Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 78

فَأَتۡبَعَهُمۡ فِرۡعَوۡنُ بِجُنُودِهِۦ فَغَشِيَهُم مِّنَ ٱلۡيَمِّ مَا غَشِيَهُمۡ

Sai Fir’auna ya bi su shi da rundunarsa sai abin da ya haxe su na ruwan kogi ya haxiye su (suka hallaka kakaf)!



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 79

وَأَضَلَّ فِرۡعَوۡنُ قَوۡمَهُۥ وَمَا هَدَىٰ

Fir’auna kuma ya vatar da mutanensa bai kuma shiryar (da su) ba



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 80

يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ قَدۡ أَنجَيۡنَٰكُم مِّنۡ عَدُوِّكُمۡ وَوَٰعَدۡنَٰكُمۡ جَانِبَ ٱلطُّورِ ٱلۡأَيۡمَنَ وَنَزَّلۡنَا عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَنَّ وَٱلسَّلۡوَىٰ

Ya ku Banu-Isra’ila, haqiqa Mun tserar da ku daga maqiyinku, (watau Fir’auna) Muka kuma yi muku alqawarin (ganawa) a varin dama na dutsen Xuri[1], Muka kuma saukar muku da darva da kuma (gasassun tsuntsayen) salwa


1- Watau Allah () ya yi musu alqawarin ganawa da Annabi Musa (), domin yin magana da shi da ba shi littafin Attaura mai qunshe da shiriya a gare su.


Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 81

كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ وَلَا تَطۡغَوۡاْ فِيهِ فَيَحِلَّ عَلَيۡكُمۡ غَضَبِيۖ وَمَن يَحۡلِلۡ عَلَيۡهِ غَضَبِي فَقَدۡ هَوَىٰ

Ku ci daga daxaxan abin da Muka arzuta ku da shi (na halal), kada kuwa ku qetare shi (zuwa haramun), sai fushina ya faxa muku; wanda kuwa fushina ya faxa masa, to haqiqa ya hallaka



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 82

وَإِنِّي لَغَفَّارٞ لِّمَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا ثُمَّ ٱهۡتَدَىٰ

Lalle Ni kuma Mai yawan gafara ne ga wanda ya tuba kuma ya yi aiki na gari sannan ya (tabbata bisa) shiriya



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 83

۞وَمَآ أَعۡجَلَكَ عَن قَوۡمِكَ يَٰمُوسَىٰ

Kuma me ya sa ka gaggawar barin mutanenka, ya Musa?



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 84

قَالَ هُمۡ أُوْلَآءِ عَلَىٰٓ أَثَرِي وَعَجِلۡتُ إِلَيۡكَ رَبِّ لِتَرۡضَىٰ

(Musa) ya ce: “Su waxannan (mutane nawa) ai za su biyo bayana ne (ba da jimawa ba), na kuwa yi gaggawa ne zuwa gare Ka ya Ubangijina don neman yardarka.”



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 85

قَالَ فَإِنَّا قَدۡ فَتَنَّا قَوۡمَكَ مِنۢ بَعۡدِكَ وَأَضَلَّهُمُ ٱلسَّامِرِيُّ

(Allah) ya ce: “To lalle Mun jarrabi mutanenka a bayanka, Samiri kuma ya vatar da su[1].”


1- Samiri, wani munafuki ne a cikin Banu Isra’ila wanda ya ja su zuwa ga bautar xan maraqi.


Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 86

فَرَجَعَ مُوسَىٰٓ إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ غَضۡبَٰنَ أَسِفٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ أَلَمۡ يَعِدۡكُمۡ رَبُّكُمۡ وَعۡدًا حَسَنًاۚ أَفَطَالَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡعَهۡدُ أَمۡ أَرَدتُّمۡ أَن يَحِلَّ عَلَيۡكُمۡ غَضَبٞ مِّن رَّبِّكُمۡ فَأَخۡلَفۡتُم مَّوۡعِدِي

Sai Musa ya komo zuwa ga mutanensa cike da fushi da baqin ciki. Ya ce: “Ya ku mutanena, yanzu Ubangijinku bai yi muku kyakkyawan alqawari ba[1]? Ko kuwa lokacin alqawarin ne ya yi muku tsawo? Ko kuwa kuna so ne fushin Ubangijinku ya saukar muku, shi ne sai kuka sava alqawarin (da muka yi na ku tabbata bisa imani)?”


1- Alqawari na cewa zai saukar musu da littafin Attaura, ya kuma shigar da su Aljjanna idan sun mutu.


Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 87

قَالُواْ مَآ أَخۡلَفۡنَا مَوۡعِدَكَ بِمَلۡكِنَا وَلَٰكِنَّا حُمِّلۡنَآ أَوۡزَارٗا مِّن زِينَةِ ٱلۡقَوۡمِ فَقَذَفۡنَٰهَا فَكَذَٰلِكَ أَلۡقَى ٱلسَّامِرِيُّ

Suka ce: “Ba mu sava alqawarinka da zavin kanmu ba, sai dai mu an xora mana kayayyakin nauyi ne na ababan adon mutane (Qibxawa), sai muka jefa su (a cikin wuta), sannan Samiri ya jefa (nasa) kamar yadda (muka yi).”



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 88

فَأَخۡرَجَ لَهُمۡ عِجۡلٗا جَسَدٗا لَّهُۥ خُوَارٞ فَقَالُواْ هَٰذَآ إِلَٰهُكُمۡ وَإِلَٰهُ مُوسَىٰ فَنَسِيَ

To sai ya fitar musu da xan maraqi jika-jika mai kuka, sai suka ce[1]: “Wannan ubangijinku ne kuma ubangijin Musa, amma sai ya manta (da yana nan).”


1- Watau wasu fitinannu daga cikin Banu Isra’ila suka faxi wannan magana.


Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 89

أَفَلَا يَرَوۡنَ أَلَّا يَرۡجِعُ إِلَيۡهِمۡ قَوۡلٗا وَلَا يَمۡلِكُ لَهُمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗا

Yanzu ba sa gani cewa (maraqin) ba ya mayar musu da magana, kuma ba ya mallakar wata cuta ko amfani gare su?



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 90

وَلَقَدۡ قَالَ لَهُمۡ هَٰرُونُ مِن قَبۡلُ يَٰقَوۡمِ إِنَّمَا فُتِنتُم بِهِۦۖ وَإِنَّ رَبَّكُمُ ٱلرَّحۡمَٰنُ فَٱتَّبِعُونِي وَأَطِيعُوٓاْ أَمۡرِي

Alhali kuwa haqiqa Haruna ya faxa musu tun da wuri cewa: “Ya ku mutanena, an jarrabe ku da shi ne kawai, kuma lalle Ubangijinku (na gaskiya) Shi ne Arrahamanu, sai ku bi ni kuma ku bi umarnina.”



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 91

قَالُواْ لَن نَّبۡرَحَ عَلَيۡهِ عَٰكِفِينَ حَتَّىٰ يَرۡجِعَ إِلَيۡنَا مُوسَىٰ

Suka ce: “Ba za mu gushe muna duqufa wajen bauta masa ba har sai Musa ya dawo mana.”



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 92

قَالَ يَٰهَٰرُونُ مَا مَنَعَكَ إِذۡ رَأَيۡتَهُمۡ ضَلُّوٓاْ

(Musa) ya ce: “Ya Haruna, me ya hana ka lokacin da ka gan su sun vace?



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 93

أَلَّا تَتَّبِعَنِۖ أَفَعَصَيۡتَ أَمۡرِي

“Ka bi ni (don ka sanar da ni)? Ko kuwa ka sava umarnina ne?”



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 94

قَالَ يَبۡنَؤُمَّ لَا تَأۡخُذۡ بِلِحۡيَتِي وَلَا بِرَأۡسِيٓۖ إِنِّي خَشِيتُ أَن تَقُولَ فَرَّقۡتَ بَيۡنَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَلَمۡ تَرۡقُبۡ قَوۡلِي

(Haruna) ya ce: “Ya xan’ummata, kada ka kama mini gemuna, da kuma (gashin) kaina; lalle ni na ji tsoron ka ce (da ni): ‘Ka rarraba kan Banu-Isra’ila, ba ka kuma kiyaye maganata ba.’”



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 95

قَالَ فَمَا خَطۡبُكَ يَٰسَٰمِرِيُّ

(Musa) ya ce: “Mene ne lamarinka, ya Samiri?”



Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 96

قَالَ بَصُرۡتُ بِمَا لَمۡ يَبۡصُرُواْ بِهِۦ فَقَبَضۡتُ قَبۡضَةٗ مِّنۡ أَثَرِ ٱلرَّسُولِ فَنَبَذۡتُهَا وَكَذَٰلِكَ سَوَّلَتۡ لِي نَفۡسِي

Ya ce: “Na ga abin da ba su gani ba ne[1], sai na xebi danqi daga gurbin (qasar) sawun (goxiyar) Manzon (wato Jibrilu) sannan na watsa ta (a kan xan maraqin). Kamar haka kuwa raina ya qawata mini.”


1- Watau ya ga Mala’ika Jibrilu a kan dokinsa lokacin da ya zo hallaka Fir’auna da jama’arsa.


Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 97

قَالَ فَٱذۡهَبۡ فَإِنَّ لَكَ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ أَن تَقُولَ لَا مِسَاسَۖ وَإِنَّ لَكَ مَوۡعِدٗا لَّن تُخۡلَفَهُۥۖ وَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ إِلَٰهِكَ ٱلَّذِي ظَلۡتَ عَلَيۡهِ عَاكِفٗاۖ لَّنُحَرِّقَنَّهُۥ ثُمَّ لَنَنسِفَنَّهُۥ فِي ٱلۡيَمِّ نَسۡفًا

(Annabi Musa) ya ce: “To sai ka tafi, amma ka tabbatar cewa (sakamakonka) a rayuwar (da za ka yi) shi ne ka riqa cewa ‘la misasa’, (watau ba za ka tavu ba kuma ba za ka tava kowa ba)[1]; kuma lalle kana da qayyadajjen lokaci wanda ba za a sava maka ba; kuma ka dubi ubangijin naka wanda ka duqufa a kansa kana bauta; lalle za mu qona shi sannan tabbas za mu sheqar da shi cikin kogi.”


1- Watau ba zai iya gauraya da mutane ba; don ba zai iya tava kowa ba, ba kuma wanda zai iya tava jikinsa.


Sourate: Suratu Xa Ha

Verset : 98

إِنَّمَآ إِلَٰهُكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَسِعَ كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمٗا

Abin bautarku kawai shi ne Allah wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi. Ya yalwaci komai da iliminsa



Sourate: Suratul Anbiya

Verset : 48

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ ٱلۡفُرۡقَانَ وَضِيَآءٗ وَذِكۡرٗا لِّلۡمُتَّقِينَ

Haqiqa Mun ba wa Musa da Haruna (Attaura) mai rarrabewa (tsakanin qarya da gaskiya) da kuma haske da shiriya ga masu taqawa



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 45

ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ وَأَخَاهُ هَٰرُونَ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ

Sannan Muka aiko Musa da xan’uwansa Haruna da ayoyinmu da kuma hujja bayyananniya



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 46

إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمًا عَالِينَ

Zuwa ga Fir’auna da manyan (‘yan majalisarsa), sai suka yi girman kai kuma suka kasance mutane masu haike wa (jama’a da zalunci)



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 47

فَقَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لِبَشَرَيۡنِ مِثۡلِنَا وَقَوۡمُهُمَا لَنَا عَٰبِدُونَ

Sai suka ce: “Yanzu ma ba da gaskiya da mutum biyu irinmu, alhali kuwa mutanensu masu yi mana bauta ne?”



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 48

فَكَذَّبُوهُمَا فَكَانُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡلَكِينَ

Sai suka qaryata su (wato Musa da Haruna), sannan suka kasance daga waxanda aka hallaka



Sourate: Suratul Mu’uminun

Verset : 49

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ لَعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ

Haqiqa kuma Mun bai wa Musa Littafi (wato Attaura) don su shiriya



Sourate: Suratul Furqan

Verset : 35

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلۡنَا مَعَهُۥٓ أَخَاهُ هَٰرُونَ وَزِيرٗا

Haqiqa kuma Mun bai wa Musa Littafi muka kuma sanya xan’uwansa Haruna tare da shi a matsayin Waziri



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 10

وَإِذۡ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئۡتِ ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka Ya kira Musa cewa: “Ka tafi wajen mutanen nan azzalumai



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 11

قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَۚ أَلَا يَتَّقُونَ

“(Watau) mutanen Fir’auna. Yanzu ba za su kiyaye dokokin Allah ba?”