّ ءَايَةَ مُلۡكِهِۦٓ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلتَّابُوتُ فِيهِ سَكِينَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَبَقِيَّةٞ مِّمَّا تَرَكَ ءَالُ مُوسَىٰ وَءَالُ هَٰرُونَ تَحۡمِلُهُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Sai Annabinsu ya ce da su: “Lalle alamar (cancantar) mulkinsa ita ce akwatin nan da zai zo muku wanda a cikinsa akwai nutsuwa daga Ubangijinku da kuma sauran abin da iyalin Musa suka bari da iyalin Haruna; mala’iku na xauke da shi. Lalle a cikin wannan tabbas akwai aya a gare ku, in kun kasance muminai.”



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 249

فَلَمَّا فَصَلَ طَالُوتُ بِٱلۡجُنُودِ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ مُبۡتَلِيكُم بِنَهَرٖ فَمَن شَرِبَ مِنۡهُ فَلَيۡسَ مِنِّي وَمَن لَّمۡ يَطۡعَمۡهُ فَإِنَّهُۥ مِنِّيٓ إِلَّا مَنِ ٱغۡتَرَفَ غُرۡفَةَۢ بِيَدِهِۦۚ فَشَرِبُواْ مِنۡهُ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ فَلَمَّا جَاوَزَهُۥ هُوَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ قَالُواْ لَا طَاقَةَ لَنَا ٱلۡيَوۡمَ بِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦۚ قَالَ ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَٰقُواْ ٱللَّهِ كَم مِّن فِئَةٖ قَلِيلَةٍ غَلَبَتۡ فِئَةٗ كَثِيرَةَۢ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

To yayin da Xalutu ya fita (bayan gari) da rundunarsa, sai ya ce: “Lalle Allah zai jarrabe ku da wata qorama, to duk wanda ya sha daga gare ta, to ba ya tare da ni, duk wanda kuwa bai sha ba, to wannan yana tare da ni, sai dai wanda ya kamfata sau xaya da (tafin) hannunsa.” Gaba xayansu sai suka sha daga cikinta sai ‘yan kaxan daga cikinsu (su ne ba su sha ba). To yayin da ya qetare shi, shi da waxanda suka yi imani tare da shi, sai suka ce: “A yau kam ba mu da iko wajen fuskantar Jalutu da rundunarsa.” Sai waxanda suke da yaqinin cewa za su haxu da Allah suka ce: “Sau da yawa wata runduna ‘yan kaxan takan yi rinjaye a kan wata runduna mai yawa da izinin Allah. Kuma Allah Yana tare da masu haquri.”