Sourate: Suratur Rum

Verset : 32

مِنَ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُمۡ وَكَانُواْ شِيَعٗاۖ كُلُّ حِزۡبِۭ بِمَا لَدَيۡهِمۡ فَرِحُونَ

Irin waxanda suka rarraba addininsu suka kuma zamanto qungiya-qungiya; kowacce qungiya tana mai farin ciki da abin da yake nata



Sourate: Suratus Shura

Verset : 14

وَمَا تَفَرَّقُوٓاْ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى لَّقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۚ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ أُورِثُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُ مُرِيبٖ

Ba su kuma rarrabu ba sai bayan ilimi ya zo musu don zalunci da ke tsakaninsu. Ba don kalmar da ta riga ta gabata daga Ubangijinka ba (ta jinkirta musu) zuwa ga wani lokaci qayyadajje, da lalle an yi hukunci tsakaninsu. Kuma lalle waxanda aka gadar wa da littafi a bayansu lallai suna cikin shakka mai sa kokwanto game da shi (Annabi Muhammadu)



Sourate: Suratuz Zukhruf 

Verset : 65

فَٱخۡتَلَفَ ٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَيۡنِهِمۡۖ فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡ عَذَابِ يَوۡمٍ أَلِيمٍ

Sai qungiyoyi suka sassava a tsakaninsu[1]; don haka tsananin azabar yini mai raxaxi ya tabbata ga waxanda suka yi zalunci


1- Wasu suka ce shi Allah ne; wasu kuma suka ce xan Allah ne; wasu kuma suka ce shi da mahaifiyarsa duka alloli ne.


Sourate: Suratul Jasiya

Verset : 17

وَءَاتَيۡنَٰهُم بَيِّنَٰتٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِۖ فَمَا ٱخۡتَلَفُوٓاْ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقۡضِي بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Muka kuma kawo musu (hujjoji) mabayyana na addini; to ba su sassava ba, sai bayan da ilimi ya zo musu don hassada a tsakaninsu. Lalle Ubangijinka zai yi hukunci a tsakaninsu a ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna yin savani cikinsa



Sourate: Suratul Jasiya

Verset : 23

أَفَرَءَيۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَٰهَهُۥ هَوَىٰهُ وَأَضَلَّهُ ٱللَّهُ عَلَىٰ عِلۡمٖ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمۡعِهِۦ وَقَلۡبِهِۦ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِۦ غِشَٰوَةٗ فَمَن يَهۡدِيهِ مِنۢ بَعۡدِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Shin kuwa ka ga wanda ya xauki son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, Allah kuwa Ya vatar da shi a kan yana sane[1], Ya kuma rufe jinsa da zuciyarsa, kuma Ya sanya yana a kan ganinsa, to wane ne zai shiryar da shi in ba Allah ba? Me ya sa ba kwa wa’azantuwa?


1- Watau ya vatar da shi bayan ilimi ya zo masa, saboda Allah ya san cewa ya cancanci vata.