لَّقَدۡ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوۡلَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ فَقِيرٞ وَنَحۡنُ أَغۡنِيَآءُۘ سَنَكۡتُبُ مَا قَالُواْ وَقَتۡلَهُمُ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَنَقُولُ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ
Tabbas haqiqa Allah ya ji maganar waxannan da suka ce: “Lalle Allah mataulaci ne, mu ne mawadata.” Da sannu za Mu rubuta abin da suka faxa, da kuma kisan da suka riqa yi wa annabawa ba tare da wani haqqi ba, kuma za Mu ce: “Ku xanxani azaba mai quna
وَيَقُولُونَ طَاعَةٞ فَإِذَا بَرَزُواْ مِنۡ عِندِكَ بَيَّتَ طَآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ غَيۡرَ ٱلَّذِي تَقُولُۖ وَٱللَّهُ يَكۡتُبُ مَا يُبَيِّتُونَۖ فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلًا
Kuma sukan ce: “Ai ba mu da wani abu sai biyayya.” To idan suka fita daga wajenka, sai wata qungiya daga cikinsu, su riqa qulla wani abu daban cikin dare, savanin abin da suke faxa; Allah kuwa Yana rubuta duk wani abu da suke qullawa da daddare; to ka kawar da kai daga kansu, kuma ka dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa abin dogaro
وَإِذَآ أَذَقۡنَا ٱلنَّاسَ رَحۡمَةٗ مِّنۢ بَعۡدِ ضَرَّآءَ مَسَّتۡهُمۡ إِذَا لَهُم مَّكۡرٞ فِيٓ ءَايَاتِنَاۚ قُلِ ٱللَّهُ أَسۡرَعُ مَكۡرًاۚ إِنَّ رُسُلَنَا يَكۡتُبُونَ مَا تَمۡكُرُونَ
Idan kuma Muka xanxana wa mutane daxi bayan wahala ta same su, sai ga su suna qulla makirci ga ayoyinmu. Ka ce: “Allah Ya fi gaggawar (sakayya a kan) makirci.” Lalle manzanninmu suna rubuta abin da kuke qullawa na makirci
وَكُلَّ إِنسَٰنٍ أَلۡزَمۡنَٰهُ طَـٰٓئِرَهُۥ فِي عُنُقِهِۦۖ وَنُخۡرِجُ لَهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ كِتَٰبٗا يَلۡقَىٰهُ مَنشُورًا
Kuma kowane mutum Mun xaura masa littafin aikinsa a wuyansa, za kuma Mu fito masa da wani littafi a ranar alqiyama da zai same shi a buxe
ٱقۡرَأۡ كِتَٰبَكَ كَفَىٰ بِنَفۡسِكَ ٱلۡيَوۡمَ عَلَيۡكَ حَسِيبٗا
(A ce da shi): “Karanta littafinka; a yau ka isa ka yi wa kanka hukunci da kanka.”
يَوۡمَ نَدۡعُواْ كُلَّ أُنَاسِۭ بِإِمَٰمِهِمۡۖ فَمَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَقۡرَءُونَ كِتَٰبَهُمۡ وَلَا يُظۡلَمُونَ فَتِيلٗا
Ranar da za Mu kirawo kowanne (jinsin) mutane da shugabansu, sannan wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama to waxannan za su karanta littafinsu, sannan ba za a zalunce su ko da gwargwadon zaren qwallon dabino ne ba
وَوُضِعَ ٱلۡكِتَٰبُ فَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُشۡفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَٰوَيۡلَتَنَا مَالِ هَٰذَا ٱلۡكِتَٰبِ لَا يُغَادِرُ صَغِيرَةٗ وَلَا كَبِيرَةً إِلَّآ أَحۡصَىٰهَاۚ وَوَجَدُواْ مَا عَمِلُواْ حَاضِرٗاۗ وَلَا يَظۡلِمُ رَبُّكَ أَحَدٗا
Aka kuma ajiye littafin (ayyukansu), sannan sai ka ga masu laifi suna cike da tsoron abin da yake cikinsa, suna kuma cewa: “Kaiconmu, me ya sami wannan littafin, ba ya barin (aiki) qarami balle babba sai ya qididdige su. Suka kuma sami (duk) abubuwan da suka aikata an zo da su. Ubangijinka kuwa ba zai zalunci kowa ba
كَلَّاۚ سَنَكۡتُبُ مَا يَقُولُ وَنَمُدُّ لَهُۥ مِنَ ٱلۡعَذَابِ مَدّٗا
A’a, ba haka ba ne. Za Mu rubuta abin da yake faxa, za Mu kuma qara masa azaba ninkin-ba-ninkin
وَلَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ وَلَدَيۡنَا كِتَٰبٞ يَنطِقُ بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Ba Ma kuwa xora wa kowane rai wani abu sai wanda zai iya. Kuma a wurinmu akwai littafi da yake furuci da gaskiya, kuma su ba za a zalunce su ba
إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَنَكۡتُبُ مَا قَدَّمُواْ وَءَاثَٰرَهُمۡۚ وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ فِيٓ إِمَامٖ مُّبِينٖ
Lalle Mu ne za Mu raya matattu, Muke kuma rubuta irin abubuwan da suka gabatar (a rayuwarsu) da kuma abin da suka bari a bayansu (bayan mutuwa). Kowane abu kuma Mun qididdige shi a cikin Lauhul-Mahafuzu
وَجَعَلُواْ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ ٱلَّذِينَ هُمۡ عِبَٰدُ ٱلرَّحۡمَٰنِ إِنَٰثًاۚ أَشَهِدُواْ خَلۡقَهُمۡۚ سَتُكۡتَبُ شَهَٰدَتُهُمۡ وَيُسۡـَٔلُونَ
Suka kuma mai da mala’iku waxanda suke bayin (Allah) Arrahmanu ne `ya`ya mata. Shin sun halarci sanda aka halicce su ne? To za a rubuta shaidarsu, za kuma a tambaye su (a lahira)
أَمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّا لَا نَسۡمَعُ سِرَّهُمۡ وَنَجۡوَىٰهُمۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَيۡهِمۡ يَكۡتُبُونَ
Ko suna tsammanin cewa Mu ba Ma jin asirinsu da ganawarsu ne? Ba haka ba ne, manzanninmu suna tare da su suna rubutawa
وَتَرَىٰ كُلَّ أُمَّةٖ جَاثِيَةٗۚ كُلُّ أُمَّةٖ تُدۡعَىٰٓ إِلَىٰ كِتَٰبِهَا ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Za kuma ka ga kowace al’umma a durqushe, kowace al’umma ana kiran ta zuwa ga littafinta, a wannan rana ne za a saka muku abin da kuka kasance kuna aikatawa
هَٰذَا كِتَٰبُنَا يَنطِقُ عَلَيۡكُم بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّا كُنَّا نَسۡتَنسِخُ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
(Za a ce da su): “Wannan Littafinmu ne da yake yi muku furuci da gaskiya[1]. Lalle Mu mun kasance Muna rubuta abin da kuka kasance kuna aikatawa[2].”
1-  Watau littafin da mala’iku suka rubuta na ayyukansu yana ba da shaida a kansu da tsantsar gaskiya.
2-  Domin Allah ne da kansa ya umarci waxannan mala’ikun su riqa rubuta ayyukan mutane a duniya.            
فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَيَقُولُ هَآؤُمُ ٱقۡرَءُواْ كِتَٰبِيَهۡ
To duk wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama zai ce: “Ku karvi littafina ku karanta
وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِشِمَالِهِۦ فَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُوتَ كِتَٰبِيَهۡ
Amma kuma wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na hagun sai ya ce: “Kaicona, ina ma da ba a ba ni littafina ba!
وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ كِتَٰبٗا
Kuma kowane abu Mun qididdige shi a rubuce
وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ
Idan kuma takardun (ayyuka) aka baza su[1]
1- Watau don kowa ya karanta takardarsa da kansa.
كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٖ
Tabbas, lalle littafin fajirai yana cikin Sijjinu
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سِجِّينٞ
Me kuma ya sanar da kai me ake ce wa Sijjinu?
كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ
Littafi ne rubutacce[1]
1- Watau wanda ya qunshi cikakkun ayyukan fajirai cif-cif ba daxi babu ragi.
كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡأَبۡرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ
Tabbas! Lalle littafin mutanen kirki haqiqa yana cikin Illiyyuna
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ
Me ya sanar da kai mene ne Iliyyuna?
كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ
Wani littafi ne rubutacce[1]
1- Watau wanda aka tanada domin rubuta kyawawan ayyukan muminai cif-cif.
يَشۡهَدُهُ ٱلۡمُقَرَّبُونَ
(Mala’iku) makusanta suke halartar sa
فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ
To amma duk wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama
فَسَوۡفَ يُحَاسَبُ حِسَابٗا يَسِيرٗا
To za a yi masa hisabi mai sauqi[1]
1- Watau ta hanyar bijiro ayyukansa a dunqule ba tare da binciken qwaqwaf ba.
وَيَنقَلِبُ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ مَسۡرُورٗا
Ya kuma juyo zuwa ga iyalinsa yana farin ciki
وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ وَرَآءَ ظَهۡرِهِۦ
Amma wanda kuwa aka bai wa littafinsa ta bayan bayansa
فَسَوۡفَ يَدۡعُواْ ثُبُورٗا
To zai yi kiran halaka