Sourate: Suratul Baqara

Verset : 213

كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِۚ وَمَا ٱخۡتَلَفَ فِيهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ أُوتُوهُ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۖ فَهَدَى ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ مِنَ ٱلۡحَقِّ بِإِذۡنِهِۦۗ وَٱللَّهُ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٍ

Mutane sun kasance al’umma guda xaya, sai Allah Ya aiko da annabawa, suna masu albishir, kuma masu gargaxi, kuma Ya saukar da littafi tare da su da gaskiya, don ya yi hukunci tsakanin mutane cikin abin da suka yi savani a kansa. Kuma ba wasu ne suka yi savani a kansa ba sai waxanda aka ba wa shi, bayan hujjoji bayyanannu sun zo musu, don zalunci a tsakaninsu; sai Allah Ya shiryar da waxanda suka yi imani ga abin da (mutane) suka yi savani cikinsa na gaskiya da izininsa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 96

إِنَّ أَوَّلَ بَيۡتٖ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكٗا وَهُدٗى لِّلۡعَٰلَمِينَ

Lalle farkon xaki da aka tanada don mutane (su yi ibada a cikinsa) shi ne wanda yake cikin Bakka[1], (xaki ne) mai albarka, kuma shiriya ne ga talikai


1- Watau Xakin Ka’aba da yake garin Makka mai alfarma.


Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 105

وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ تَفَرَّقُواْ وَٱخۡتَلَفُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Kuma kada ku kasance kamar waxanda suka rarrabu, kuma suka sassava bayan hujjoji sun zo musu. Waxannan kuwa suna da azaba mai girma



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 138

هَٰذَا بَيَانٞ لِّلنَّاسِ وَهُدٗى وَمَوۡعِظَةٞ لِّلۡمُتَّقِينَ

Wannan bayani ne don mutane, kuma shiriya ce da kuma wa’azi ga masu taqawa



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 165

أَوَلَمَّآ أَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةٞ قَدۡ أَصَبۡتُم مِّثۡلَيۡهَا قُلۡتُمۡ أَنَّىٰ هَٰذَاۖ قُلۡ هُوَ مِنۡ عِندِ أَنفُسِكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Shin yayin da wata musifa ta same ku, wadda kuma haqiqa kun yi wa (kafirai) irinta ninki biyu, sai ku riqa cewa: “Yaya haka ta faru?” Ka ce: “Ai wannan daga gare ku ne.” Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 174

فَٱنقَلَبُواْ بِنِعۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَضۡلٖ لَّمۡ يَمۡسَسۡهُمۡ سُوٓءٞ وَٱتَّبَعُواْ رِضۡوَٰنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ ذُو فَضۡلٍ عَظِيمٍ

(A sakamakon haka) sai suka dawo da ni’ima ta musamman daga Allah da falala, wani abin qi bai shafe su ba, kuma (suka dace da cewa) sun bi yardar Allah. Allah kuma Ma’abocin falala ne wadda take mai girma



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 175

إِنَّمَا ذَٰلِكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ يُخَوِّفُ أَوۡلِيَآءَهُۥ فَلَا تَخَافُوهُمۡ وَخَافُونِ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Wannan (labarin), Shaixan ne kawai yake tsoratar da ku masoyansa, don haka kar ku ji tsoron su, amma ku ji tsoro Na in dai har ku muminai ne



Sourate: Suratul Ma’ida

Verset : 97

۞جَعَلَ ٱللَّهُ ٱلۡكَعۡبَةَ ٱلۡبَيۡتَ ٱلۡحَرَامَ قِيَٰمٗا لِّلنَّاسِ وَٱلشَّهۡرَ ٱلۡحَرَامَ وَٱلۡهَدۡيَ وَٱلۡقَلَـٰٓئِدَۚ ذَٰلِكَ لِتَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَأَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ

Allah Ya sanya Ka’aba xaki ne mai alfarma, wuri mai matuqar amfani ga mutane, haka watanni masu alfarma, da dabbar hadaya da dabbar hadaya mai rataye. Wannan kuwa don ku sani cewa, lalle Allah Ya san abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa, kuma lalle Allah Masanin komai ne



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 158

قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ

Ka ce: “Ya ku mutane, lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku gaba xaya, wanda Yake da mallakar sammai da qasa, babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Shi ne Yake rayawa, kuma Shi Yake kashewa; don haka ku yi imani da Allah da Manzonsa Annabi Ummiyyi, wanda yake yin imani da Allah da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku zama shiryayyu.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 19

وَمَا كَانَ ٱلنَّاسُ إِلَّآ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَٱخۡتَلَفُواْۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡ فِيمَا فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

A da can mutane sun zamanto al’umma xaya ce (a kan tauhidi), to sai suka sassava. Da ba don wata kalma da ta gabata daga Ubangijinka[1] ba, to da an yi hukunci a tsakaninsu game da abin da suke sassavawa a kai


1- Watau hukuncinsa na cewa zai saurara wa mushirikai har zuwa ranar alqiyama.


Sourate: Suratu Yunus

Verset : 57

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَتۡكُم مَّوۡعِظَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَشِفَآءٞ لِّمَا فِي ٱلصُّدُورِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ

Ya ku mutane, haqiqa gargaxi ya zo muku daga Ubangijinku da kuma waraka ga abin da yake cikin zukatanku, kuma shiriya ne da rahama ga muminai



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 108

قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُمُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۖ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيۡكُم بِوَكِيلٖ

Ka ce: “Ya ku mutane, haqiqa gaskiya ta zo muku daga Ubangijinku; duk wanda ya shiriya to ya shiriya ne don kansa; wanda kuma ya vace to lalle ya vace don kansa ne; ni kuwa ba wakili ne a kanku ba.”



Sourate: Suratu Yusuf 

Verset : 38

وَٱتَّبَعۡتُ مِلَّةَ ءَابَآءِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ مَا كَانَ لَنَآ أَن نُّشۡرِكَ بِٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۚ ذَٰلِكَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ عَلَيۡنَا وَعَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ

“Na kuma bi hanyar iyayena Ibrahimu da Is’haqa da kuma Yaqubu. Bai kamace mu ba a ce mu tara wani abu da Allah. Wannan yana daga falalar Allah a gare mu da kuma sauran mutane, sai dai kuma yawancin mutane ba sa godewa



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 1

الٓرۚ كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ إِلَيۡكَ لِتُخۡرِجَ ٱلنَّاسَ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ بِإِذۡنِ رَبِّهِمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ

ALIF LAM RA[1]. Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya


1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.


Sourate: Suratun Nahl

Verset : 44

بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلزُّبُرِۗ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلذِّكۡرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيۡهِمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

(Mun aiko su) da hujjoji bayyanannu da littattafai. Mun kuma saukar maka da Alqur’ani don ka yi wa mutane bayanin abin da aka saukar musu ko sa yi tunani



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 89

وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٖ فَأَبَىٰٓ أَكۡثَرُ ٱلنَّاسِ إِلَّا كُفُورٗا

Kuma haqiqa Mun sarrafa wa mutane kowanne irin misali a cikin wannan Alqur’ani, sai dai yawancin mutane sun qi (komai) sai kafircewa



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 49

قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَآ أَنَا۠ لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٞ

Ka ce: “Ya ku mutane, ni dai kawai mai gargarxi ne a gare ku mai bayyana (gargaxi).”



Sourate: Suratur Rum

Verset : 30

فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفٗاۚ فِطۡرَتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي فَطَرَ ٱلنَّاسَ عَلَيۡهَاۚ لَا تَبۡدِيلَ لِخَلۡقِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلۡقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

To sai ka tsayar da fuskarka ga addini mai kauce wa varna. (Shi ne) asalin halittar da Allah Ya halicci mutane a kanta[1]. Ba wani canji ga halittar Allah. Wannan shi ne miqaqqen addini, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka ba)


1- Watau kaxaita Allah da bauta. Addinin Musulunci shi ne addinin da ya dace da halittar xan’adam ta asali, watau fixra.


Sourate: Suratu Saba’i

Verset : 28

وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا كَآفَّةٗ لِّلنَّاسِ بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

Ba Mu kuma aiko ka ba sai ga mutane baki xaya kana mai albishir mai kuma gargaxi, sai dai kuma yawancin mutane ba sa sanin (hakan)



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 41

إِنَّآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ لِلنَّاسِ بِٱلۡحَقِّۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِوَكِيلٍ

Lalle Mu Mun saukar maka da Littafi da gaskiya ga mutane; saboda haka duk wanda ya shiriya to ya yi wa kansa alheri, wanda kuwa ya vata, to lalle ya vata ne don kansa; kuma kai ba wakili ba ne a kansu



Sourate: Suratus Shura

Verset : 13

۞شَرَعَ لَكُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا وَصَّىٰ بِهِۦ نُوحٗا وَٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَمَا وَصَّيۡنَا بِهِۦٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَىٰٓۖ أَنۡ أَقِيمُواْ ٱلدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُواْ فِيهِۚ كَبُرَ عَلَى ٱلۡمُشۡرِكِينَ مَا تَدۡعُوهُمۡ إِلَيۡهِۚ ٱللَّهُ يَجۡتَبِيٓ إِلَيۡهِ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِيٓ إِلَيۡهِ مَن يُنِيبُ

Ya shar’anta muku (irin) abin da Ya yi wa Nuhu wahayi da shi na addini, da kuma wanda Muka yiwo maka wahayinsa, da kuma abin da Muka yi wa Ibrahimu da Musa da Isa wasiyya da shi cewa: “Ku tsayar da addini, kuma kada ku rarraba a cikinsa.” Abin da kake kiran kafirai zuwa gare shi ya yi musu nauyi. Allah Yana zavar wanda Ya ga dama zuwa gare shi (addini) Yana kuma shiryar da wanda Ya mayar da al’amarinsa zuwa gare Shi



Sourate: Suratul Jasiya

Verset : 20

هَٰذَا بَصَـٰٓئِرُ لِلنَّاسِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّقَوۡمٖ يُوقِنُونَ

Wannan (Alqur’ani) izina ne ga mutane da shiriya da rahama ga mutanen da suke sakankancewa



Sourate: Suratul Hadid

Verset : 25

لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَنزَلۡنَا مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَنزَلۡنَا ٱلۡحَدِيدَ فِيهِ بَأۡسٞ شَدِيدٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥ وَرُسُلَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ

Haqiqa Mun aiko manzanninmu da (ayoyi) mabayyana, Muka kuma saukar da littafi da ma’auni a tare da su (manzannin) don mutane su tsaya da adalci; Muka kuma saukar da baqin qarfe wanda a tare da shi akwai tsananin qarfi da kuma amfani ga mutane, don kuma Allah Ya bayyanar da wanda yake taimakon Sa da manzanninsa a voye. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi