Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 71

قَالَ ءَامَنتُمۡ لَهُۥ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِي عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحۡرَۖ فَلَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمۡ فِي جُذُوعِ ٱلنَّخۡلِ وَلَتَعۡلَمُنَّ أَيُّنَآ أَشَدُّ عَذَابٗا وَأَبۡقَىٰ

(Fir’auna) ya ce: “Yanzu kwa yi imani da shi tun kafin in yi muku izini? Lalle shi ne babbanku wanda ya koya muku tsafi; to lalle zan yayyanke hannayenku da qafafuwanku a tarnaqe (wato hannun dama da qafar hagu), kuma tabbas zan gicciye ku a kan kututturen dabino, lalle kuma tabbas za ku san wane ne tsakanin ni da shi wanda ya fi tsananin azaba kuma ta fi xorewa



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 72

قَالُواْ لَن نُّؤۡثِرَكَ عَلَىٰ مَا جَآءَنَا مِنَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلَّذِي فَطَرَنَاۖ فَٱقۡضِ مَآ أَنتَ قَاضٍۖ إِنَّمَا تَقۡضِي هَٰذِهِ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَآ

Suka ce: “Ba za mu fifita ka ba a kan abin da ya zo mana na (ayoyi) mabayyana, da kuma a kan wanda Ya halicce mu. Sai ka hukunta duk abin da za ka hukunta; za ka yi hukunci ne kawai a wannnan rayuwar ta duniya



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 73

إِنَّآ ءَامَنَّا بِرَبِّنَا لِيَغۡفِرَ لَنَا خَطَٰيَٰنَا وَمَآ أَكۡرَهۡتَنَا عَلَيۡهِ مِنَ ٱلسِّحۡرِۗ وَٱللَّهُ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰٓ

“Lalle mu kam mun yi imani da Ubangijinmu don Ya gafarta mana laifukanmu da kuma abin da ka tilasta mu a kansa na tsafi. Allah kuwa Shi ne Mafi alherin (sakamako), kuma Shi ne Mafi dawwamar (azaba).”



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 74

إِنَّهُۥ مَن يَأۡتِ رَبَّهُۥ مُجۡرِمٗا فَإِنَّ لَهُۥ جَهَنَّمَ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحۡيَىٰ

Lalle duk wanda ya zo wa Ubangijinsa yana mai babban laifi[1] to lalle yana da (sakamakon) Jahannama, ba zai mutu a cikinta ba, ba kuma zai rayu ba (rayuwa mai daxi)


1- Watau kafirce wa Allah da haxa wani da shi a wajen bauta.


Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 75

وَمَن يَأۡتِهِۦ مُؤۡمِنٗا قَدۡ عَمِلَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلدَّرَجَٰتُ ٱلۡعُلَىٰ

Wanda kuwa ya zo masa yana mumini ya zamana ya yi aiki na gari, to waxannan suna da (sakamakon samun) darajoji maxaukaka



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 76

جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ مَن تَزَكَّىٰ

(Watau) gidajen Aljanna na dawwama waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, masu dawwama ne a cikinsu. Wannan kuwa shi ne sakamakon wanda ya tsarkaka (daga savo)



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 77

وَلَقَدۡ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَسۡرِ بِعِبَادِي فَٱضۡرِبۡ لَهُمۡ طَرِيقٗا فِي ٱلۡبَحۡرِ يَبَسٗا لَّا تَخَٰفُ دَرَكٗا وَلَا تَخۡشَىٰ

Haqiqa kuma Mun yi wa Musa wahayi cewa: “Ka tafi da bayina cikin dare sannan ka keta musu hanya qeqasasshiya a cikin kogi, ba za ka ji tsoron riskar (Fir’auna da jama’arsa) ba, kuma ba za ka ji tsoron (nutsewa) ba.”



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 78

فَأَتۡبَعَهُمۡ فِرۡعَوۡنُ بِجُنُودِهِۦ فَغَشِيَهُم مِّنَ ٱلۡيَمِّ مَا غَشِيَهُمۡ

Sai Fir’auna ya bi su shi da rundunarsa sai abin da ya haxe su na ruwan kogi ya haxiye su (suka hallaka kakaf)!



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 79

وَأَضَلَّ فِرۡعَوۡنُ قَوۡمَهُۥ وَمَا هَدَىٰ

Fir’auna kuma ya vatar da mutanensa bai kuma shiryar (da su) ba



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 45

ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ وَأَخَاهُ هَٰرُونَ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ

Sannan Muka aiko Musa da xan’uwansa Haruna da ayoyinmu da kuma hujja bayyananniya



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 46

إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمًا عَالِينَ

Zuwa ga Fir’auna da manyan (‘yan majalisarsa), sai suka yi girman kai kuma suka kasance mutane masu haike wa (jama’a da zalunci)



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 47

فَقَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لِبَشَرَيۡنِ مِثۡلِنَا وَقَوۡمُهُمَا لَنَا عَٰبِدُونَ

Sai suka ce: “Yanzu ma ba da gaskiya da mutum biyu irinmu, alhali kuwa mutanensu masu yi mana bauta ne?”



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 48

فَكَذَّبُوهُمَا فَكَانُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡلَكِينَ

Sai suka qaryata su (wato Musa da Haruna), sannan suka kasance daga waxanda aka hallaka



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 10

وَإِذۡ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئۡتِ ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka Ya kira Musa cewa: “Ka tafi wajen mutanen nan azzalumai



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 11

قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَۚ أَلَا يَتَّقُونَ

“(Watau) mutanen Fir’auna. Yanzu ba za su kiyaye dokokin Allah ba?”



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 12

قَالَ رَبِّ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ

(Musa) ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni ina tsoron su qaryata ni



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 13

وَيَضِيقُ صَدۡرِي وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِي فَأَرۡسِلۡ إِلَىٰ هَٰرُونَ

“Kuma qirjina yana quntata, kuma harshena ba ya sakuwa, sai Ka aika zuwa ga (xan’uwana) Haruna



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 14

وَلَهُمۡ عَلَيَّ ذَنۢبٞ فَأَخَافُ أَن يَقۡتُلُونِ

“Ni kuma akwai wani laifi da na yi musu, sai nake tsoron su kashe ni.”



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 15

قَالَ كَلَّاۖ فَٱذۡهَبَا بِـَٔايَٰتِنَآۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسۡتَمِعُونَ

(Allah) Ya ce: “A’a; (ba abin da zai same ka), sai ku tafi (kai da xan’uwanka) da ayoyinmu; lalle Mu masu jin (komai da zai faru) ne tare da ku



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 16

فَأۡتِيَا فِرۡعَوۡنَ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

“Ku je wajen Fir’auna sai ku faxa masa cewa: ‘Lalle mu manzannin Ubangijin talikai ne



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 17

أَنۡ أَرۡسِلۡ مَعَنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

“‘Cewa, ka sako mana da Banu-Isra’ila’.”



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 18

قَالَ أَلَمۡ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدٗا وَلَبِثۡتَ فِينَا مِنۡ عُمُرِكَ سِنِينَ

(Fir’auna) ya ce: “Yanzu ba mu muka raine ka a cikinmu tun kana jariri ba, kuma ka zauna ka yi wasu shekaru na rayuwarka a cikinmu?



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 19

وَفَعَلۡتَ فَعۡلَتَكَ ٱلَّتِي فَعَلۡتَ وَأَنتَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

“Ka kuma aikata aika-aikarka da ka aikata[1] alhali kuwa kana daga masu butulce wa (ni’imata)?”


1- Yana nufin kashe Baqibxe da ya yi lokacin da ya same shi yana faxa da Ba’isra’ile. Duba Suratul Qasas, ayat ta 15.


Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 20

قَالَ فَعَلۡتُهَآ إِذٗا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ

(Musa) ya ce: “Na aikata haka ne a lokacin ina cikin marasa shiriya (ta rashin wahayi)



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 21

فَفَرَرۡتُ مِنكُمۡ لَمَّا خِفۡتُكُمۡ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكۡمٗا وَجَعَلَنِي مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

“Sannan na guje muku lokacin da na tsorata da ku, sai Ubangijina Ya ba ni kyautar ilimi Ya kuma sanya ni daga manzanni



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 22

وَتِلۡكَ نِعۡمَةٞ تَمُنُّهَا عَلَيَّ أَنۡ عَبَّدتَّ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

“Waccen ni’imar kuwa da kake goranta min ita saboda ka bautar da Bani-Isra’ila ne.”



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 23

قَالَ فِرۡعَوۡنُ وَمَا رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Fir’auna ya ce: “To wane ne Ubangijin talikai?”



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 24

قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ

(Musa) ya ce: “(Shi ne) Ubangijin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu, idan har kun kasance masu sakankancewa (da hakan)”



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 25

قَالَ لِمَنۡ حَوۡلَهُۥٓ أَلَا تَسۡتَمِعُونَ

(Fir’auna) ya ce da waxanda suke kewaye da shi: “Shin ba kwa jin (abin da yake faxa)?”



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 26

قَالَ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ

(Musa) ya ce: “Shi ne Ubangijinku kuma Ubangijin iyayenku na farko!”