Sourate: Suratul Baqara

Verset : 213

كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِۚ وَمَا ٱخۡتَلَفَ فِيهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ أُوتُوهُ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۖ فَهَدَى ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ مِنَ ٱلۡحَقِّ بِإِذۡنِهِۦۗ وَٱللَّهُ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٍ

Mutane sun kasance al’umma guda xaya, sai Allah Ya aiko da annabawa, suna masu albishir, kuma masu gargaxi, kuma Ya saukar da littafi tare da su da gaskiya, don ya yi hukunci tsakanin mutane cikin abin da suka yi savani a kansa. Kuma ba wasu ne suka yi savani a kansa ba sai waxanda aka ba wa shi, bayan hujjoji bayyanannu sun zo musu, don zalunci a tsakaninsu; sai Allah Ya shiryar da waxanda suka yi imani ga abin da (mutane) suka yi savani cikinsa na gaskiya da izininsa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 246

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ مِنۢ بَعۡدِ مُوسَىٰٓ إِذۡ قَالُواْ لِنَبِيّٖ لَّهُمُ ٱبۡعَثۡ لَنَا مَلِكٗا نُّقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ قَالَ هَلۡ عَسَيۡتُمۡ إِن كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِتَالُ أَلَّا تُقَٰتِلُواْۖ قَالُواْ وَمَا لَنَآ أَلَّا نُقَٰتِلَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَقَدۡ أُخۡرِجۡنَا مِن دِيَٰرِنَا وَأَبۡنَآئِنَاۖ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقِتَالُ تَوَلَّوۡاْ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّـٰلِمِينَ

Shin ba ka ga wasu manyan mutane ba daga cikin Banu Isra’ila bayan (mutuwar) Musa yayin da suka faxa wa Annabinsu: “Ka naxa mana wani sarki, wanda za mu yi yaqi (tare da shi) don xaukaka kalmar Allah?” Sai ya ce: “Shin ba kwa tsammanin idan an wajabta muku yaqi, ba za ku yi yaqin ba?” Sai suka ce: “Me zai sa ba za mu yi yaqi don xaukaka kalmar Allah ba, alhali kuwa an fitar da mu daga gidajenmu da ‘ya’yanmu?” To yayin da aka wajabta musu yaqin sai suka juya baya sai ‘yan kaxan daga cikinsu. Kuma Allah Masanin azzalumai ne



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 247

وَقَالَ لَهُمۡ نَبِيُّهُمۡ إِنَّ ٱللَّهَ قَدۡ بَعَثَ لَكُمۡ طَالُوتَ مَلِكٗاۚ قَالُوٓاْ أَنَّىٰ يَكُونُ لَهُ ٱلۡمُلۡكُ عَلَيۡنَا وَنَحۡنُ أَحَقُّ بِٱلۡمُلۡكِ مِنۡهُ وَلَمۡ يُؤۡتَ سَعَةٗ مِّنَ ٱلۡمَالِۚ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰهُ عَلَيۡكُمۡ وَزَادَهُۥ بَسۡطَةٗ فِي ٱلۡعِلۡمِ وَٱلۡجِسۡمِۖ وَٱللَّهُ يُؤۡتِي مُلۡكَهُۥ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ

Kuma Annabinsu ya ce da su: “Lalle haqiqa Allah Ya naxa Xalutu ya zama Sarki gare ku.” Sai suka ce: “Ta yaya zai samu sarauta a kanmu, alhalin mun fi shi cancatar sarauta, kuma ba a ba shi yalwar dukiya ba?” Sai ya ce: “Lalle Allah Ya zave shi a kanku, kuma Ya qare shi da yalwar ilimi da ta girman jiki, kuma Allah Yana bayar da mulkinsa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai yalwa ne, Masani.”



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 248

وَقَالَ لَهُمۡ نَبِيُّهُمۡ إِنَّ ءَايَةَ مُلۡكِهِۦٓ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلتَّابُوتُ فِيهِ سَكِينَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَبَقِيَّةٞ مِّمَّا تَرَكَ ءَالُ مُوسَىٰ وَءَالُ هَٰرُونَ تَحۡمِلُهُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Sai Annabinsu ya ce da su: “Lalle alamar (cancantar) mulkinsa ita ce akwatin nan da zai zo muku wanda a cikinsa akwai nutsuwa daga Ubangijinku da kuma sauran abin da iyalin Musa suka bari da iyalin Haruna; mala’iku na xauke da shi. Lalle a cikin wannan tabbas akwai aya a gare ku, in kun kasance muminai.”



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 79

مَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُؤۡتِيَهُ ٱللَّهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَ ثُمَّ يَقُولَ لِلنَّاسِ كُونُواْ عِبَادٗا لِّي مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِن كُونُواْ رَبَّـٰنِيِّـۧنَ بِمَا كُنتُمۡ تُعَلِّمُونَ ٱلۡكِتَٰبَ وَبِمَا كُنتُمۡ تَدۡرُسُونَ

Bai dace ba ga wani mutum wanda Allah zai ba shi littafi da hukunci da annabci, sannan ya ce wa mutane: “Ku zama bayina ba na Allah ba,” sai dai (ya ce): “Ku zamo malamai na Allah saboda abin da kuke karantarwa na littafi, kuma saboda abin da kuka kasance kuna karantawa.”



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 80

وَلَا يَأۡمُرَكُمۡ أَن تَتَّخِذُواْ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ أَرۡبَابًاۚ أَيَأۡمُرُكُم بِٱلۡكُفۡرِ بَعۡدَ إِذۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ

Kuma ba zai umarce ku da ku riqi mala’iku ko annabawa a matsayin iyayengiji ba; yanzu zai umarce ku da kafirci ne bayan kuna Musulmi?



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 81

وَإِذۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ لَمَآ ءَاتَيۡتُكُم مِّن كِتَٰبٖ وَحِكۡمَةٖ ثُمَّ جَآءَكُمۡ رَسُولٞ مُّصَدِّقٞ لِّمَا مَعَكُمۡ لَتُؤۡمِنُنَّ بِهِۦ وَلَتَنصُرُنَّهُۥۚ قَالَ ءَأَقۡرَرۡتُمۡ وَأَخَذۡتُمۡ عَلَىٰ ذَٰلِكُمۡ إِصۡرِيۖ قَالُوٓاْ أَقۡرَرۡنَاۚ قَالَ فَٱشۡهَدُواْ وَأَنَا۠ مَعَكُم مِّنَ ٱلشَّـٰهِدِينَ

Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya yi alqawari da annabawa cewa: “Duk irin abin da Na ba ku na littafi da wata hikima, sannan sai wani Manzo ya zo muku mai gaskata abin da yake tare da ku, to lalle ku yi imani da shi, kuma lalle ku taimake shi.” Ya ce: “Shin kun yarda da hakan, kuma kun xauki alqawarina a kan hakan?” Suka ce: “Mun yarda da haka.” Ya ce: “To ku shaida, kuma Ni ma Ina tare da ku cikin masu shaidawa.”



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 146

وَكَأَيِّن مِّن نَّبِيّٖ قَٰتَلَ مَعَهُۥ رِبِّيُّونَ كَثِيرٞ فَمَا وَهَنُواْ لِمَآ أَصَابَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَمَا ضَعُفُواْ وَمَا ٱسۡتَكَانُواْۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلصَّـٰبِرِينَ

Kuma sau da yawa an sami wani annabi (daga cikin annabawa), mabiya masu yawa sun yi yaqi tare da shi, amma ba su tava yin rauni ba saboda abin da ya same su a tafarkin Allah, kuma ba su tava yin ragwanci ba, kuma ba su tava miqa wuya ba. Kuma Allah Yana son masu haquri



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 147

وَمَا كَانَ قَوۡلَهُمۡ إِلَّآ أَن قَالُواْ رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَإِسۡرَافَنَا فِيٓ أَمۡرِنَا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma ba su da wata magana sai faxar: “Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana zunubanmu da qetare iyakar da muka yi cikin lamurranmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutunen da suke kafirai



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 161

وَمَا كَانَ لِنَبِيٍّ أَن يَغُلَّۚ وَمَن يَغۡلُلۡ يَأۡتِ بِمَا غَلَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Kuma bai dace ba ga wani annabi ya yi ha’inci. Duk wanda ya yi ha’inci kuwa zai zo da abin da ya ha’inta ranar tashin alqiyama. Sannan kowane rai a cika masa (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su (halitta) ba za a zalunce su ba



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 69

وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَٱلصَّـٰلِحِينَۚ وَحَسُنَ أُوْلَـٰٓئِكَ رَفِيقٗا

Kuma duk waxanda suka yi wa Allah xa’a da wannan Manzon, to waxannan suna tare da waxanda Allah Ya yi musu ni’ima, su ne annabawa da siddiqai da shahidai da salihan bayi. Kuma madalla da waxannan abokai



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 163

۞إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَٰرُونَ وَسُلَيۡمَٰنَۚ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Lalle Mun yi maka wahayi irin wahayin da Muka yi wa Nuhu da kuma annabawan da suka biyo bayansa, kuma Mun yi wahayi ga Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da kuma jikokin (Ya’aqubu) da Isa da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu; kuma Muka bai wa Dawuda littafin Zabura



Sourate: Suratul An’am

Verset : 112

وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوّٗا شَيَٰطِينَ ٱلۡإِنسِ وَٱلۡجِنِّ يُوحِي بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ زُخۡرُفَ ٱلۡقَوۡلِ غُرُورٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُونَ

Kuma kamar haka ne Muka sanya wa kowane annabi maqiya daga shaixanun mutane da aljannu, sashinsu yana kimsa wa wani sashi qayataccen zance, don ruxi. Kuma da Ubangijinka Ya ga dama da ba su aikata haka ba; don haka ka qyale su da irin abin da suke qagowa



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 94

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا فِي قَرۡيَةٖ مِّن نَّبِيٍّ إِلَّآ أَخَذۡنَآ أَهۡلَهَا بِٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ لَعَلَّهُمۡ يَضَّرَّعُونَ

Kuma ba Mu tava aiko wani annabi cikin wata alqarya ba, (mutanensa suka qaryata shi) sai Mun kama su da tsananin talauci da cututtuka, ko sa qasqantar da kai



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 55

وَرَبُّكَ أَعۡلَمُ بِمَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَلَقَدۡ فَضَّلۡنَا بَعۡضَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ عَلَىٰ بَعۡضٖۖ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Ubangijinka kuma (Shi ne) Mafi sanin abin da yake cikin sammai da qasa. Haqiqa kuma Mun fifita wasu annabawa a kan wasu; Muka kuma bai wa Dawuda (littafin) Zabura



Sourate: Suratu Maryam

Verset : 58

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِن ذُرِّيَّةِ ءَادَمَ وَمِمَّنۡ حَمَلۡنَا مَعَ نُوحٖ وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡرَـٰٓءِيلَ وَمِمَّنۡ هَدَيۡنَا وَٱجۡتَبَيۡنَآۚ إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُ ٱلرَّحۡمَٰنِ خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَبُكِيّٗا۩

Waxannan su ne annabawa waxanda Allah Ya yi ni’ima a gare su, daga zuriyar Adamu, da kuma waxanda Muka xauko (a jirgin ruwa) tare da Nuhu, daga kuma zuriyar Ibrahimu da Isra’ila (watau Ya’aqubu), da kuma waxanda Muka shiryar da su Muka kuma zave su. Idan ana karanta musu ayoyin (Allah) Mai rahama sai su faxi su yi sujjada suna kuka



Sourate: Suratul Furqan

Verset : 31

وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوّٗا مِّنَ ٱلۡمُجۡرِمِينَۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ هَادِيٗا وَنَصِيرٗا

Kamar haka Muka sanya wa kowanne annabi abokan gaba daga masu laifi, kuma Ubangijinka Ya ishe ka Mai shiryarwa Mai taimako



Sourate: Suratul Ahzab

Verset : 7

وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِيثَٰقَهُمۡ وَمِنكَ وَمِن نُّوحٖ وَإِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۖ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا

Kuma (ka tuna) lokacin da Muka riqi alqawura daga annabawa (na isar da aike), kuma daga gare ka, kuma daga Nuhu da Ibrahimu da Musa da Isa xan Maryamu; Muka kuma riqi alqawari mai kauri daga gare su



Sourate: Suratul Ahzab

Verset : 40

مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَآ أَحَدٖ مِّن رِّجَالِكُمۡ وَلَٰكِن رَّسُولَ ٱللَّهِ وَخَاتَمَ ٱلنَّبِيِّـۧنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا

(Annabi) Muhammadu bai kasance uban xaya daga cikin mazajenku ba, sai dai (shi) ya kasance Manzon Allah ne kuma cikamakin annabawa. Allah kuma Ya kasance Masanin komai ne



Sourate: Suratuz Zukhruf 

Verset : 6

وَكَمۡ أَرۡسَلۡنَا مِن نَّبِيّٖ فِي ٱلۡأَوَّلِينَ

Annabi nawa Muka aika wa mutanen farko



Sourate: Suratuz Zukhruf 

Verset : 7

وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن نَّبِيٍّ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Ba kuma wani annabi da yakan zo musu sai sun kasance suna yi masa izgili



Sourate: Suratul Jasiya

Verset : 16

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَفَضَّلۡنَٰهُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Haqiqa kuma Mun bai wa Banu Isra’ila littafin (Attaura) da hukunci da annabta. Muka kuma arzuta su da tsarkakan (abubuwa), kuma Muka fifita su a kan talikai



Sourate: Suratul Hadid

Verset : 26

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحٗا وَإِبۡرَٰهِيمَ وَجَعَلۡنَا فِي ذُرِّيَّتِهِمَا ٱلنُّبُوَّةَ وَٱلۡكِتَٰبَۖ فَمِنۡهُم مُّهۡتَدٖۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ

Haqiqa kuma Mun aiko Nuhu da Ibrahimu, Muka kuma sanya annabta da littafi cikin zuriyarsu; To daga cikinsu akwai shiryayyu, masu yawa kuwa daga cikinsu fasiqai ne