Sourate: Suratul A’araf

Verset : 206

إِنَّ ٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَيُسَبِّحُونَهُۥ وَلَهُۥ يَسۡجُدُونَۤ۩

Lalle waxanda suke wajen Ubangijinka, ba sa girman kai wajen bautar Sa, kuma suna tsarkake Shi, kuma gare Shi kawai suke yin sujjada



Sourate: Suratur Ra’ad

Verset : 15

وَلِلَّهِۤ يَسۡجُدُۤ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ طَوۡعٗا وَكَرۡهٗا وَظِلَٰلُهُم بِٱلۡغُدُوِّ وَٱلۡأٓصَالِ۩

Waxanda kuma suke sammai da qasa (duka) ga Allah suke sujjada sun so ko sun qi, haka kuma inuwoyinsu, safe da maraice



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 49

وَلِلَّهِۤ يَسۡجُدُۤ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ مِن دَآبَّةٖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ

Abin da yake cikin sammai da abin da yake bayan qasa na kowace dabba da mala’iku suna yin sujjada ne ga Allah, su kuma ba sa girman kai



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 50

يَخَافُونَ رَبَّهُم مِّن فَوۡقِهِمۡ وَيَفۡعَلُونَ مَا يُؤۡمَرُونَ۩

Suna tsoron Ubangijnsu daga samansu kuma suna aikata abin da ake umartar su da shi



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 107

قُلۡ ءَامِنُواْ بِهِۦٓ أَوۡ لَا تُؤۡمِنُوٓاْۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ مِن قَبۡلِهِۦٓ إِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ يَخِرُّونَۤ لِلۡأَذۡقَانِۤ سُجَّدٗاۤ

Ka ce da su: “Ko ku yi imani da shi ko kada ku yi imani da shi (duk xaya ne).” Lalle waxanda aka bai wa ilimi gabaninsa (Yahudu da Nasara)[1] idan ana karanta musu shi suna faxuwa da fuskokinsu suna masu sujjada


1- Watau mutanen kirki daga cikinsu.


Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 108

وَيَقُولُونَ سُبۡحَٰنَ رَبِّنَآ إِن كَانَ وَعۡدُ رَبِّنَا لَمَفۡعُولٗا

Suna kuma cewa: “Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu, lalle alqawarin Ubangijinmu tabbas ya zamanto abin aikatawa ne.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 109

وَيَخِرُّونَ لِلۡأَذۡقَانِ يَبۡكُونَ وَيَزِيدُهُمۡ خُشُوعٗا۩

Suna kuma faxuwa da fuskokinsu suna kuka, Yana kuma qara musu qasqantar da kai



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 58

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِن ذُرِّيَّةِ ءَادَمَ وَمِمَّنۡ حَمَلۡنَا مَعَ نُوحٖ وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡرَـٰٓءِيلَ وَمِمَّنۡ هَدَيۡنَا وَٱجۡتَبَيۡنَآۚ إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُ ٱلرَّحۡمَٰنِ خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَبُكِيّٗا۩

Waxannan su ne annabawa waxanda Allah Ya yi ni’ima a gare su, daga zuriyar Adamu, da kuma waxanda Muka xauko (a jirgin ruwa) tare da Nuhu, daga kuma zuriyar Ibrahimu da Isra’ila (watau Ya’aqubu), da kuma waxanda Muka shiryar da su Muka kuma zave su. Idan ana karanta musu ayoyin (Allah) Mai rahama sai su faxi su yi sujjada suna kuka



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 18

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يَسۡجُدُۤ لَهُۥۤ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ وَٱلنُّجُومُ وَٱلۡجِبَالُ وَٱلشَّجَرُ وَٱلدَّوَآبُّ وَكَثِيرٞ مِّنَ ٱلنَّاسِۖ وَكَثِيرٌ حَقَّ عَلَيۡهِ ٱلۡعَذَابُۗ وَمَن يُهِنِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن مُّكۡرِمٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يَشَآءُ۩

Shin ba ka san cewa duk abin da yake cikin sammai da qasa suna yin sujjada ne ga Allah ba, (haka ma) rana da wata da taurari da duwatsu da bishiyoyi da dabbobi da kuma mutane masu yawa; da yawa kuma azaba ta tabbata a kansu? Duk kuwa wanda Allah Ya wulaqanta, to ba shi da wani mai girmama shi. Lalle Allah Yana aikata abin da Ya ga dama



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 77

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱرۡكَعُواْ وَٱسۡجُدُواْۤ وَٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمۡ وَٱفۡعَلُواْ ٱلۡخَيۡرَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ۩

Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi ruku’i kuma ku yi sujjada, ku kuma bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alheri don ku rabauta



Sourate: Suratul Furqan

Verset : 60

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱسۡجُدُواْۤ لِلرَّحۡمَٰنِ قَالُواْ وَمَا ٱلرَّحۡمَٰنُ أَنَسۡجُدُ لِمَا تَأۡمُرُنَا وَزَادَهُمۡ نُفُورٗا۩

Idan kuwa aka ce da su: “Ku yi sujjada ga Arrahmanu” sai su ce: “Mene ne Arrahmanu[1]? Yanzu ma yi sujjada ga abin da kake umartar mu?” (Wannan umarnin) kuma ya qara musu fanxarewa


1- Watau kafirai ba su yarda da sunan Allah Arrahmanu ba, kamar yadda ya zo a cikin Suratur Ra’ad, aya ta 30.


Sourate: Suratun Namli

Verset : 25

أَلَّاۤ يَسۡجُدُواْۤ لِلَّهِ ٱلَّذِي يُخۡرِجُ ٱلۡخَبۡءَ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَيَعۡلَمُ مَا تُخۡفُونَ وَمَا تُعۡلِنُونَ

“Don kada su yi sujjada ga Allah wanda Yake fito da abin da yake voye a cikin sammai da qasa, kuma Yake sane da abin da kuke voyewa da abin da kuke bayyanawa



Sourate: Suratun Namli

Verset : 26

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ۩

“(Shi ne) Allah Wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, Ubangijin Al’arshi mai girma.”



Sourate: Suratus Sajda

Verset : 15

إِنَّمَا يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِهَا خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَسَبَّحُواْ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ۩

Lalle kawai masu imani da ayoyinmu su ne waxanda idan aka yi musu wa’azi da su za su faxi suna masu sujjada su kuma yi tasbihi tare da yabon Ubangijinsu, kuma su ba sa yin girman kai



Sourate: Suratu Sad

Verset : 24

قَالَ لَقَدۡ ظَلَمَكَ بِسُؤَالِ نَعۡجَتِكَ إِلَىٰ نِعَاجِهِۦۖ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡخُلَطَآءِ لَيَبۡغِي بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٍ إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَقَلِيلٞ مَّا هُمۡۗ وَظَنَّ دَاوُۥدُ أَنَّمَا فَتَنَّـٰهُ فَٱسۡتَغۡفَرَ رَبَّهُۥ وَخَرَّۤ رَاكِعٗاۤ وَأَنَابَ۩

(Dawuda) Ya ce: “Haqiqa ya zalunce ka saboda neman haxe akuyarka cikin awakinsa; kuma lalle yawancin masu haxa dukiyarsu tabbas wasunsu suna zaluntar wasu, sai fa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, su kuwa kaxan ne qwarai. Sai kuma Dawuda ya tabbata cewa Mun jarraba shi ne, sai ya nemi gafarar Ubangijinsa, ya kuma faxi yana sujjada kuma ya koma (ga Allah)



Sourate: Suratu Fussilat

Verset : 37

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلَّيۡلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُۚ لَا تَسۡجُدُواْ لِلشَّمۡسِ وَلَا لِلۡقَمَرِ وَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

Kuma dare da wuni da rana da wata suna daga ayoyinsa. Kada ku yi sujjada ga rana ko ga wata, ku yi sujjada ga Allah Wanda Ya halicce su idan har kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa



Sourate: Suratu Fussilat

Verset : 38

فَإِنِ ٱسۡتَكۡبَرُواْ فَٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ يُسَبِّحُونَ لَهُۥ بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَهُمۡ لَا يَسۡـَٔمُونَ۩

Idan kuwa sun yi girman kai, to waxanda suke wurin Ubangijinka (mala’iku) suna yi masa tasbihi dare da rana, kuma su ba sa qosawa



Sourate: Suratun Najm

Verset : 62

فَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ وَٱعۡبُدُواْ۩

To ku yi sujjada ga Allah ku kuma bauta (masa)



Sourate: Suratul Inshiqaq

Verset : 21

وَإِذَا قُرِئَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقُرۡءَانُ لَا يَسۡجُدُونَۤ۩

Idan kuma an karanta musu Alqur’ani ba sa yin sujjada?



Sourate: Suratul Alaq

Verset : 19

كَلَّا لَا تُطِعۡهُ وَٱسۡجُدۡۤ وَٱقۡتَرِب۩

Faufau! Kada ka bi shi, ka kuma yi salla, ka kusanta (ga Allah)